JINSINAH 11~15
❄❄ *JINSINAH*❄❄
*Feedoh* *yanmata*
*page* 1⃣1⃣to1⃣5⃣
*GARIN* *SOKOTO*
Garin sokoto garine dake cike da ni'imomin Allah garine daya had'a *jinsi* kala Kala, "Muhammad asalinshi d'an garin sokoto cikin unguwar hubbare, tun yana ss3 Allah yama mahaifinshi rasuwa, amma dayake mahaifiyarshi, tsayayyar macece, batayi wasa da karatunshi ba, cikin ikon Allah yagama degree d'inshi akan computer science, Muhammad bai dad'eba Allah yahad'ashi da wani mutumi, yabashi aiki, bayan yaga yanda Muhammad yake da k'okari da rik'e amana shinefa, ya had'ashi aure da d'iyarshi mai suna fadeelah
"Fadeelah ba laifi saboda tana da kyau, saidai irin matannan ne da suka d'auki duniya da zafi kodan tayi karatu k'asar waje ne? "Tun farkon auren Muhammad baiwani ji dad'in aurenta ba, saboda ba abinda take mashi, iyaka tai zaune tadinga latsa waya, aikinta kenan, daya mata magana saitace ba yar aiki aka kawo mashi ba, tun abun bai damunshi haryakai yafara damunshi, dayakaima iyayenta k'ara sai cewa sukayi yayi hak'uri yarinya ce zata gyara.
"Haka dai Muhammad keta fama ko ruwan tea saiya d'ora gashi shi bai iya girki ba, gashi bai iya zuwa gidansu yaci saboda mahaifiyarshi kartayi zargin wani Abu, dadai yaga yunwa na niyar kamashi, mafari kenan yake zuwa restaurant cin abinci..
"Bakin wani moll naga faruk yayi parking motarshi, d'aga kaina nayi, naga da manyan bak'i anrubuta *AG,G* *MALL* fitowa yayi daga cikin mota ya nufa cikin mall d'in yana waya, karo suka kaima juna, wayar dake hannunta ta fad'i atare suka kai hannu kan wayar, "sakar mashi wayan tayi, yana d'ago wayan yaga tayi ratsa ratsa, Muhammad yace ya salam, dan Allah kiyi hak'uri, wata kyakkyawar budurwa nagani, tayi murmushi tace karkadamu, Muhammad yace dole na damu, amma mukoma ciki kizab'a wata, budurwannan ta girgiza kai tace u mean ramuwa zakaman? Muhammad yace ah ah, tace eh mana, nikam bazan amshi ramuwarka ba, muhammad yayi yayi, amma budurwannan tak'iya, dole ya hak'ura yabata fasassar wayanta, sauri ya dingayi yayi abinda yakawoshi, yana fita baiganta ba, ya duba ko ina amma babu ita babu dalilinta, hakadai yaja jiki yatafi mota,,,
"Kwance muhammad yake yayi rigingine, yana tunanin fuskan yarinyar nan, murmushi ya dingayi shikad'ai, dakuma ya tuna baisan inda zai ganta ba, sai annashuwarshi ta d'auke, haka dai ya dinga sak'e sak'e har bacci barawo yayi gaba dashi,,,
*BAYAN* *KWANA* *BIYU*
Tsaye take bakin titin ark'illa tana jiran Napep, wata bak'ar Honda ce tadawo baya ta tsaya daidai inda take, "bud'e motar akayi aka fito, tana ganinshi ta ganeshi, k'arasowa yayi yana murmushi, itama murmushi tayi mai, tace sannu yace yawwa yanmata, muhammad yace Ina zaki haka, tace mai gida, muhammad yace zan iya saukeki, tace ah ah kabarshi na gode, b'ata rai yayi yace miyasa idan nayi niyar yimaki abu kike hanani? Gaskia banjin dad'i murmushi tayi, tace ah ah fa, bansan inbaka wahala gidanmu da nisa, Muhammad yace inane, tace rinjin sambo, murmushi yayi yace karki damu muje nakaiki, tnx tace kana ta bishi,,,
"Suna shiga mota muhammad yace rannan nan saina fito bangankiba, tace aydama natsaida napep Ina fitowa kawai muka tafi, Muhammad yace miye sunan sis d'in tawa, tace Claire, juyowa yayi da sauri, murmushi tayi ta girgiza mashi Kai, tace kada kayi mamaki, dan kaganni da irin shigarku ta hausawa ko? Girgiza kai yayi, tace ni ba musulma baceba, saidai bana shigar fidda tsiraici, wanda KO a bible haramunne, shiyasa duk wanda yaji sunana yake mamaki, muhammad yace hakane gaskia nayi mamaki dake ba musulma baceba duk d'aukana ke *jinsinah* ce, saboda yanda kike shiga dakuma hausanki, claire tace tabbas niba musulma baceba, saidai idan bana fad'ama mutum ba saikuma wanda suka sanni, saboda ni nan sokoto aka haifeni, kuma cikin *jinsinka* hausawa natashi, shiyasa na iya hausa da wasu al adunku hakadai suka dinga fira, har suka iso k'ofar gidansu, muhammad yace claire zan iya samun no d'inki, claire tace y not? Wayanshi ya fiddo yabata tasaka mashi number godia yayi, yamata bankwana yaja mota yatafi,,
"Tundaga wannan rannan Claire da muhammad suka had'u shikenan suke zumunci, daga baya kuma soyayya mai k'arfi ta shiga tsakaninsu, iyayenta babu wanda baisani ba, kuma sunyi sunyi su rabata dashi, dan aganinsu abun kunya ne ace d'iyarsu ta auri bahaushe musulmi, saidai kuma kamar k'ara mata san muhammad sukeyi,,,,,,
*CIGABAN* *LABARI*
Sauri Claire keyi takoma gida dan kar mummyn enta ta ta duba bata gantaba, tana isa gidan cire takalminta tayi tafara tafiya a hankali, gaban Claire ne ya yanke yafad'i , saboda abinda tagani....
Dedicated to biebee isa❤
IG: yar_ficika
Written by
Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment