DIJAH 231~235

🏵🏵DIJAH🏵🏵

Feedoh yanmata

2⃣3⃣1⃣~2⃣3⃣5⃣

Sai kai da kawowa sukeyi, tsaye tayi, tana nan tsaye, saiga Ammi tafito, "Ammi tace dijatunah lapia naganki nan, murmushi dijah tayi tace Ammi abubuwa nagani, kuma na tambayi ya hamza yace baisaniba, "dariya Ammi tayi tace karki damu d'iyata muje ki huta kinji, cikin gida ta nufa, "Allah Allah take taga affy ta tambayeta, tana gama cin abinci, Ammi tace tatafi d'akinta, tayi wanka kaya na nan tasaka, dijah tace toh, sama tawuce d'akinta tanufa yana nan tsab kamar yanda tabarshi, murmushi tayi, tace Allah sarki my room nayi mssn enka, "wanka tashiga, tana fitowa saiga affy ta shigo cikin wani pink lace yayi kyau, tashi dijah tayi ta rungumeta, affy tace sis congratx dijah tace tnx Sistoh, 'dijah tace yawwa Sistoh waini lapia naga bak'in abubuwa gidanan, dariya dijah tayi tace nimafa bansani ba, tab'e baki tayi dijah dantasan askancin dijah, "shiryawa dijah tayi cikin peach lace riga da skirt ga d'inkinta ya karb'eta kamar ba itaba, "affy tamata makeup ta d'aurama dijah d'ankwali, ihu affy tayi tace sistr inlaw kinga kyanki, "murmushi tayi, ta kalli kanta cikin madubi, ita kanta dijah saida ta tsorata dataga kyanta, cikin ranta tace ashe haka nake, "murmushi ta dingayi, affy tace muje ana jiranki fa.....

*****************************
Suna sauka k'asa taga iyayenta Ammi tace Masha Allah d'iyata kinyi kyau, mama dai murmushi kawai takeyi, Inna larai tace dijah kinganki kamar anzanaki, dariya akayi, fita sukayi waje inda aka aje kujeru, frndz d'inta tagani suna ganin fitowarta suka hau tafi, mamaki ta dingayi ya 'akayi haka, can saiga hamzarie yafito cikin shadd gezna  blue, yayi matuk'ar kyau, kallon kallo sukeyi, k'arasowa Hamzariee yayi yace my babe kinga kanki kuwa, dijah tace kaima aykayi kyau, "hannunta yakama ya zaunar da ita, "iyayensu suka fito, daddy ne ya bud'e wajen da adua, "Hamzariee ne yatashi yayi magana, yace muna godia da dukkan wanda ya halarci taronan mungode, mak'asudin taruwan mu anan wajen shine, domin taya k'anwata kuma matata murna kammala karatunta lapia, Allah ya amfani karatunta, "wuri ya d'auki taro, d'aya bayan d'aya iyayensu suka dinga godia, kana akafara ba dijah gifts babanta yabata company d'inshi guda, mama tabata, gida a maitama, daddy yabata kud'i hakama Ammi kud'i tabata, shiko Hamzariee kyautar mota yamata benz, haka frnds d'inta suka dinga bata kyauta, "kiran dijah akayi tayi magana, sallama tayi tare da godia ga iyayenta da abokanta da kuma mijinta, dijah harda kukan murna, kuka tayi sosai, "haka akaci akasha kowa yatafi gida cikin farin ciki.....

Dijah ce suke tad'i da Hamzariee tace charming wai ya akayi aka had'a abunnan bansaniba, dariya yayi yace da taimakon bestynki feedoh muka gayyaci k'awayenki, kuma nace karta gayamaki, itz surprise, dariya dijah tayi tace Allah sarki, ya hamza nagode sosai da kulawarka Allah yasaka maka da alkairi, Hamzariee d'ora d'an yatsanshi yayi kan leb'enta yace karkiman godia iz part ov my duty inkula dake, saboda farin cikinki shine nawa, murmushi dijah tayi tare da rungume hamzariee, "haka suka dinga fira har dare yayi kamar karsu rabu......

Kwana ukku da kammala karatun dijah, yan gidansu naf suka turo, "an tsaida ranan bikin su dijah wata biyu, masu zuwa, "Hamzariee yayi jinini shi bahaka yasoba, shida yaso sati biyu masu zuwa, Amma za'ace wata biyu, "daddy yace Hamzariee idan kashirya ni ban shirya ba, saboda yara biyu zan auraddasu dan haka saina shirya, Ammi dai dariya tayi, tace ay halin hamza saishi, "daddy ne yakira baba, yace baisan yama dijah komai na aure shizai masu itada affy, baba yace Alh nauyi zaima yawa yace ayduk yayanane dan haka nizanmasu, "godia Alh Lawal yayima daddy, daddy yace bakomai, "dijah ce zaune parlor tana yankema Inna larai akaifa, Inna larai tace wlhi dijah idan natuna abunda nake maki, duk sainaji na muzanta, dijah tace haba Inna komaifa yawuce dan Allah kidaina tunawa, Inna tace Allah yajik'an malam da lubabatu dijah tace Amin.......

"Baba ne yakira dijah yace dijah burinki yacika kingama skul, kinada sauran buk'ata, gyara zama dijah tayi tace eh baba, amma wannan da kud'ina zanyi, saboda baba yanada burin yagyara garinsu, bakiyawa, amma baiga cikar burinshi ba, daddy yace toh mizakiyi, dijah tace zanyi masallaci da rijiyoyi da islamiyya, da gyara gidan baba, Allah yakai ladan kabarinsu shida mama, baba yace kinyi tunani mai kyau amma zamu iya bada guddumuwa KO? Dijah tace eh baba nagode, baba yace bakomai, Allah yacika maki burinki, dijah tace Amin........

www.Phirdauceejeebo.mywapblog.com

IG: yar_ficika

Written by
           Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180