DIJAH 66~70

🏵🏵DIJAH🏵🏵

Na
    Feedoh✍🏻✍🏻

6⃣6⃣~7⃣0⃣

Malam ya shiga office d'in doctor da sallama,"doctor ya amsa mashi yace kazauna malam, saida doctor ya numfasa yace, malam sakamakon razana da patient d'innan tayi, tasamu hrt atack, amma cikin ikon Allah mushawo kan matsalan in shaa Allah data farfad'o zata samu sauk'i,"saidai bazamu sallameta da wuri ba sai munga yanda jikin yake," girgiza kai malam yayi yace shikenan likita na gode Allah yabata lapia, " likita yace amin, Amma malam ya'akayi haka tafaru, "numfasawa malam yayi, yace likita rashin mahaifiya tayi yau, dama mahaifiyarta nada ciwon zuciya bayan tatafi makaranta ciwon yatashi, "kokafin mutafi asibiti rai yayi halinshi, tana dawowa daga makaranta ta tarda haka shinefa, "girgiza kai likita yayi yace ya salam Allah yajikanta da rahma amma natausaya Mata, amin malam yace, "likita yace malam zaka iya zuwa ka dubata, godiya malam yayima likita yafita.

********************
D'akin da dijah take kwance malam ya tura kai da sallama ya shiga, halin dayaga d'iyarshi ciki saida yayi kuka yace mamana Allah yabaki lapia yasa kaffara ne," yakuma jik'an mahaifiyarki da gafara, gumi yashare kana yafita waje, "aysha yasamu yace nibari naje gida saboda yan zaman gaisuwa zandawo anjima nakawo maku abubuwan buk'ata d'aga kai Aysha tayi...

Kwanan lubabatu takwas da rasuwa aka sallami dijah asibiti,"tayi wani irin fari duk tarame kamar Babylabo😜 ga batacin abinci duk tayi zuru zuru, "malam ne gabanta yana mata nasiha itako banda kuka ba abinda take,"malam yace haba hadiza shin baxaki d'auki kaddararki ba, dama Allah yanufa bazaki rayu da lubabatu ba dan Allah kisama ranki hak'uri," dijah tace baba ba laifina baneba bansan yaxan rayu babu mama kusa daniba kasan yanda nake zaune gidannan itace wadda nake ganin haske wajenta yanzukuma babu ita,"malam yace nasani uwata kuma in shaa Allah bazaki maraiciba saidai idan banda rai.

Dijah nazaune kusa da malam, "yace uwata tashi ki kiraman innarki, "tashi tayi jiki ba kwari taje k'ofar d'akin larai tayi sallama larai tace waye? "Dijah tace nice Inna dama baba ke kiranki,"tsaki tayi tace naji, tashi dijah tayi tanufi d'akin malam da sallamarta tace baba tana zuwa, "larai ce tazo bako sallama tasamu wuri tazauna ,girgiza kai malam yayi, yace dama bawani abubane yasa nakiraki saidan natunatar dake abinda kika manta, larai kiji tsoron Allah, kiga irin zaman da kikayi da marigayiya tana binki kina matsamata amma yau gashi tabarki wannan duniyar, duk ba wannan ba, yanzu ga dijah nan tadawo hanunki marainiyace kuma amanace a hannunmu duk irin rik'on da kika Mata Allah yana ganinki, kuma wlhi kobayan raina kika kori dijah banyafe makiba, kekuma dijah kicigaba da mata biyayya watarana sai labari,"Allah kuma ya gafartama lubabatu yasa aljanna ce makomarta, Amin dijah tace, "tab'e baki larai tayi tace Allah yabani ikon rik'ewa, girgixa kai malam yayi yace Amin.

www.phirdauceejeebo.mywapblog.com

Written by
           Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180