JINSINAH 136~140
❄❄ *JINSINAH*❄❄
*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻
*_page_* 1⃣3⃣6⃣ *_to_*1⃣4⃣0⃣
Kuka takeyi sosai, tana shiga parlor ba kowa sai arif dake wasa, yana ganinta ya nufota da gwarancinshi, d'aukanshi tayi ta rungume tana kuka sosai, kamar zata cire ranta, shiko arif, k'ok'arin share mata hawaye yskeyi, "takai minti biyar tsaye amma finah batasan tana tsaye ba, " dafata anty tayi, tace haba mamana shin bazakiyi hak'uri hakanan ba, ki d'auki k'addara, amma ke kenan kullum cikin kuka, ki duba kiga yadda kika rame, kintashi hankalin kanki kintashi namu, "moh adua yake nema wajenki, bawai ki zauna kina kuka ba, adua zakimashi, Allah ya fiddoshi halin da ya tsinci kanshi, " finah tace wlhi anty ba kukan moh nake ba mahaifiya tace...... Finah ta kwashe komai tagayama anty, shiru anty tayi tace finah yanzu miye abinyi? Finah tace anty nacema tinah idan daddy bayanan taman waya nazo saboda inmata aduoi, anty tace Good idea, "toh yazakiyi, saboda kada aganeki, kuma wani ya kira daddy, murmushi finah tayi tace anty nasan mizanyi, " Anty tace Allah ya taimakeki, kuma yasa shine silan shigansu musulunci suma, finah tace amin,,,,,,,,
*******
Washe gari, tunda finah ta tashi gabanta ke fad'uwa innalillahi wa inna ilahir raj'un take fad'a bata dai gayama kowa ba, "fone d'inta ce tafara ringing da kamar bazata d'auka ba, harta kusa tsinkewa ta d'auka, " ganin tinah a screen d'in wayanta yasa gabanta ya tsananta fad'uwa jiki sake ta d'auki wayan, "tana d'auka tinah tace hello nafisa kizo gida jikin mummy yatashi, kuma gashi daddy yayi tafiya sainan da 5dayz zai dawo, finah tace tinah gani nan amma plz dont tell anybody zanzo, kuma ko nazo karki nuna nice, tinah tace dont worry my sis bazan fad'a ba, " da sauri finah tashiga d'akin anty taga ya mata, anty tace saikin dawo Allah ya bada sa'a, arif ne ya nufota yana d'aga hannu, shafa mashi kanshi tayi tace sorry my boy bazan iya tafiya dakai ba, fake tamashi, ta juya tatafi tanajin kukanshi amma ina batako waiwayo ba, anty ce ta d'aukeshi ta goya tana rirriga haryayi bacci,,,,
"Tsaye take gaban gidansu, kamar tana tsoron shiga, babu wanda zai ganta yagane ta, saboda tasaka dogon hijab har k'asa ga nik'af tasaka, ko wanda suka haifeta basu cewa itace, " aduoin neman samun nasara tayi kana ta kutsa kai cikin gidan, tun daga parlor tafarajin ihun mummy, da sauri tashiga bedroom d'in ganin mutane tayi dandanne da ita ga tinah gefe guda tana ta hawaye, "matsowa tayi wajen, wata mata tace hey who are u itadai finah batace komai ba, karatu tafara rerawa cikin muryanta mai dad'in saurare, takai 1hour tana mata karatu, sudai mutane sunsama sarautan Allah ido, kawai gani sukayi mummy tayi attishawa jikinta duk yasaki, saikuma bacci da ya kwashe ta, kowa abun mamaki yake bashi, saboda babu irin adu'an da ba suyi ba amma kamar ana k'ara ingizosu, tun jiya da dare suke abu guda sai yanzu da finah tazo, " juyowa tayi zata tafi wata mata ta biyota tana tambaya plz ke wacece d'aga mata hannu finah tayi, ta sa kai tafita,,,,
Can k'asan layinsu ta tsaya batafi minti ukku ba, saiga tinah, tinah tace finah mi kikayima mummy haka, kinsan tun jiya ake abu guda, amma shiru, murmushi finah tayi ta yaye nik'af d'in da ke fuskanta tace tinah ayar Allah ce na karanta mata, kad'an daga cikin ikon ubangijina kenan, tinah babu wani ubangiji da yawuce Allah su bahanahu wata'alah duk wani wanda yace shi Allah ne k'arya yake, ayoyi da hadisai finah ta dinga jawoma tinah tana kafama mata hujja dashi, dafa ta tayi tace idan zancigaba da kawo maki misalai saimu kwana mu yini wlhi bamu gama ba, inasan yanda Allah ya tab'oni na koma hanyar gaskia inasan dukkan ku kuma Allah ya shiryeku, tana kaiwa nan ta juya ta tafi, dakyar tinah taja k'afafuwanta saboda yanda jikinta yayi sanyi, "da sallama finah tashiga gida, arif ne ya nufota da sauri sauri d'aukanshi tayi ta rungume, tagoge kwallan da suka gangaro mata, anty ce ta kawo mata abinci, saida taci tayi k'at kana ta juya kan anty tana murmushi tace anty anfa samu nasara, murmushi anty tay tace masha Allah, " tagayama anty komai, murna anty tayi ta d'aga hannu tama Allah godia, anty tace finah zaki dunga zuwa kafin daddy yadawo, in shaa Allah zasu rabu da ita, finah tace nima nayi wannan tunanin,,,,,
"Bari mu lek'a gidan moh muga wainar da ake toyawa,,,
Fadilah ce kwance jikin moh tana ta mashi shagwab'a shiko sai biye mata yakeyi, " umma ce tashigo da sallama ko kallonta finah batayiba bare ta amsa, wuri umma tasamu ta rakub'e tace na Allah wajenka nazo, "yace umma inajinki, tace dama kud'i zakaban naje ssibiti, " kafin ya bada amsa fadilah ta mik'e zaune tace tsohuwa bai badawa, saboda bai dasu ke kenan kullum baki da lafiya, juyowa fadilah tayi ta kalli moh tace wlhi dear lafiyanta lau k'arya take kawai zata kaima bokayenta ne, "umma na hawaye tace fadilah nike k'arya fadilah tace eh ay ita kikayi shiyasa, " moh yace umma kiyi hak'uri banda kud', yana fad'an haka fadilah tajashi sukayi d'aki juyowa tayi ta ma umma gwalo, tashi umma tayi tana sharan hawaye,,,,,,
Kullum sai finah taje gidansu kuma da doguwar hijab da nik'af babu wanda yasan itace sai tinah, "kuma Alhamdulillah mummy nasamun sauk'i,,,,
" yau yakama laraba, daidai da kwana hud'u da finah tafarayima mummy ruk'iya, finah ce gaban mummy suna ta badak'ala da aljannunta, saboda tanasan subarta har abada, "k'iyawa sukayi da sukaji ruk'iya sukayi magana, kuma da alkawarin bazasu k'ara dawo mata ba, " duk abunnan gaban idon mutane akayishi, "suna fita finah tace Alhamdulillah d'aga hannu tayi tama Allah godiya, juyawa tayi zata fita taci karo da babanta, tsaye, gabanta ne yafad'i, daddy yace young lady wacece ke? Kuma zan iya ganin fuskanki, saboda yanda kika taimaki matata, tarabu da ciwonta, girgiza kai tayi alamar ah ah, marairaice fuska daddt2 yayi yace plz ko bazaki amshi abinda nayi niyar bakiba, kibari inga fuskanki, "cire nik'ab d'inta tayi ta d'ago a hankali,tana hawaye suna had'a ido da daddy wata zabura daddy yayi yana nuna ta da k'arfi yace claire,,,,,,,,,
*_Dedicated_* *_biebee_* *_isa_*❤
IG: yar_ficika
© *_written_* *_by_*
*_Feedoh_* *_Deedoh_*✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment