DIJAH 101~105
🏵🏵DIJAH🏵🏵
Feedoh yanmata
1⃣0⃣1⃣~1⃣0⃣5⃣
Gudu yake sosai kamar zai tashi sama,Allah nai yakaisu asibiti lapis, "yana shiga wasu nurses yagani cemasu yake kutaimakeni ,d'aya daga cikinsu tace malam minene?, nan ya gwada masu motarshi saboda bai iya magana, "gadon marasa lapia aka d'aura dijah emergency aka nufa da ita, yana biye dasu, anzo k'ofar emergency nurse ta juyo tace malam kayi hak'uri bazaka iya shiga ba, " tsaye yake yarasa abinyi Sai yawo yakeyi, "waya ya d'auko number naga yayi dialing ringn biyu aka d'auka, kunneshi yakai wayan yace hello Ammi Banji mi akace daga d'ayan b'angarenba, gaisheta yayi cikin ladani, kana yace Ammi bazan samu dawowa yau ba saidai Zuwa gobe, daga d'ayan b'angaren naji wadda aka Kira Ammi tace ,hamza miyasa? Bayan kaceman kataho' "Wanda aka Kira hamza yace Ammi wani abunne ya taso amma gobe in shaa Allah za dawo' Ammi tace hamza idan wani abune yasameka ka gayama plz, Hamza yace no bawani abu fa Ammi kawai wani aikin ne ya taso kedai Kiman adu'a, Ammi tace ay kullum Ina ma adu,a ,murmushi yayi yace by Ammi nd lurv u, lurv u more tace kana suka kashe waya, tagumi Hamza yayi yana kallon k'ofan emergency, waya yak'ara dialing Ana d'auka yace hello Nafeeu kazo kasameni federal medical centre nakad'e wata yarinya ne , Banji abinda Nafeeu yace ba, Hamza yace saikazo.......
Nafeeu ne yak'araso asibitin dataimakon wani yagane inda Hamza yake, Hamza na hango Nafeeu da sauri yak'arasa inda yake yana Zuwa yafad'a kan Nafeeu Sai hawaye kamar yaro, "Nafeeu ya bubbugi bayanshi yace Haba hamzarieen Ammi miye kuma na kuka, hamza yace wlh naf ko kaza bantab'a kad'ewa ba amma yau gashi nakad'e mutum kuma wlhi naf karkaso kaga yanda jini ke xuba jikinta nidai fatana kada ta mutu, " dafashi naf yayi yace Haba hamzariee shin idan ta mutu yazakayi? Kana da maganin k'addara ne? Girgiza Kai Hamza yayi naf yace toh duk Abinda kaga yasami mutum k'addara shi ce kadai kaita mata adua, hope dai baka gayama Ammi ba? Hamza yace Ina zangaya mata ta tada hankalinta tace katsina zata zo ga daddy baya k'asar' nadai Gaya mata Sai gobe zandawo, Nafeeu yace Allah ya bata lapia Amin Hamza yace........
Awarsu Hamza hud'u asibiti amma haryanzu ba wani labari, naf Sai kwantarma da Hamza yake da hankali, "can wata nurse ta fito tace waya kawo patient yanzu? Zombur Hamza yayi yace nine, nurse tace kayi hak'uri Allah yamata cikawa, fad'uwa yanemiyi saida naf yarik'o Hamza, kuka Hamza yakeyi sosai yace yanzu naf nayi kisa kenan, miyasa za kashe rai, lallashi naf yafari yace bakai Ka kashe ta ba kwananta ne suka k'are kawai Kaidai ne sila, yanzu Hamza ba lokacin kuka baneba, Zuwa zamuyi munemi danginta, inafatan zaka iya kaimu inda Ka kad'eta d'aga kanshi Hamza yayi yana share kwalla.........
www.phirdauceejeebo.mywapblog.com
Written by
Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment