DIJAH 196~200

🏵🏵DIJAH🏵🏵

Feedoh yanmata✍🏻

1⃣9⃣6⃣~2⃣0⃣0⃣

Ammi tace sai yanzu, ayda muntafi munbarku, hamza yace Ammi fa mune jigon tafiyan, gaba d'aya akayi dariya, duk suka shiga mota, "basu tsaya ko inaba sai asokoro, wajen wani black gate sukayi parking horn sukayi, maigadi ya lek'o yana ganin motan Alh Lawal ya wangale gate, danna kan motatocinsu sayi cikin gidan, wajen haraban aje motoci suka tsaya duk sukayi parking suka fito, "hanyar parlor suka nufa, suna shiga parlor nan naga aljannar duniya, wata hanya naga Alh Lawal yabi yayimasu daddy izinin su biyoshi, wani parlor nagani, nan naga sakin baki wajen dijah tana kallo, "nikaina feedoh saida na girgiza da ganin irin dukiyarsu dijah, ashe d'iya da gantanta tayi wahala k'auye, Alh Lawal yace yana zuwa, bari yama zainabu magana, daddy yace toh , sama bene naga ya nufa, ba'a dad'eba saigashi sun sakko tare ita dai dijah kanta na k'asa zuciyanta saifaman bugawa takeyi, tana sakkowa suka gaisa da su daddy da tambayarta jiki tace jiki yayi sauk'i affy da hamza suka gaidata, amsawa tayi cikin kulawa, dijah dai kanta na k'asa itakuma zainabu tak'urama dijah ido sota keyi ta d'ago, a hankali dijah tafara d'agowa baki na rawa tace ina wun....... Bata idaba Hajia zainabu ta mik'e tsaye tana nuna dijah da hannu, tace Alh ina kasamo mai Kama da d'iyata, "kodai na haukacene, Allah kabani ikon dangana, gashi ina neman haukacewa, tadinga sambatu, dijah inbanda kuka ba abinda take, "takawa dijah tayi taje gabanta tace ba hauka kikeba nice d'iyarki, wadda kuka yarda, saikuma tafashe da kuka, "rungumeta Hajia zainabu tayi tace kigafarceni, wlhi banina yardaki ba, rabani akayi dake, babu wanda baiyi kuka ba parlor nan, "saida sukayi kuka mai isarsu kana aka lallashesu, Hajia zainabu ta d'aga hannu tace Allah nagode ma daka maidoman d'iyata gida, Allah yak'ara tsareta da dukkan musulmi baki d'aya, su daddy sukace Amin.....

*****************************
Shiru parlor ya d'auka kamar ba kowa Hajia zainabu tace Alh ya akai kuka had'u, Alh yace gidan Alh abubakar, zainabu tace Allah sarki, Alh Lawal yace dijah kibamu labarinki, "dijah tace toh kamar yanda nagaya maku daddy......... Nanfa ta kwashe labarinta tagayama iyayenta babu abinda ta rage, "Hajia zainabu kuwa inbanda kuka ba abinda take, Alh Lawal yace Allah yajik'an malam da matarshi da Rahma, naso suna raye da saisunga gata irin wanda suka maki, "amma ko yanzu ita Inna larai d'in zanuje zanganta, saboda malam, kuma Allah ya shiryeta yasa tayi nadama duka akace Amin, "abinci aka dinga jera masu saida sukaci suka k'oshi "kana sukatashi suyi sallah, su daddy suka wuce masallaci sukuma su affy aka gwada masu d'aki, bayan sungama sallah dijah ta kalli affy tace sis dama haka mutum keji idan yana tare da iyayenshi? Lallai iyaye Rahma ne, "Allah na godema daka gwadaman iyayena, suna cikin fira hamza ya shigo, affy tace bruh nan ma saika biyota, yace "eh ina ruwanki, dariya affy tayi, hararan dijah yayi, tace charming mikuma nayi, hamza yace aykinsani, tunda mukazo gidannan kike wani shareni, kuma Allah saina had'aki da baba, dijah tace sowee my d'an saurayi wlhi ban sharekaba, nina isa nashare mijinah, tab'e baki affy tayi tace kunji dashi dai, hanun dijah Hamzariee Yakama yace muje su daddy nakira.....

Suna dawowa parlor suka zauna shiko hamza yana nan lik'e da dijah inda tazuna nan ya zauna, Ammi sai hararanshi takeyi amma k'ememe yayi kamar baisan mitakeyiba, afyy dake kallonsu saifaman gumtse dariya takeyi, "dijah tace baba ya akayi wai narabu Daku? Alh lawal yace yanzu kuwa zakiji, kallon zainabu yayi yace Hajia bismillah..

*****************************
Hajia zainabu tace kamar yanda kukasani, Alh Lawal shine mahaifinki, yana da mata d'aya mai suna Hajia karima, shekaransu 20 da aure amma basu tab'a haihuwa ba, abun duk yadamesu, Alh Lawal yayi tunanin yak'ara aure, bazan mantaba Alh Lawal yaje wajen mahaifina saboda yataimaka mashi da adua, nikuma nadawo islamiyya, naduk'a nagaidashi ya amsa, ina shiga cikin gida yacema mahaifina wannan fa? Murmushi mahaifina yayi yace zainabu kenan auta tatace Alh Lawal yace ammata miji? Banana yace ah ah, Alh Lawal baiyi k'asa a gwuiwa ba yace idan ba damuwa yanasan abashi aure na, "banana yace bakomai amma kabari zanyi shawara da mahaifiyarta, gobe idan Allah yakaimu saikadawo Alh Lawal yayi godia yatafi, "mahaifina yana shiga gida yataramu, yacema mahaifiyata dama Alh Lawal ne yaga autarki yanaso, mahaifiyata tace ay malam hukunci na wurinka, "kallona yayi yace zainabu kinji, idan kinsan baimaki ba, karki ji kunyata, nace abbu wlhi bakomai na amince dama mijin farko ay alhakin iyayene suzab'arma d'iya, dan haka idan yayimaka nima yayiman, abbu yace nagode kwarai xainabu Allah yashimaki albarka, nace Amin...,

🏵🏵DIJAH🏵🏵

Feedoyanmata✍🏻

2⃣0⃣1⃣~2⃣0⃣5⃣

Washe gari Alh Lawal yadawo, yayi sallama da mahaifina, "mahafina yafito suka gaisa Alh lawal yace nazo maganar mu, banana yace bakomai duk sanda ka shirya ka aiko, godia Alh Lawal yayi, babana yace bansan komai naka sadaki kawai nake buk'ata, godia Alh Lawal yayi, "koda Alh Lawal yaje yagayama matarshi tatada hankalinta, tace alh nizakama kishiya dan bantab'a haihuwa ba, toh wlhi kozanyi yawo tsirara bawadda zata shigo gidana, Alh Lawal yace aure in shaa Allah ba fashion kije kiyi duk abinda zakiyi..

Alh Lawal ya aiko iyayenshi da sadaki, aka biya sadaki tare da tsaida ranan aure wata guda, "Hajia karima tatada hankalinta, babu abinda batayiba amma ba abinda aka fasa, "akwana a tashi, ba wuya, aka d'aura aurena da alh Lawal, aka kaini gidana alh Lawal bai had'amu ba, saboda yasan halin matarshi, "watana ukku nafara laulayi, ayko murna wajen alh ba'a magana, Hajia karima dataji ranan anyi tashin hankali, ba abinda batayiba, dan ciki ya zube amma ciki ba abinda yayi, "wata tara na cika nahaifeki, zokiga murna wajen babanki duk Wanda yazo barka saiyace Masha Allah, mahaifinki yamaki hud'uba da fatima"Hajia karima batazo barka ba, said a nakwana biyar da haihuwa tazo, faran faran tamani, takawo kayan barka, dangina suka amsa suna godia..

Asuba nayi natashi dubawa nayi bangankiba, "nace ko goggo ta goyakine, goggo ta shigo d'aki nace goggo ina jaririya tace yo ayke zan tambaya, tace aybangantaba, wasa wasa aka nemeki aka rasa haka kika b'ace kamar allura alh aka tado aka fad'a mashi nan fa aka karad'e gida da nema aka nemeki aka rasa alh Lawal yayi kuka, Niko danaga ba'a gankiba har gari ya waye yanke jiki nayi na fad'i.....,..

www.phirdauceejeebo.mywapblog.com

IG: yar_ficika

Written by
           Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180