DIJAH 71~75
🏵🏵DIJAH🏵🏵
Feedoh yanmata✍🏻
7⃣1⃣~7⃣5⃣
Haka rayuwa ta kasance gidan malam yau dad'i gobe babu, dijah kuwa kuwa rayuwa ta mata k'unci saboda idan kaga dariyar dijah toh malam na nan, "amma da zaran malam bainan duk aikin gidan dijah zatayishi ga bugu da zagi da Inna larai ke Mata, saidai kuma koda wasa dijah bata tab'a gayama malam halin datake ciki ba,"saidai raman da dijah keyi tana d'agama malam hankali, kuma idan ya tambayeta cewa take babu komai, haka dai malam yacigaba da ba dijah taimako, gani yake kamar rashin lubabatune ke damunta, baisan harda axaban Inna larai ba...
Haka dai malaam yacigaba da ba dijah taimako, kuma cikin ikon Allah tafara sama ranta dangana, saidai haryanzu babu k'iba sai wani fari datayi, kuma azaba sai wadda ta k'aru wajen Inna larai, dan kullum da kalar azabar datakema dijah, amma idan malam nan shiru zakaji....
***********************
Akwana a tashi ba wuya wajen Allah, yau shekaran lubabatu biyu da rasuwa, dijah hartafara saba da azabar inna larai,"ranan wata litinin malam yatashi da wani irin zazzabi, "abu kamar da wasa amma jiki yayi tsamari, Inna larai ya kira ita da dijah, malam yace larai nasan sarai baki daina matsama dijah ba, kawai dai na kauda kaine saboda hadiza bata gayaman ba, ina rok'onki dakiji tsoron Allah kirik'e marainiyar nan da amana, saboda nidai inaji araina bamai tsawon kwana baneba, kuma bantab'a haihuwa ba sai dijah da Allah yabani amanarta dan haka gidannan nabarmaku kucigaba da rayuwa har randa dijah zatayi aure, kuma ko bayan raina kika kori dijah wlhi banyafe makiba, "uwata nadawo gareki, dakiyi hak'uri da halin da zaki tsinci kanki ciki wata rana sai labari, tabbas nasan zaki maraici, amma kimika ma Allah lamuranki kinjiko, "kuka dijah keyi tace in shaa Allah baba zakatashi, sauna rigaka mutuwa, girgiza mata kai yayi yace dijah hak'uri zakuyi Allah bai barin wani dan wani yaji dad'i," da kuwa Allah na bari dana rok'i Allah yabarmaki lubabatu....
www.phirdauceejeebo.mywapblog.com
Written by
Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment