ZAMAN GIDA 16~20
🤔🤔 *ZAMAN* *GIDA*🤔🤔
*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻
*_page_* 1⃣6⃣ *_to_*2⃣0⃣
Tunda feedoh tayi sallan asuba bata koma ba, gida tahau gyara, abin yaba Kakus mamaki dan feedoh bata had'a bacci dakomai ba, "kakus tagaza hak'uri tace yar nan bak'i zamuyi ne? Dariya feedoh tayi tace ah ah Kakus, "sonake nagama da wuri saboda zanje makaranta, kakus tace wace makaranta bakunyi Hutu ba, "feedoh tace wani lecture ne ke nemanmu, kakus tace toh Allah ya jishemu alkairi, feedoh tace amin,,,,,,
K'arfe goma (10am) feedoh tagama komai, bankwana tama kakus tafita, tana fita takira marafa, Marafa tace muhad'au Tasha, tana aje waya tahau mini jeep (napep), tasha yakaita, wurin mutum ukku feedoh takama, batafi 10mnt da zuwa ba su hady suka k'araso, suna zuwa basu dad'eba mota tacika,,,,
"Mintuna k'alilan suka isa charanchi, "feedoh ce ta tambayi wani gidan malam sha yanzu, mutumin yace masu cikin wani k'auye ne, saisun hau mashin, "godia sukayi suka hau mashin, "tafiya akayi takai ta Rabin awa kana suka iso wajen wani dutsi, "masu mashinan sukace masu wannan dutsin zaku hau idan kuka kai k'arshe zakuga bukka to nan ne , godia sukayi suka sallamesu,,,,
"Da kyar suka hau dutsi, tafiya sukeyi kamar bazasu kaiba, hardai hady tafara tsegumi, "suna gangarewa sukaga bukka, murmushi sukayi, bakin bukka suka tsaya, feedoh ce tace gafaranku dai, wata k'atuwar murya ta amsa masu, harsaida marafa ta tsorata, "shiga sukayi suna shiga suka samu wuri suka sauna, "malam sha yanzu yace yanmata mike tafe Daku, gyara zama Hady tayi ta zayyane mashi komai, "tak'ara dacewa malam matsalarmu d'aya muduka, duk rashin miji,,,
Kallon su malam yayi, yayi yan dube dubenshi, yace gaskia yanmata kuna cikin had'ari, saboda ku duka ukkun aljani ne gareku, kuma idan ba rabashi akayi daku ba to akwai matsala, "feedoh tace to malam ya za'ayi, yace kowace zata kawo 50k idan kuka bada toh aure cikin shekaran nan zakuyishi, kutashi kutafi idan kun shirya kun iya dawowa,, "tunda suka fito hady ke zazzaga masifa, tace wlhi malam nan sun rainamu, shi wancan abinda yafad'a daban hakama shi wanan, Marafa tace ko gidan uwarwa zamu samo 50k, feedoh dai kasa cewa komai tayi dan takaici, "haka suka hau dutse da kyar hady hartana sulalawa, said a aka kamota,,,,,
*shin* *wai* *su* *waye* *wad'annan* *yan* *matan?* *Kudai* *biyo* *feedoh* *yanmata* *danjin* *su* *waye* *yan* *matannan*
*Dedicated* *to* *sadiya* *Marafa* *nd* *hadiza* *Ahmad*
*Feedoh* *Deedoh*✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment