DIJAH 236~240

🏵🏵DIJAH🏵🏵

Feedoh yanmata✍🏻

2⃣3⃣6⃣~2⃣4⃣0⃣

Aiki akeyi a garinsu malam sosai, Hamzariee yasamo masuyin aykin, aikin akeyi ba dare ba rana, "sati biyu aka gama komai, saboda kowa dayaji maganan saida yabada guddumuwa, harta affy saida ta bada, "yau ne za'a bud'e masallatan da islamiyoyin da rijiyoyin da dijah ta gina, "duk abinnan da akeyi Inna bata saniba, saida sukaje bakiyawa, "anzo unguwarsu amma tarasa gane inane gidan, saidataga anshiga amma still bata ganeba, saboda anmaida gida plat house, "kasa hak'uri tayi tace Hajia wai wane gidane nan? Dijah ce tabata amsa tace Inna gidanki mana, tace wane gidan nawa kuma, tace wanda kikaci gado wajen baba, sannan dijah ta labarta mata komai da duk abinda tayi, tace Inna yau za'a bud'e masallatan, "fashewa da kuka Inna tayi tace lallai Khadijah kin haihu, Allah yasaka maki da alkairi, ya ja kwananki da na iyayenki, dijah tace Amin, da kyar su mama suka samu tayi shiru, "numfasawa Inna tayi, tace dijah wannan gida ba nawa baneba, nikad'ai, kafin malam ya rasu cewa yayi nidake, murmushi dijah tayi tace hakane Inna amma nabarmaki duniya da lahira, "Inna tace ba'ayi hakaba, dijah ba'asan gawar fari ba, amma inasa ran na rigaki mutuwa, kinga kenan bamai zaunar gidan, "daddy ne yace gaskiane Inna yanzu abinda za'ayi a bar gidannan duk wanda yazo cikinku saiku dinga sauka, Inna tace haka yayi, dijah ma tace haka yayi, "abaya dijah tasaka black tayi rolling da scarves tayi kyau sosai, Hamzariee kasa d'aga idonshi yayi a kanta, saida tace malam kallon ya isa hakanan, wajen bud'e masallaci da islamiya suka tafi, nan aka bud'e taro da adua, akayi bayanin mak'asudin wanan taro, sannan kuma dijah tace islamiyar ta bud'eta kyauta ne, sabida taimakon wanda basu dashi, dakuma Allah yakai ladan kabarin malam da lubabatu, wasu harda kuka, tasha albarka, "sai yamma lik'is sukadawo, duk tagaji, bankwana Hamzariee yamata dan gidansu naf zaikwana, "wanna tayi dan dama tana fashin sallah, abinci taci sukad'anyi fira da affy ta kwanta, "cikin barcinta ne tayi mafarkin malam da lubabatu, sunzo wajenta, cikin fararen kaya, "zama sukayi kusa da ita, malam yace uwata mungode sosai Allah yasaka maki da alkairi kuma in shaa Allah saikinfi haka, kuma nagode da irin d'awainiyar dakike da larai, lubabatu tace nima iyakar abinda zance maki kenan, mungode, "malam have toh d'iyata zamu barki, tashi sukayi, dijah tace mama baba dan Allah karkusake barina karo na biyu, wlhi ina buk'atarku kusadani, dariya suka dinga mata suna d'aga mata hannu harsuka b'ace itako saifaman kiransu takeyi, girgixata akayi, firgigit ta bud'e Idonta tanata waige waige, affy tace wai lapiarki kuwa, dubi tym 2:39am fa, shiru dijah tayi, tashi tayi taje ta d'auro alwalla tafara sallah,

*****************************
Akwana atashi ba wuya wajen Allah, yau saura sati biyu bikinsu dijah, gidajennan biyu, shirye shirye kawai sukeyi, suko amare ba zama rabon iv suketayi, dijah ce da feedoh suketa faman rabon iv gidajen k'awayensu, ga gyaran jiki anama amare, duk idan kagansu saisun baka sha'awa sun burgeka, badai kamar dijah, "datayi wani irin kyau, "dijah ce suka dawo gida da marece lik'is tana shiga taga inna nata washe baki, feedoh tace Inna lafiya, Inna tace lafiya lau feedah murna nake, feedoh tace aykinji ke Inna kowa saikin b'atama suna, Inna tace toh kema wannan suna kamar wata arniya, kudai yan buri abarku da abinku, dijah inbanda dariya ba abinda takeyi, "Inna tace dijah anfa kawo lefenki, amma wanan lefe na mata ashirin ne, murmushi dijah tayi suka haye sama, tabbas lefen dijah yayi saboda akwati 12 aka sakamata, ga tsarkanta ta gwal, kai gaskia ban iya gaya maku abinda akasaka, dan idan nace zan lissafa akwai aiki, itama affy naf yayi k'ok'ari saboda akwati goma yasa mata.....

Yau akaje akaima amare jere, inda wasu sukatafi kd gidan affy akamata Jere, dayake naf can yake aiki, "wasu kuma suka tsayanan abuja akama dijah jere, gidanta dake maitama, gaskia daddy yakashe kud'i saboda kowace saida aka mata 4bedroom da 3parlor gaskia gidajen amare yayi kyau, saidai fatan Allah yabasu zaman lapia da zuri'a d'ayyaba, "yau ne za'a fara event....

www.Phirdauceejeebo.mywapblog.com

IG: yar_ficika

Written by
           Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180