DIJAH 206~210
🏵🏵DIJAH🏵🏵
Feedoh yanmata✍🏻
2⃣0⃣6⃣~2⃣1⃣0⃣
Farkawan da zanyi asibiti naganki, mutane zagaye dani harda Hajia karima, sai kuka takeyi, babanki na kalla nace Alh ina jaririyata? Shiru yayi, shima sai kwalla yakeyi, nan fa Abu yakoma man sabo, saida likita yaman alluran bacci, "satina d'aya asibiti kana aka sallameni, kuma aka nemeki har anfara fidda ran za'a sake ganinki, nikuma tinda ga ranan ban k'ara lapia ba, kullum cikin ciwon zuciya, idan abun yatasoman baiman da wasa, ahaka zanganki zanganki amma ina babu labari, har aka shekara kuma tindaga ke ban k'ara haihuwa ba, "wasa wasa har aka shekara ukku babu labarinki, harnama fidda rai, saidai abinda nakasa sama raina kin mutu, dangani nake kina raye, "kullum cikin adua a nake Allah ya bayyanaki, "ranan ina zaune, saiga Alh Lawal yashigo, yana zuwa yaceman hajia karima tayi accident tana asibiti, banyi wata wata ba, muka shirya muka tafi asibiti, "ina shiga tafashe da kuka tace zainabu kiyafeman dan Allah, nice nasa aka sace d'iyar da kika Haifa, nace akasheta, kuma ninamaki asirin da karki sake haihuwa yanzu haka gashi wajen Neman asiri nayi narasa hannu d'aya dan Allah kiyafeman, kuka na dingayi nace wlhi bazan iya yafemaki ba, yanzu kinkasheman d'iya, shine zakice na yafemaki, karima tace d'iyarki bata mutu ba, saboda wanda nasa suka saceta sunce man basu kasheta ba, amma sunkaita wani k'auye, kuka nafashe dashi nace yasunan k'auyen amma ina batada bakin magana saboda inbanda fizge fizge ba abinda takeyi, saida aka rufe d'akin datake, kafin kace mi halitarta ta canja daga baya kuma ta mutu, numfasawa zainabu tayi ta kalli dijah, tace toh kinji yanda muka rabu, kuma daga nan nakasa dangana dan gani nake kina raye, tunda karima taceman, dan haka kullum cikin adua muke sai yau Allah yahad'amu, "parlor babu wanda bai zubda kwallaba, daddy yace gaskia dijah kinga rayuwan dunia amma gashi hak'uri yanzu yazamar maki alakiri, itadai dijah kuka takeyi, tace mama ina neman Alfarma wajenki dan Allah kiyafema abokiyar zamanki, aygashi Allah yabayyanani, "kuma babana da mamana kafin su rasu sun koyaman da duk abinda mutum yaman na koyi hak'uri da yafiya, saboda Allah nasan masu yafiya , narok'e ku ya mahaifana da kuyafe masu, "daddy yace maganan dijah gaskia ne Alh yakamata kuyafemata saboda kotasamu sauk'i wajen Allah Alh Lawal yace hakane, nayafe mata, Hajia zanabu ma tace haka, tare da nema mata rahamar ubangiji,
*****************************
Rungume dijah Hajia zainabu tayi, tace nagodema Allah dayakaiki hannu nagari, suka baki tarbiyan dakomu mahaifanki iyakar wadda zamu baki kenan ubangiji Allah yajik'ansu da Rahma, dijah tace Amin mama, "Hajia takalli dijah tace yanzu ajinki mawa? Dijah tace ay final year nake exams ma nakeyi, tace eyyeh toh Allah yabada sa'a, Ammi tace Amin, "Alh Lawal yace Hajia d'ankifa kesan ta tace waye alh Lawal yace gashinan yanuna hamza, sunkuyar dakai hamza yayi, dariya tayi tace toh Alhamdulillah ay abu yayi kyau, datagama exams sai ayi biki, tayi karatu d'akinta, " Ammi tace bamai ma d'iyata aure saita fara karatu, hamza yace plz Amminah kibari ayi auren wlhi zatayi d'akina, dak'uwa Ammi tamai tace bakada kunya niba surukarka baceba, affy tace ay sirikin zamani gareki Ammi, hamza ya gallamata harara, dariya akayi, "Hajia zainabu tace ataimaka mana Ammi tayi karatun d'akinta, daddy yace sai munyi shawara, "Alh Lawal yace shikenan kunma d'iyarku yarona barmasu d'iyarsu kanemo ko yar waye Zan aura maka kaji, dariya Ammi tayi tace dayafima,
Daddy yace ba'ayi hakaba idan sundaidaita Kansu ayshikenan, hamza yace Allah mundaidaita, "daddy yace toh idan yan gidansu Nafeeu sunturo sai asaka rana gaba d'aya alh Lawal yace haka za'ayi, "sunsha fira kana su daddy suka tashi zasu tafi, Hajia zainabu tace Ammi ki araman d'iyarki saboda inasan taga danginta, murmushi Ammi tayi tace bakomai, shiko Hamzariee baiso ba, haka kawai yahak'ura, affy ko sai dariya takemai, har wajen mota suka rakosu ita kanta dijah taji daban amma ba yanda zatayi, dole tazauna da iyayenta........
www.phirdauceejeebo.mywapblog.com
IG: yar_ficika
Written by
Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment