JINSINAH 91~95
❄❄ *JINSINAH*❄❄
*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻
*_Page_* 9⃣1⃣ *_to_* 9⃣5⃣
Dafashi amir yayi, yace haba moh ka saka dangana aranka, shin idan "finah ta mutu kana da abinyi ne? "Dama kwananta suka k'are kayi tawakkali, kaifa musulmine mumini ba irin *_Jinsinmu_* aka sani darashin tawakkali ba, haba moh, "cikin kuka moh yace wlhi amir da gangan takasheta, ina shigowa naga tasaka mata k'afa, mi finah tama mamana da matata haka, "toh wlhi yanda Fadilah takashe finah nima saina kasheta , yakuma fashewa da wani irin kuka, maicin rai, "amir yace kada kace Fadilah takasheta itace dai sila, dakuma kwananta da yak'are, kaidai ka rungumi k'addara Allah yasa abinda aka ciro yana da rayuwa Allah kuma yarayashi,,,,,,,,,,,,,
"Itadai dr Safiyya binsu kawai take da ido, "gaskia moh yabata tausayi sosai, tabbas tasan ba son wasa moh yakema finah ba, "saidai gashi sukuma tasu k'addara aure haka tazo masu, " kallonsu dr tayi, murmushi tayi, tace moh ashe haryanzu rigimarka na nan, "toh ka kwantar da hankalinka, finah na nan bata mutu ba, "wani d'agowa sukayi tare suka kalleta, d'aga masu kai tayi, tace *yeah* *shez* *alive* , wani irin ihu moh yasaki, saikum kuka, d'aga hannunshi yayi sama yanama Allah godia ga hawaye yana bin kuncinshi, "shikanshi Amir saida yayi kukan dad'i, "yana gama adua, rungume, amir yayi, yace Amir kaji ance bata mutuba, bubbuga mashi kafad'a amir yayi, yace aikin Allah kenan moh, "kallon moh dr Safiyya tayi cikin sha'awa itadai komai nata burgeshi yakeyi, gaskia tasan tayi asaran namiji,,,,,,
"Amir yace dr shikuma abinda aka Ciro mata kumafa, "dariya dr tayi tace ayna aza bakusanshi, tunda babu Wanda yadamu dashi, kunata finah, "dariya sukayi, moh yace yaza'ayi mu manta, kedai kawai bazaki gane baneba, dr ta harareshi tace dama yaza'ayi Nagane wannan aysai kai, "dariya moh yayi, yace to amaryan hanif on my kneels , "kidaure ki ida ladanki, dariya tayi,,,,,,,
************
Dr Safiyya tace Alhamdulillah munyi nasaran aikinmu, kuma mun ciroma finah *bouncing baby boy lafiyayye dashi mai kama da babanshi, wata irin farin ciki naga moh yanayi, Wanda ni Yar* *ficika* idan nace zan rubuta makushi toh wlhi zamu kwana mu wuni munayi, nabarku masu karatu Ku auna kugani, "Alhamdulillah abinda yake fad'a kenan, rungume amir yayi, yana Murna, tabbas shima amir wani irin farin ciki yakeyi, "tabbas Allah ba azzalumin kowa baneba, yanda Fadilah kesan taga bayan finah in shaa Allah bazata samu sa'a ba, duk cikin zuciya amir ke wannan magana,,,,,,,
"Moh yace dr zamu iya ganinsu, girgixa kai dr tayi, tace zadai ku iya ganin babyn, saboda ita gaskia koda zata farfado sai zuwa jibi kaga kwana biyu kenan, kuma bamuso adamu patient dinmu da surutu, cz faduwar datayi ta bugu, so dan haka munaso ta huta, mahaifanta shima yahuta, "tabbas finah nada sauran kwana gaba, dan yanda naga jinin data zubda wa yaban tsoro, Alhamdulillah gashi yanzu tana da sauran rayuwa, "hawaye suka gangaroma, moh tabbas finah nacikin wani hali, "girgiza mashi kai dr tayi tace ba kuka zaka Mata ba adua zaka Mata kaji,,,,
"D'aga kanshi yayi yace in shaa Allah dr, waya tajawo takira, Ana d'agawa naji tace kungama shirya babyn? Banji mi akace ba toh kikawoshi, "Jim kad'an saiga wata nurse ta shigo da sallama rungume da baby, "tana zuwa dr ta nuna mata moh tace bashi, "hannunshi na kyarma ya k'arba, "Masha Allah baby mai kyau, Kama yake da babanshi, "farin ciki marar misaltuwa,moh keyi, rungumeshi yayi, yana hawayen dad'i, "dr da amir suna mashi dariya, "amir yace dr dama kuna saida Kayan baby? Dr tace mikagani? Amir yace naga bamuzo da komai ba na haihuwa yanzu kuma ga yaro cikin kaya, "murmushi dr tayi tace kuduka ay d'azu rud'e kuke, "shiyasa naba wata nurse kud'i ta siyo, cz ku bakusan ma mi kukeyiba a d'azu, dariya amir yayi, banda moh Wanda tunda ya k'arbi baby yake tafaman kallonshi yana murmushi,,,,,,
"Waya amir yayi, tana d'agawa, yace congrats kinyi miji, wani irin ihu Anty tayi, amir yace karki fasaman dodon kunne, nidai, muna softies hospital, Anty tace gani nan, "bari nani d'in suhaila tadawo, saina barsu gida, amir yace toh shikenan, ya aje, "amir yace toh moh bani babyn nima nagani, ka rik'e yaro, kamar yau kafara ganin baby's dariya sukayi gaba d'aya ya mik'ama amir, baby, dr tace nidai kutafi resting room kubarni nayi aikina, idan yayi kuka akwai nurse din dazata kula dashi, "dariya moh yayi yace korarmu kikeyi KO? Dr tace eh, amir yace ayda gaskiayanta, fita sukayi suna dariya suka nufa resting room,,,,,,,,,,,
*_Dedicated_* *_to_* *_biebee_* *_isa_*❤
IG: yar_ficika
© *_written_* *_by_*
*_Feedoh_* *_Deedoh_*✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment