JINSINAH 66~70

❄❄ *JINSINAH* ❄❄

*_Feedoh_* *_yanmata_* ✍🏻

*_page_* 6⃣6⃣ *_to_* 7⃣0⃣

Moh ya rud'e yarasa mizaiyi saikawai yafashe da kuka, "juyawa Umma tayi zatatafi, moh yace Umma mukaita asibiti karta rasa ranta? "Umma tace ta rasa mana saime? Dan tubabba tarasa ranta tsaki tayi tanufa sashenta, "kuka yakeyi sosai yarasa mai taimaka mashi, "maigadi ne yaxo yace yallabai asibiti zaka kaita ba kuka zaka dingayi ba, "dayake duk akan idonshi akayi komai,,,,,,

    "Dataimakon baba maigadi moh ya saka finah mota, jan motan yayi da gudu sai softie's clinic, yana shiga gate din asibitin yafara kiran nurse, "nurse ne suka fito suna tambayanshi lafiya, da hannu yake gwadaasu finah ganin halin datake ciki ne yasa suka koma da gudu suka d'auko gadon marassa lafiya, suka azata, daidai dr Safiyya na fitowa, ganin finah tayi kwance ba rai, ga jini na zuba hankalinta yatashi "juyowa tayi ta kalli moh kallon tuhuma kana tabi bayan nurse din,,,,,
                   ***

D'akin da aka nufa da finah moh zai shiga wata nurse tahanashi kuka yadingayi kamar ranshi zaifita, saikuma yadinga nemanma finah adu'ar samun sauk'i da ita da abinda ke cikinta,,,,,,

            "Awar finah ukku kana dr safiiya tafito, bakin d'akin da finah take nan ta tarda moh harsaida yabata tausayi, saboda taga damuwa a idonshi sosai, kallonshi tayi tace moh muje office inasan magana dakai,,,

           "Bayan Dr Safiyya moh yabi da sallamarshi ya shiga office d'in dr ta amsa mashi sallama, tace have a sit moh, kujera yaja yazauna, "saida tayi yan rubuce rubucenta, kana ta d'ago gilas d'inda ke fuskarta tacire kwata kwata annurin fuskanta yabace,,,

          "Dr Safiyya ta kalli moh tace haba moh shin mi yarinyar nan tamaku haka? Kakasa sama mata farin ciki? Duk da har gobe Ina Sanka, amma wlhi jinake finah kamar *jinina* baikamata ace kamar yanda yarinyar nan tamaka halarci ba amma ka kasa samamata farin ciki, kasan kuwa irin illar damuwa, toh wlhi inma baka saniba kasani damuwa nada illoli daban daban, nidama nasan matarka bazata bari finah tazauna lafiya ba,,,,

             "Moh yace wlhi doctor ba laifina baneba kekanki shaidace a irin sanda nakema finah amma mahaifiyata da Fadilah,   shhhhhh dr tace bansan naji komai saboda family issue ne baikamata najiba, amma dan Allah shawaran da zanbaka kanemama finah far in ciki a gidanka saboda yanzu finah matsayin yar uwa na d'auketa, duk da tahana muradina ya aureni tunda yaganta, "murmushi moh yayi yace dr aykema yanzu kinsamu wani tunda gashi saura month aurenki, murmushi tayi tace moh kenan aytunda na rasaka nayi bankwana da soyayya saidai kawai zanyi aure ne saboda yazama dole,,,,

     "Moh yace dr yajikin finah da kuma babynta Allah yasa baifita ba, murmushi doctor tayi tace finah tasamu sauki dan harma tasamu bacci, "kuma cikinta na nan lafiya lau, nikaina na tsorata daganin jinin dake zuba,, amma cikin ikon Allah cikin na nan, hamdalah moh yayi ya d'aga hannunshi sama yanama Allah godia gakuma hawaye na zuba idonshi,,,,

     "Takarda dr Safiyya ta mik'amashi tace in as an magungunan nan yanzu amsa yayi yace toh, godiya yama dr kana yafita, yana fita yakira amir ya gayamashi dan yasan babu Wanda zaiyi jinyar finah sai Anty Aysha,,,,,,,

         "Tunda Amir
yagayama Anty, finah na asibiti take kuka, ga tsohon ciki tare da ita "dakyar amir yasamu tayi shiru, "shiryawa sukayi suka nufi asibiti, suna zuwa suka wuce d'akin da Feenah take dayake Ana shiga, "ganin halinda finah take yak'ara rud'ar da Anty inbanda kuka ba abinda take, anty tace amir kalli yanda finah takoma 3month  kawai idan aurennan bazaiyu ba nidai yasawake mata, "amir yace haba Aysha yakike magana kamar marar ilimi shin kin isa ki kankarema finah k'addaranta ne? Girgiza kai tayi tana hawaye, yace toh k'addaranta ce haka, dan haka adua zamu dingayi mata watarana sai labari,,,
                      ***
Anty tace shikenan Allah yakawo Mata k'arshen wannan wahalan, yakawo randa itama zatayi dariya da farin ciki kamar kowa, Allah kuma yakawo mata farin ciki a rayuwanta Amir yace amin my wife,,,,,,,,


*_Dedicated_* *_to_* *_biebee_* *_isa_* ❤

IG: yar_ficika


© *_written_* *_by_*

               *_Feedoh_* *_Deedoh_*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180