DIJAH 76~80

🏵🏵DIJAH🏵🏵

Feedoh yanmata✍🏻

7⃣6⃣~8⃣0⃣

Kuka yaci k'arfin dijah, tace in shaa Allah baba zaka tashi, "jikin inna larai yayi sanyi, tace malam zama katashi in shaa Allah, dijah tace baba bari nasamo mota mutafi asibiti," girgiza mata kai malam yayi yace dijah kibarshi nikam nasan ciwona bana tashi baneba, kidai rik'e maraicinki Allah yamaki albarka," kuka yaci k'arfin dijah, cikin kuka taji malam  na kalmatush shahada, yana kaiwa k'arshe taji shiru, kallon Inna larai tayi da sauri, itama innar ita take kallo, wajen da malam yake kwance Inna tatafi d'aga hannun malam tayi taga ya koma kunne takai k'irjin malam shiru taji, Inna dai ta tabbatar da malam ya cika , "wani ihu datasaki saida mak'ota suka juwo fitowa tayi tana ihu tana tashiga ukku itako dijah ta dake, mak'otane suka dinga shigowa sukaji lapia, nan suka tarda malam ya rasu  kowa yaji mutuwar malam saboda mutum ne Wanda yasan darajan mak'otanshi hak'uri akeba Inna larai amma kamar Ana k'ara ingizata kamar ba musulma ba, da kyar aka samu tayi shiru,

An shirya malam za'a kaishi gidanshi na gaskia, dijah tace abari tamai adua, adua tamai sosai," dijah tace baba nagode da irin kulawarku akaina kaida mama, naso kuna raye nima namaku gata kamar yanda kuka Mani, amma kash gashi yau babu d'ayanku, kuma babu wani naku, Allah yasakamaku da gidan Aljanna Firdausi, Allah yakai haske kabarinku, nagode da irin rik'on da kukamani Allah ne kad'ai zai biyaku, duk wanda ke wurinnan saida yayi kuka, saboda tausayin dijah, "dijah nagani aka tafi da malam gidanshi na gaskia, sannan ne kuka yazo mata, kuma mutuwar mamanta tadawo mata sabuwa, d'akin lubabatu ta shige tana kuka, saida wata aminiyar lubabatu ta shigo d'akin tadinga yimata nasiha da yarda da k'addara..

Tun malam baiyi arba'in ba Inna larai tayi fatali da nasihar dayamata ta dinga gallazama dijah, duk wani aiki ita zata matashi, kuma tarabata da kowa, duk wanda yayi niyar taimaka mata saita rabata dashi, kuma tamashi rashin arzik'i dole mutane naji nagani suka hak'ura da taimakon dijah..

CIGABAN LABARI
Dijah taja hannun hanne, tace hanne kinga muyi sauri dan yau na dad'e kuma jikina zaigayamani, girgiza Kai hanne tayi tana tausayin dijah,
"Suna isa k'ofar gida, dijah tama hanne sallama, tashiga gida,"jiki sake tayi sallama amma tasan baza'a amsaba, shiga tayi gidan Inna larai tagani zaune tana faman kad'a kafa, yalban zar k'afar kamarta baby Labo #wink.....

www.phirdauceejeebo.mywapblog.com

Written by
           Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180