DIJAH 146~150

🏵🏵DIJAH🏵🏵

Feedoh yanmata✍🏻

1⃣4⃣6⃣~1⃣5⃣0⃣

Satin dija daya da farfadowa, Shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakanin dijah da Hamzariee, dan kullum yana hanyar asibiti, kuma duk idan yazo shizai bata abinci, " kuma baitafiya sai dare, "tafiyace takama Hamzariee zaije London daddy ya aikeshi, "baiso tafiyan ba saidai bayanda zaiyine, "Hamzariee ne gaban Ammi yace Amminah Allah basan tafiyarnan, "murmushi Ammi tayi dan tasan dalili, kanshi ta shafa tace haba yarona aiken mahaifinka fane, kuma duka sati guda zakayi, katafi kajiko," nasan bakomai kakejiba illah dijah yar amanarka, namaka alk'awarin zan kula da ita harkadawo, Hamzariee yace toh shikenan Ammi nagode, nabar maki amanarta, "Ammi tace nakuma d'auka kaidai Allah ya kiyaye yace Amn, affy ce ta shigo tace ya Hamzariee nasama kayan mota, "hamza yace zonan my angel, tana zuwa, yace afrah tace naam ya hamza, "hamza yace afrah ga amanar Khadijah nan, plz you should good take kia ov her, affy tace I'll in shaa Allah ya hamza, hamza yace tnx so much, "Ammi tace Hamzariee na zaka biya hospital ko?, hamza yace ah ah Ammi kedai ki kularman da ita kinji, kuma idan naje airport zankira saikiban ita, "Ammi tace flight d'inku wane tym ne, hamza yace 3:00pm, Ammi tace OK, "hakadai hamza yatafi badan ranshi yaso ba, ita kanta Ammi bataji dad'i ba saidai yazama dole saboda Aiken mahaifinshi ne.....

***************************
Haraban asibiti sukaga dijah na tafiya, tana hangosu ta dinga washe baki, "da d'an gudunta ta isa wajensu hannun affy ta kama tana dariya, affy tace dijah ya jiki, dijah tace nafa warke, " juyawa kan Ammi tayi zata duk'a ta gaidata Ammi ta d'agota ta rungume, tace ya jikinki? "Cikin kunya dijah tace da sauk'i, Ammi tace Allah ya k'ara lapia, "waige waige tafara, amma bataga wanda take nema ba, Ammi da affy sun lura da haka, amma basuce mata komai ba, "d'aki suka wuce suna zama takasa daurewa tace afrah ina yah hamza, "afrah tayi shiru, Ammi tace dijah kiyi hak'uri hamza yayi tafiya, daddy ya aikeshi amma sati d'aya zaiyi, idonta yayo narai narai kamar zatayi kuka, "Ammi takafa lallashi, affy tazuba mata abincin da suka kawo tace ta k'oshi, Ammi tayi tayi tacefa ita ta k'oshi, suna cikin haka saiga wayan Ammi tayi rngn tana dubawa taga hamza, d'aukan wayantayi suka gaisa, Ammi tace toh gadai amanar ka nan tak'i cin abinci, "mik'ama dijah waya Ammi tayi, dijah dai taga yanda suke waya, so that itama haka tayi, "shiru tayi, hamza yayi magana, yace hello dijah nah, a sanyaye tace naam, ina wuni yace lapia lau, "yace dijah kiyi hak'uri tafiya takamani, nima bada san raina ba yanda zanyi, dijah tace miyasa baka biyo mukayi bankwana ba, "hamza yace nayi laifi amma kiyi hak'uri kinji? ,"dijah tace shikenan, yaushe zaka dawo? Yace sati d'aya zanyi, kuma namaki alk'awari idan and'aukoni airport ko gida bazanjeba sainazo naganki, dijah tace shikenan,"hamza yace tsaya Ammi tace kink'i cin abinci, kinasan nak'i dawowa, kakuma my b'ata, dijah tace ah ah, yace toh kici abinci, dijah tace shikenan zanci, "hamza yace yawwa dijatunah kiman adua kinji, tace shikenan Allah yamaidoka lapia, "hamza yace Amin nagode, tamik'ama Ammi waya sunyi fira, duk kan dijah ne, "sukayi bankwana, "Ammi tace toh yanzu zakici abincin ko? Rufe fuskanta tayi, tana dariya, dariya affy tayi, "haka dijah ta dingacin abinci da kanta, turawa kawai take, bawai dan yana mata dad'i ba, "saboda Hamzariee yasaba shike bata, batawani ci dayawaba ta aje, " sai yamma sukatafi, "kafin su taxi ansha fama dan kuka ta saka wai ita asibitin ya isheta, dak'yar aka samu tahak'ura, dan saida Ammi tace toh baxata k'ara zuwa ba, nan kuma ta dinga ba Ammi hak'uri, "hakadai aka lallab'ata suka taho.........

www.phirdauceejeebo.mywapblog.com

IG: yar_ficika

Written by
           Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180