HUDAH 86~90
⭐⭐HUDAH⭐⭐
Na
Feedoh & Meesha Lurv
8⃣6⃣~9⃣0⃣
Alh yasakai yafita ranshi bace yana allah wadaran da halin matarshi, mummy juyo kai tayi kan faruq, tace dan ubanka miyahadaka da wannan tsinannar yarinyar da ake neman hadaka da ita?faruq yace bakomai mummy, tace karya kake yace shifa baisan komaiba mummy takada ta raya amma faruq yace shifa baisan komai ba, mummy tace toh kasan halin daddynku tunda yace saika aure ta saika aure ta, faruq yace wlhi mummy dana auri yarinyar nan gara na mutu, mummy tace bakama mutuwa kan wanan yar iskan, fady tace mummy wai miye laifin HUDAH dan Allah naga ko natsuwa tafi ya faruq din, bige mata baki mummy tayi tace tashikiban wuri, kema ay angama dake, fady tatashi tana kumbure baki, mummy tace kabarman komai hannuna nasan yanda zanyi..
Daddy baitsaya ko inaba sai wani super market yayimana siyayya kana yakama hanyar asibiti, sallama yayi maaah ce ta amsa yashigo yana fara'a suka gaisa da maaah, kana yace autar maaah yakarfin jiki? Nace jiki da sauki daddy, yace Allah yakara sauki, banda bakin da zanmaki magana hudah saboda anriga da an cuceki amma Allah shizaimaki sakayya, wlhi danasan abinda faruq zaimaki kenan dana roki mutuwarshi saboda niya tona ma asiri, sai a lokacin maaah tayi magana race haba Alh kada ka dora laifi akanka, kaddaran huda ke haka, kuma bayanda zamuyi mukankare mata ita saboda kaddaran tace, alh yace hakane maaah nagode kwarai dagaske, daddy yace hudah nasan ayanzu babu wanda kika tsana iron faruq kuma gashi muna neman hadaku aure, yin hakan shine daidai, kiyi hakuri duk abinda zakigani wajen faruq da mamanshi, hudah datake ta hawaye tunda daddy yafara magana tace in shaa Allah daddy zaka sameni mai biyayya yace yawwa huda nagode konji Allah yamaki albarka tace amin, daddy yace hadiza nasaka ranan auren hudah da faruq sati ukku masu zuwa kuma bana bukatar komai wajenku, maaah tace toh Alh mungode Allah yasaka da alkairi.
Daddy yakoma gida fuskan nan tashi kamar ta sadiya marafa idan tana masifa,kamar baita ba dariya ba, yatara iyalanshi su duka, yace dalilin dayasa nace kuzo shine nasaka ranan auren faruq da Hudah sati ukku masu zuwa mummy tace what? Alh kasan mikakeyi kuwa wlhi jinina bazai hada zuri'a da dangin hadiza ba, alh yace nagama magana kutashi kuban wuri faruq inbanda zufa ba abinda yakeyi, mummy tatashi tana surutai.
Satina biyu asibiti daidai da sauran sati daya a daura aure na da faruq amma ko sau daya banganshi ba, nima kuma bandamu ba, na tattara komai nabarma Allah, dannasan bamakawa sai anyi aure na da faruq kuma kullum cikin nasiha mummy takeman,ana gobe daurin aure daddy da fady sukazo suka daukan mukaje nayi siyayya, dan daddy baibin takan faruq da mummynshi, har iv daddy ya raba, washegarin daurin aure natashi jikina bawani kwari dan yau zan rabu da maaah natafi gidan da ba'asan darajata ba, sallamar daddy naji yashigo yana kuka,maaah tace lapia? Ya mika mata takarda tace alh ayban iya karatuba, yagirgiza kai, yace maaah kuyafeman, tace alh miye wai? Yace hadiza faruq yabar kasar takamaimai banmasan kasar dayatafi ba, inatashi naga takarda ya ajeman waishi bazai iya auren huda ba dan haka yabar kasar kuma duka wayoyinshi kashe, in shaa Allah faruq saiyaga ishara, maaah tace Alh karkamai baki, dama can faruq ba mijin huda baneba Allah yasa hakan shiyafi zama alkairi daddy ya girgiza kai yafita, narungume maaah ina murnah maaah tace Auta kinji dadi ko? Nace wlhi kuwa maaaah nah, tace toh Allah yamaki zabi nagari nace amin.
Abinda yafaru kuwa mummy hankalinta yatashi dataji faruq zai auri hudah tarasa yanda zatayi ga lokaci na wucewa shine tamai visa shikanshi baisaniba saida visa tafito kana yasani, shine fa ranan daurin auren jirginsu zaitashi xuwa Germany dama zaiyi PhD enshi....
www.phirdauceejeebo.mywapblog.com
Written by
Fiddausi Abdul'Azeez (Feedoh) &
Ayeesha Musa (Meesha Lurv).
Comments
Post a Comment