DIJAH 176~180
🏵🏵DIJAH🏵🏵
Feedoh yanmata✍🏻
1⃣7⃣6⃣~1⃣8⃣0⃣
BAYAN WATA BAKWAI
Komai yafaru cikin wata bakwai, cikin harda shigan dijah skul, inda tashiga premier international skul, js3 suka d'auketa saboda taci exams d'insu dan Allah ya zubama dijah kwanya, abin har tsoro yake basu da anyi abu nan da nan ta hardace,b'angaren hamza kuwa haka yacigaba da dakon son dijah, shi baigaya mataba, amma kowa yaganshi zaigane ramar dayayi, yakuma canja yakoma shiru shiru, "abin nadamun Ammi, takuma tambayeshi yace bakomai, "Ammi ce ta sami dijah da affy parlor suna kallon wani India, Ammi tace dijah, amsawa tayi, Ammi tace dijah kije ki tambayi yayanku, mike damunshi kwana biyu ya canja, "dijah tace Ammi nima abun na damuna wlhi, kwata kwata yadaina sakewa damu, affy tace wlhi Ammi duk mundamu, Ammi tace dijah wanan aikin kine plz kibincikaman matsalan yarona, "murmushi dijah tayi tace in shaa Allah, "dijah ce ta had'a tray d'in abinci ta nufa d'akin Hamzariee, sallama tayi, shiru ba'a amsa ba, tura kai d'akin tayi, ganinshi tayi kwance ya tsurama tv ido kuma ba kallo yakeba, saida ta razana data ga wani bak'i da rama da yayi, wajen gadon tanufa, takai minti biyar tsaye amma baisan tashigo ba, nikaina yar ficika na tausayama hamza saboda soyayya bata kamashi da wasa ba🤔,"kanshi ta shafa tareda girgizashi a hankali, firgigit ya farka, murmushi ya mata yace dijatunah yaushe kika shigo, d'aure fuska tayi, tace ina zakasa. Shigowa na, kana Neman hallaka kanka, ka sama mahaifiyarka hawan jini, "saboda tadamu da halin daka saka kanka, murnushi yayi yajawo hannunta, dab dashi tazauna, yace kiyi hak'uri dijatunah kedai kiman adua, "tab'e baki tayi tace naji, abinci tajawo ta dinga bashi, dandole take cin abincinnan, dan yasan idan yak'i ci akwai rigima, "tagama bashi abinci takwashe kayan dawowa tayi tazauna kusa dashi, tace ya hamza magana nakesan nayi dakai, yace dijatunah ina jinki, "tace ya hamza inasan nasan damuwarka kagayaman miye matsalarka, plz ya hamza ka daure kagayaman damuwarka, wlhi bansan ganinka cikin damuwa, danuwarka da muwata tace, hannunta yakamo yace dijatunah ba abinda Zan b'oye maki kiban kwana biyu zangaya maki damuwata in shaa Allahu, girgiza kai tayi tace shikenan Allah yakaimu tace Amin, hamza yace yaushe zaku fara exams? Dijah tace next week, yace Allah shikaimu, dijah tace 2dayz fa bamuje wajen koyon mota ba, hamza yace ki shirya muje yau....
*****************************
Yau ne kwana biyun da Hamzariee ya bawama dijah akan zai fad'a mata da muwarshi, "tun safe take lallab'ashi ya gaya mata amma ya k'iya, sai hanya hanya yakemata, d'aki ta rutsashi, ranta b'ace tace ya hamza na gode, yau kanunaman ba jininka nakeba, na tabbata inda affy ce daka gayamata da muwarka, amma ba wani abu, kuma in shaa Allah bazan k'ara shiga harkanka ba, juyawa tayi zata fita, da sauri ya rik'o hannunta, juyowa tayi cikin tsiwa, gani tayi hawaye na binshi, dasauri ta matso inda yake, tace ya hamza maganan danamaka ita tasaka ka kuka? Dan Allah kayi hak'uri wlhi i don't mean 2 hurt u, kawai dai naga ya dace nasan matsalanka, plz on mah kneelz yayana kayi hak'uri, murmushi yamata na k'arfin hali, yace basaboda maganan da kikaman bane nake kuka, kawai bansan yanda zaki d'auki maganar da zamuyi baneba, zama tayi tace karkadamu, ya hamza kaidai kagayaman matsalanka.....
Hamza yace dijah sanki nakeyi, mik'ewa tsaye tayi cikin razana tace so? Wane irin so kuma, dan Allah ya hamza kayi hak'uri taya soyayya zata shiga tsakaninmu, kasan kowaceceni, niba yar asali baceba, asalima ni shegia ce, taya zakaso shegiya marar asali, janyo ta yayi, yace dijah koya kike wlhi naji nagani, inasanki, sankuma da ban iya dainawa sai randa na daina numfashi, kumama koda ke shegiya ce ayba laifinki baneba, bareama inaji ajikina kinada uwa da uba kamar kowa, "dan Allah dijah karda nice bakisona wlhi zan iya rasa raina, kuka tafashe da shi tace hamza kanaso nabar gidanku kenan dan na tabbatar duk idan iyayenka sukaji basu barina, Allah sarki nikuma haka rayuwana zata k'are a gararamba, Allah yajik'anki mama nasan dakina da rai,da duk haka bata faruba, rufe mata baki yayi, yace dijah kiyi hak'uri nima bansan sanda nafara sankiba wlhi, danasan zansoki da banbari na shak'u dakeba saboda bansan jefaki cikin Matsala, "wlhi dijah bantab'a san wata ba saike, bansan ya so yakeba sai akanki, dan Allah kiji tausaina karki barni, wlhi bazan iya cigaba da numfashi ba idan baki kusa dani, "kuka ta fashe dashi, daidai Ammi tashigo d'akin saboda taji maganganunsu kaf, hankalinta yatashi, tana shigowa ranta b'ace dijah tana ganin Ammi ta bar d'akin da gudu tana kuka.............
www.phirdauceejeebo.mywapblog.com
IG: yar_ficika
Written by
Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment