DIJAH 141~145

🏵🏵DIJAH🏵🏵 Deedoh

Feedoh yanmata

1⃣4⃣1⃣~1⃣4⃣5⃣

Suna kan hanya kowa yaga chanjin da Hamzariee yayi, "saboda yasaki jikinshi, "har affy na tsokanarshi, tace su ya hamzariee duk ancikamu da surutu, "amma da bamai jin bakinka, "dariya yayi yace anji d'in yarinya sai saka ido, "daddy yace ayba sa ido baneba,  gaskia ne, "Ammi tace dan Allah ku kyaleman yaro, duk kunsamai ido, "dariya affy da daddy sukayi, "haka suka isa gida cikin nishad'i...

Hamzariee ne kwance d'aki waya yake latsawa yana ta murmushi, "Nafeeu ya kira, naf na d'auka yace hello frnd guest what, murmushi naf yayi, yace dijah ta farka ko, "dariya hamza yayi yace naf how do u knw dat? ,"dariya Nafeeu yayi yace baka k'i kirana ba kai kagayaman, "amma lokacin daka kad'eta ayni ka nema amma yanzu baka kirani ba, "dariya hamza yayi yace bagashi na nemeka ba, yace yanzu ba, "Hamzariee yace nasan wannan mummunar yarinyar tafad'a maka kuma saita Sani, "naf yace wlhi karka tab'aman mata idan ba hakaba, "duk randa ka kawo matarka sai mun rama, "hamza yace ba rana kenan, "yace aysai munsa Ammi ta nemomaka yar k'auye, " hamza yace ashe ko kamance wacece Ammi, "naf yace toh naji, yanzu yajikin patient d'inka, "hamza yace sunanta dijah malam, " murmushi naf yayi yace toh ya jikin dijah, hamza yace dasauki, "naf yace Allah yak'ara sauk'i hamza yace Amin, "sun d'an tab'a fira kana sukayi sallama.....

*****************************
Hamzariee ne yafito cikin shirin kaftani sun matuk'ar yimashi kyau, "yana fitowa sukaci karo da Ammi, "yana ganinta ya b'ata rai yace Ammi ya baki shirya ba?, "Ammi tace wlhi Hamzariee nah bak'i zanyi, kaje kawai, "tunda affy na skul bare kuje tare idan kaje kace ina gaidata, "amma bark nakawoma pepper soup katafi mata dashi, cewa yayi toh yana godia, tareda yima Ammi fake  a kunci......

Yana shiga asibiti dijah ce yagani a haraban asibiti ana koyama tafiya, itada nurse d'in dake jinyanta, "hannu ya hard'e ya dinga kallonta yana murmushi, hangoshi dijah tayi, murmushi tamashi, "k'arasowa yayi yana murmushi yace iyyeh dijah an warke kenan, toh ya jikin naki? A hankali tace da sauk'i, yace Allah yak'ara sauki, "tace Amin, juyowa yayi kan nurse yace yamai jiki tace dasauk'i, yace sannu, nagode, yace bakomai, "dijah tace nidai nagaji mutafi d'aki, murmushi nurse tayi tace aykin yi k'ok'ari mutafi d'aki, kamata tayi suka tafi d'aki, "suna isa nurse tahad'ama dijah tea karb'a Hamzariee yayi yace madam wanan is part ov Mah duty fa, murmushi nurse tayi tabashi cup, "matsawa yayi yaba dijah tea ta goce yace plz ki karb'a mana, "dakyar yasamu takesha a hankali yadinga bata harta gama, pepper soup ya zubo mata yace Ammi nah tace nakawo maki, "dijah tace nagode, bata ya dingayi harta gama, "fira suke d'anyi dode bawani sakewa tayi dashiba, "dijah tace dan Allah yama sunanka? Murmushi yayi yace dijah, dariya tayi tace plz mana, "yace toh sunana hamza, tace sunan mai dad'i yace nagode, "dijah tace ya hamza ya akai naxo nan dan Allah, "yace nina kawoki, zata k'ara magana yace ya isa hakanan, kibari harkiji sauk'i, dijah tace toh, "fira suka dingayi saida akayi magrib, "yayi mata sallama yace da yayi sallah zai wuce, "dijah bataso hakan ba, harya kula, yace dijah ko baki san natafi, dijah tace eh ya hamza, "murmushi yayi yace karki damu zandawo gobe, "d'aga kai tayi tace Allah yakaimu, yace Amin, dijah tace ina gaida Ammi da daddy da afrah, hamza yace duk kinsan sunansu amma baki san nawa ba ko? Murmushi tayi tace afrah ne tagayaman jiya, amma tace wai kai zaka gayaman naka, murmushi yayi yace toh, zangaidasu, tace nagode, "tafiya yayi shima badan ranshi yasoba saidai dole yatafi tunda magrib tayi...

www.phirdauceejeebo.mywapblog.com

IG: yar_ficika

Written by
           Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180