DIJAH 91~95
🏵🏵DIJAH🏵🏵
Feedoh yanmata
9⃣1⃣~9⃣5⃣
Kwanan dijah ukku da dawowa asibiti, kuma Inna larai bata tanka mata, saboda ta tsorata dataga dijah tasuma ta da'uka ta mutu, saidai kwanakinan ukku inna ko sau d'aya bataba dijah abinciba, "hanne ke kawomata safe rana dakuma na dare, kuma inna batasan hanne nakawoma dijah abinci ba, "yauma kamar kullum hanne ce takawoma dijah abinci, sallama hanne tayi babu kowa tsakar gida d'akin dijah ta wuce zaune ta tarda ita tana lazimi, "murmushi dijah tama hanne, hanne tace ya jikinki? Dijah tace dasauk'i sosai, "hanne tace dijah Inna ko ta shigo? Girgiza Kai dijah tayi tace wlhi ko sau d'aya, "nagode kwarai da gaske hanne Allah yasaka da alkairi inbarcinke da yunwa ta k'arasani, "hawaye hanne keyi tana k'ara tsanar Inna a ranta, hanne tace bakomai dijah wlhi kinfi haka wajena, Allah yabaki lapia , dijah ta amsa da amn, haka sukacigaba da hira hanne na k'ara kwantarma da dijah hankali......
*****************************
Inna larai ce ta banko d'an kyauren d'akin dijah tana huci, tace dan uwarki haryanzu baki warkeba kodan kinga nasamaki ido shegia kai, toh wlhi yay ko mutuwa kike kina dawowa saikinman aikina, munahukar banza, aydama tsintartar mage bata mage, wadda uwarta tayi abun kunya, itadai dijah kanta k'asa inbanda kuka ba abinda takeyi, dakuma tsanar rayuwar datake ciki yanzu, ita kad'ai take tunanin abinda zatayi dan gaskia hak'urinta yayi yawa, "nikaina feedoh bansan mi dijah zatayba🤔🤔 Allah kad'ai yasani saikuma ita dijar.......
Ahankali dijah ta d'ago tace inna kiyi hak'uri jikin nawane ba kwari shiyasa ban fitoba, tsawa inna ta daka mata, tace eh lallai dijah iskancinki yayi yawa dan uwarki ina fad'a kina fad'a ko? ,"toh ba kwari jikinki baidashiba ko yau aka haifeki saikinman aikina dan uwarki shegia gantalalliya kawai, maza ki fito kiman aikina Kuma ki gama kije kid'auko ruwa, dan gaki cikin gida bazan kama neman almajirai ba, "dijah tace goggo ina iya fad'uwa bata rufe bakiba taji saukar mari wanda saida ya gigitata, inna tace dijah nikike gayama magana haka, dan ubanki, wlhi yau saikingayama jikinki shegia yar iska Kai, "wayar wuta inna ta d'akko tazane dijah, kuka dijah keyi amma ina saidan kanta ta kyaleta, inna tace kuma kifito kiman aikina shegia kawai, kafin kace mi jikin dijah yayi zafi kamar garwashi, "haka ta dafa bango ta fito tana hawaye.....
www.phirdauceejeebo.mywapblog.com
Written by
Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment