DIJAH 161~165
🏵🏵DIJAH🏵🏵
Feedoh yanmata✍🏻
1⃣6⃣1⃣~1⃣6⃣5⃣
suna tashi da safe sukayi wanka,dijah ce ta sakko parlor cikin doguwar riga pink, gaskia tayi kyau, tana sakkowa tasamu su Ammi parlor, gaidasu tayi suka amsa da tambayarta jikinta ,Affy tace eyyeh su dijah anyi kyau, "Ammi tace masha Allah, hamza kuwa kafama dijah ido yayi yana kallonta, gaidashi tayi, ya amsa fuska sake, da tambayar jikinta, tace dasauk'i, Ammi tace toh muje ayi kalaci, daining suka wuce, shidai hamza inbanda kallon dijah ba abinda yake, affy tace ya hamza baka gane dijah baneba? naga kanata kallonta, kunya ta kamshi, Ammi tace ina ruwanki, daddy yace aygaskia ta fad'a, akayi dariya, "bayan sungama cin abinci sukadawo parlour, daddy yace dijah toh muna sauraranki....
**********************
gyara zama dijah tayi, tace kamar yanda kuka sani sunana khadija amma dijah ake ceman kumani............. kaf ta kwashe labarinta tabasu bata b'oye masu komai ba, parlour babu wanda baiyi kukaba, saboda tausaya mata, "daddy ne yayi tamaza, ya lallashi su ammi, daddy yace dijah naji labarinki, kuma zanbaki zab'i idan kinasan kikoma zan maidaki, idan kuma kinasan kizauna damu toh, "dijah tace daddy inasan zama daku yace toh shikenan, "amma dan Allah ki rik'emu amana, zamu d'aukeki kamar mumuka haifeki, kada kici amanarmu, dijah tace in shaa Allahu daddy, Ammi tace dijah zonan, rungumeta tayi tace ki d'aukeni uwa kamr yanda nake uwa wajensu hamza, kuma daddy ki d'aukeshi uba, sukuma su hamza matsayin yan uwanki, Dijah tace in shaa Allahu Ammi, daddy yace Alhamdulillah, Allah ya bayyana iyayenki, sukuma wanda suka rik'eki da amana Allah yabiyasu da gidan aljanna, dijah tace amin, daddy yace hamza ga marainiyar Allah nan Allah yabamu dan Allah ka rik'eta kamar affy, dode ta sanadiyarka muka santa, hamza yace in shaa Allah, daddy yace affynah kema ki d'auketa kamar ciki d'aya kuke, affy tace in shaa Allah, dijah tace daddy nagode maku Allah yasaka maku da alkairi, daddy yace amin dijatun hamzariee.....
dijah tace Ammi ya akayi nazo nan, nanfa suka gayamata yanda akayi, da watanninta asibiti, kuka tayi sosai dakyar ammi ta lallasheta.....
Ammi da daddy suka tashi, hamzariee yace toh affy atashi, zanyi sirri da k'anwata, murmushi tayi tatashi, "hamzariee kusa da dijah yadawo, hannunta yakamo yace dijatunah naji labarinki, in shaa Allah zanmaki gatan da sai anyi koyi dake, zanmaidaki abun kwatance agari, saina nuna maki k'aunar da naufal yama hudah, "dijah tace nagode ya hamza, hakadai ya dinga janta da fira, har Ammi ta sauko ta samesu, "Ammi tace toh malam kyaleta hakanan, batada lapia kasani, dariya yayi, yace anya karfa ta kwaceman fada, dariya Ammi tayi tace da alama takusa, hamza yace aydayake dijatunah nace ba komai...........
NOTE: Assalamu Alaikum, dan Allah kuyi hak'uri da wannan ban lapia ne, amma in shaa Allahu idan na samu sauki zakujini, tnx so much, lurv u my beautiful people❤
www.phirdauceejeebo.mywapblog.com
IG: yar_ficika
written by
Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment