JINSINAH 71~75

❄❄ *JINSINAH* ❄❄

*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻

*_page_* 7⃣1⃣ *_to_* 7⃣5⃣

Amir ne ya kalli hannunshi yace Aysha bari naje na kawo maku kayan buk'ata tunda na tabbata ba abinda zasu kawo, Anty tace hakane kam, yakai k'ofa sukaci karo da moh, "amir ne ya mik'ama moh hannu suka gaisa moh yace saikuma Ina, amir yace zanje gida nakawo masu abinda zasu buk'ata, moh yace hakane bari mugaisa da Anty inzo muje, "shiga moh yayi da sallama da kyar Anty ta amsa mashi dan haushinshi takeji, gani takeyi yanada damar da zai fidda finah wannan halin amma yakasa, "moh ne ya gaidata ta amsa ba yabo ba fallasa, shikuma baikawo komai aranshi ba, "tambayarshi tayi yamai jiki ya amsa Mata, dasauki, "moh yace bari naje amir na jirana, "OK Anty tace,,,,,

       "Bari mulek'a wajen fadila, "tinda Fadilah yashiga d'aki take tarasa inda zatasa kanta, shekara da shekaru tana neman haihuwa bata samuba, amma daga zuwan tubbabbar nan ace tana da ciki, "wayanta ta d'auko takira k'awarta habiba, "habiba nad'aga wayan Fadilah tace habiba komi kike kibari kizo Ina nemanki, habiba tace lafiya Fadilah tace ba lafiya ba kedai kizo yanzu,,,,,,,,,,

Zagayen d'aki takamayi, ta rasa dubara, "sallama habiba tadinga kwalawa, Fadilah ta kasa amsawa, "d'akin Fadilah habiba tanufa, tana zuwa ta tarda ta tanata zagayen d'aki, dafata Fadilah tayi tace haba hajiyana mike faruwa naganki haka, ji duk yanda kika koma, haba Fadilah calm down mana, idan kinasa damuwa cikin ranking Allah bazamuci ribar abinda mukeso ba,,,,,,
                    ***

Wurin Fadilah tasamu tazauna taja dogon numfashi, saikuma hawaye, shinefa yak'ara tadama habiba hankali, saboda duk abinda zakaga yasaka Fadilah kuka toh ba kad'an baneba, "habiba tace kima Allah kifad'aman abinda ke damunki, "Fadilah tace habiba ke shaidace yanda nakesan haihuwa, amma nakasa samu, kuma likita yagayamani bazan haihuba, saboda magungunan dana dungasha, lokacin da Ina budurwa, gashi mahaifana ta lalace, kuma duk kinsan haka, "toh yau abin tashin hankali, yanzu wannan tubabbar daga zuwanta tanada ciki harna wata ukku, "razana habiba tayi dataji ance finah nada ciki,,,,

        "Tace fadilah ciki fa kikace? Girgiza kai Fadilah tayi tace abinda nacekenam, "fadilah tace wlhi baiyuwa bata isa tahaihu a giddannan ba, saboda ba gidanta baneba gidanki ne ke kad'ai dan haka wannan cikin badai a haifeshiba, saidai tayi b'arinshi wlhi,,,,

Wa'iya zubillah gaskia wasu basuda imani, Allah ka karemu da mugayen k'awaye *_Amin_*,,,,


                 "Fadilah tace yanzu habiba miye abinyi? Murmushi habiba tayi tace karki damu nasan abinyi indai bokaye nada rai toh mukuma buk'atunmu zasu biya, ke dagayau kifara lissafa finah cikin layin juyayyu, saboda mahaifarta zansa ab'ata gaba d'aya kedai kawai kijuye kudi "murna Fadilah farayi, tarungume habiba tace shiyasa nakesanki kawata, nagode kwarai bakida matsala indai kud'ine, "tashi tayi taje side bed d'inta tad'auko kud'i dubu d'ari ukku, tamik'ama habiba tace gashinan idan basu isaba kiman magana, amsa habiba tayi tace karki damu gobe in shaa Allah zanyi sammako naje bankwana sukayi habiba tatashi tawuce,,,,,,,

          "Satin finah biyu  asibiti amma babu Wanda yazo ganinta, daga Umma har Fadilah "yau ne dr safiiyya ta sallami finah, Anty ce tace moh yakamata natafi da finah gidana saboda tak'ara jin sauki, "moh yace Anty kiyi hak'uri takoma gidanta, "anty tace haba moh katausaya mata mana kaga halin datake ciki na tabbata datakoma aiki zata farayi, moh yace Anty zanyi iyakar k'okarina naga bata koma aikin wahala ba dan Allah kiyi hakuri, "Amir ne yasa baki yace idan kintafi da ita lafiya zaki bata, haba Aysha kidinga saka tawakkali aranki, kibarshi yatafi da matarshi, Anty tace shikenan "dama wai danta k'ara warwarewa shiyasa, kodayake jikin ay yayi kyau,,,,,,,

            "Street gidan moh aka wuce, itakanta finah batasoba, dantasan azabar dazata komamawa, suna shiga su umma da fadilah sukagani, bakin gida, gaidasu sukayi amma babu wacce ta amsa bare atambayi yamai jiki, part d'in finah suka wuce duk yayi k'ura nanfa anty tazage tadinga gyara saidataga komai yayi daidai kana, "zama tayi tadinga ba finah shawarwari, Anty tace finah saikin dage da adua kada kizauna, saboda mutannen na, "kuka finah tadingayi tace wlhi Anty danasan haka *JINSIN* hausawa yake da banbar *JINSINAH* ba, Anty tace haba finah mike damunki, kada kiyi sabo, "k'addaranki ke haka, hakuri zakiyi kedai adu'an danace kiyi ita zakiyi, finah tace shikenan, "sai la'asar kana Anty Aysha suka tafi itada amir,,,,,,


           "Habiba ce tashiga part din Fadilah ta Nata kwada sallama,amma shiru, can uwar d'akinta tasameta, habiba tace ayta sallama shiru, Fadilah tace waya nagamayi "yaushe kika dawo, habiba tace ko gida banjeba, waje tasamu tazauna, ta bud'e jikkarta ta d'auko garin magani, tace ki kula dashi, cikin abinsha zaki Samara, idan hartasha, hmmm toh saidai wata *NAFISAR* tahaihu amma badai wannan ba, "rungumeta Fadilah tayi tace nagode kawata Allah yabarni dake "habiba tace amin kawa,,,,,,

*_TURK'ASHI_*🙆🏼🙆🏼🙆🏼

*_Dedicated_* *_to_* *_biebee_* *_isa_*❤

IG: yar_ficika


© *_written_* *_by_*

             *_Feedoh_* *_Deedoh_*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180