ZAMAN GIDA 26~30

🤔🤔 *ZAMAN* *GIDA*🤔🤔

*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻

*_page_* 2⃣6⃣ *_to_*3⃣0⃣

Sukace jakki fa kikace, Rookiey tace I mean it, Hady tace lallai akwai aiki, feedoh tace nikam da kyar zani, Marafa tace kukema magana, Rookiey tace haba ladies kada ku sare pls kudai muje ba'a san inda ake dacewa ba, numfasawa Hady tayi tace shikenan, "Marafa tace yanzu toh ya zamuyi da yan gidanmu, feedoh tace muce matar lecturer d'inmu ce tarasu jibiya, shine akace student suje gaisuwa, Hady tace good idea,,,,,

         "K'arfe takwas na safe suka had'u tasha, saboda suna san suje su dawo da wuri, kowa na fad'an yanda akayi akabarshi, feedoh tace ni Kakus aynema tayi ta hanani, wai jibiyan ubanwa, da iyayena suka rasu yazoman, nace ay lokacin banje skul d'inba, Kakus tace toh yanzu da kikaje ma bazakije gidan uban kowa ba, kai saida na had'a da malam habu makwabcinmu kana tabarni, dariya sukayi sukace aikin Kakus sai ita,,,,

"Cikin ikon Allah basu wani dad'e ba mota ta cika, suka d'aga sai marad'i, "suna isa marad'i, suka tsaida mashina, suka gayamasu k'auyen da zasu, masu mashina suka d'aukesu, tafiya sukeyi cikin k'urmin daji, kamar zasu bar garin, saida sukayi tafiyan awa guda chur kana, masu mashina suka ajesu, sukace jakkuna zaku hau su zasu k'arasa Daku, kud'insu suka basu, suka matsa wajen masu jakai, bayani suka masu, inda zasu, sukace toh kuhau, da kyar suka iya hawan jakki, dan saida Marafa ta gangaro aka rik'eta, itako hady d'araf ta haye maybe dama Ana hawa k'auye😂, tafiya suka dungayi takai ta Rabin awa bisa jaki,kana suka iso wani d'an k'auye, ba gida gaba ba gida baya, saiwani bukka shikad'aine wajen, masu jakkai suka ajesu sukace ga gidan malam d'in godia sukayi, sukace su tsaya su fito dan su maidasu,,,,,

"Tunani suka farayi waye zai fara shiga, Rookiey Kaxs ce tayi gaba tace gafaranku dai, akace ahuwo, suwaye kushigo amma ta baya baya zaku shigo, kallon juna sukayi, tsawa aka masu akace ko baku shirya bane zaku tsaya, idan bazaku shigo ba kuyi gaba, jiki na kyarma suka juya baya, suka shiga, suna shiga aka Saki wata tsawa saida Hady takusa fitsari, itako feedoh kyarma ta kama, saikuma akace masu karkuji tsoro sarkin aljannu ne ke maku barka da zuwa, kusamu wuri kuzauna, wuri suka samu suka zauna, suna zare idanuwa, basuga ta inda mutum ya biyoba saidai suka ganshi gabansu, Marafa ta mik'e zata ruga rokieey ta Rik'ota,,,
            **********

Malamin yace mike tafe daku yanmata, hady ce ta gyara zama ta ce malam matsalarmu duk iri d'aya ce ta zayyane ma malam komai, dariya aka saki mai kamar kuka, malam yace yanmata aikinku k'aramin aiki ne Idan namaku aiki zuwa nan da kwana ukku kowace mijinta zai fito, saboda aikina ba makawa yanaci, "murna suka dingayi, buk'atar su takusa cika, "malam yace amma fa aikin na da wahala, ba lallai bane idan zaku iya, kallon juna sukayi, cankuma sukace malam zamu iya duk wahalansa, malam yace kun tabbata sukace eh,,,,,

*Dedicated* *to* *Sadiya* *Marafa* *nd* *Hadiza* *Ahmad*


*Feedoh* *Deedoh*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180