JINSINAH 131~135

❄❄ *JINSINAH*❄❄

*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻

*_page_*1⃣3⃣1⃣ *_to_*1⃣3⃣5⃣

*BAYAN* *WATA* *SHIDDA*

Abubuwa sunfaru cikin wata shidda,inda fadilah ke mulki gidan moh sai yanda tace akeyi, "komai nata umma keyinshi, umma tayi bak'i ta rame babu wani kwanciyan hankali kullum cikin Uk'uba take, "idan tashiga d'aki tayi kuka, dan tabbas tasan alhakin finah ne ke binsu, "fadilah ce tashigo d'akin umma bako sallama, samun umma tayi tabuga tagumi, "fadilah tace baiwar Allah ga wankina can yana jiranki dan wulak'anci kinzo kinyi zaune, "jiki na rawa umma ta tashi takwashi kayan fadilah tatafi tawanke,,,

            "Finah ce zaune tayi tagumi ga hawaye na binta, shiko arif sai wasanshi yakeyi, "yaro d'an waa shidda, zaka rantse yayi shekara, yayi wayo, kamar bashiba kamar shi da moh tak'ara fitowa, "anty ce da amir suka shigo, sunata sallama, amma ina finah tayi nisa, arif ne yadinga tsalle yana gwarancinshi wanda,babu wanda yasan miyake cewa, "d'agashi amir yayi yana mashi wasa shiko sai k'ara wangale baki yakeyi, amir yace my boy ka k'ara girma, dariya anty tayi tace ayban mashi renon wasa,,,
                          ********

Anty tazauna kusa da finah dafata tayi firgigit tayi tadawo cikin hayyacinta, share mata hawaye tayi tace nasan abinda ke damunki, finah kiyi hak'uri tabbas abun akwai ciwo amma kiyi hak'uri, "cikin sheshek'ar kuka finah tace anty kifa gani yau 6month bai nememu ba, ko bai nemeniba, ay yanemi yaronshi, dama shima yagaji dani, "fashewa tayi da kuka mai cin rai,,,,,

Duk abinda sukeyi amir najinsu, gyaran murya yayi yace nima abun na d'aure mun kai, ko waya, moh yadaina mani amma, kiyi hak'uri in shaa Allah ni zanje wajenshi gobe office dan bansan naje gida,,,,,,

Amir ne office d'in moh, "moh naganinshi yafara susan kai, amir yace aydama ka sosa kai, "mph yace kayi hak'uri abubuwanne sai a hankali "zama yayi ya kalli moh yace wajenka nazo, "gyara zama moh yayi yace inajinka, "amir yace yanzu abinda kayi ka kyauta? Dan karabu da mata shikanan yau wata shidda bakazo ba idan bakazo dan itaba aykazo dan yaronta, wlhi moh bakuyima finah adalciba dakai da zur'anka, saboda kai yarinyar nan tabbar iyayenta da *JINSINTA* amma irin sakayya da zakuyi mata kenan,, "tunda amir yafara magana, moh yake kallonshi saida yakai k'arshe, "moh yace amir nifa bansan inda zancenka ya nufa ba, kana maganan wata finah da yaronta ni na aureta, "kafi kowa sanin matata d'aya fadilah kuma bata tab'a haihuwa ba, "gaskia saidai wani Muhammad d'in amma baniba, "shiko amir da gaskia tamashi yawa sakin baki yayi yana kallon amir harya gama, "amir yace tabbas moh kacanja kuma dan nasan halinka dasaina ce ka fara shaye shaye, "amma kasani inma kana cikin hayyacinka, kayi haka tabbas zakayi nadama, "moh yakai k'arshe cikin d'aga murya yace amir idan zancen wata da bansaniba zakaman, plz get out of my office tun bansa akayi waje dakai ba, "tashi amir yayi yana girgiza kai, yabar office d'in cike da takaici,,,

            "Tunda amir yaje gida yarasa abinda ke damunshi, "anty ce take tambayanshi yasukayi da moh, gumi yashare, yagayama anty komai salati tayi tace anya moh ba anjuya mashi kwakwalwa ba? Amir yace nima nayi tunanin haka, tabbas moh baicikin hayyacinshi, saboda ni shaidane irin san dayakema finah, amir yace Allah ka kawoma moh Sauk'in halin daya shiga anty tace amin, "amir yace ni banmasan ta inda zanfarama finah ba, anty tace bari yanzunan ta gama cewa baka dawoba, "kamar daga sama sukaji tace ku kwantar da hankalinku naji komai, "mi arif yayi ma umma dazata rabashi da mahaifinshi, idan tace ni tubabbace shifa arif miye nashi aciki shifa *JINSINTA* ne, wlhi arif bai cancanci haka ba, kuka yaci k'arfinta koma wa tayi d'aki da gudu, tana kuka,,,

           "Tafito daga *AGG* *MALL*  kamar daga sama taji ana cewa claire, "abun mamaki yabata, "juyawan dazatayi, taga ashe neighbour d'insu ce tina, k'arasowa tinah tayi wajen finah tinah tace claire, ina kika shige 2dayz "finah tace shhhh my name is nafisa not claire, tab'e baki tinah tayi tace oopz kinfa canja addini, "dafa finah tinah tayi tace, nafisa yakamata ki shirya da mahaifanki hakanan, kibar addinin nan kikoma gida, kiyi jinyar mahaifiyarki, "mahaifiyarki bak'ak'en aljannu sun shigeta harma tana neman guduwa, babu church d'in da ba akaita ba, amma abun k'aruwa ma yake yi "salati finah tafarayi, saikuma tafashi da kuka, "kallon tinah tayi tace tinah bazan iya barin addinin nanb, saboda shine addinin gaskia, "kuma in shaa Allah dashi mahaifiyata zataji Sauk'i, "kedai taimako d'aya zakiyiman tinah tace nami? "Finah tace ki karb'i number na duk, randa daddy baya gida ki kirani, shiru tinah tayi, saikuma tace shikenan ba damuwa, "exchanging number sukayi, godiya finah tama tinah kan tawuce gida, tana tafe tana sak'e sak'e aranta,,,,,


*_Dedicated_* *_to_* *_biebee_* *_isa_*


IG: yar_ficika



© *_written_*  *_by_*
                        *_Feedoh_* *_Deedoh_*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180