DIJAH 111~115
🏵🏵DIJAH🏵🏵
Feedoh yanmata
1⃣1⃣1⃣~1⃣1⃣5⃣
Kodasu hamza suka isa airport d'in abuja Ambulance d'in hospital taxo d'aukarsu, angama komai akasaka dijah a ambulance sai DIF hospital, "saida akagama na dijah komai kana yawuce gida, saboda hospital d'in basu san d'an jinya komai sunadashi kawai kud'i zaka biya shiyasa baisha wahalar neman wanda zai zauna da ita ba, " yana fita asibitin drop ya d'auka yace yakaishi maitama, " gaban wani black gate naga yanunama driver ya tsaya, tsayawa yayi, fitowa hamza yayi yaba mai drop kud'inshi yaja trolling d'inshi yanufa gate, "daga bakin gate naga ma aikatan sunata mai sannu da zuwa murmushi yayi ya amsa "haka ya dinga cin Karo da ma'aikatan gida, suna gaisheshi cikin ladabi, " k'ofar parlour ya nufa da fara'nshi yana sallama, wata dattijuwa ce fara ta amsa mashi da fara'anta tace oyoyo my baby kaidawa kazo banji horn d'in motanka ba, k'arasowa yayi cikin parlourn yasamu wuri kusa da dattijuwar nan ya zauna, yace wash Ammi nagaji, "murmushi Ammi tayi tace raggo dakai, "ina tambayarka bakaban amsa ba, yamitse fuska hamza yayi yace itz a long story Ammi kedai bari nayi wanka naci abinci kana, Ammi tace toh shikenan, "wata yar budurwan yarinya ce ta rugo da gudu tana oyoyo cwt bruh tafad'a kanshi, murmushi hamza yayi yace wai ni karki karyani turo baki tayi tace bruh duka guda nawa nake? "Murmushi hamza yayi yace Allah Ammi yarinyar nan ta girma, kodai nace naf yafito ne kawai, yafad'a maganan yana kallon Afrah, "turo baki Afrah tayi tace Allah bruh kadaina dukafa ss2 nake "murmushi hamza yayi yace basai ki ida skul d'in d'akinshi ba, "tashi tayi tana bubbuga k'afa irin na shagwab'abbun nan tace Allah saina fad'ama daddy abinda kukeman kaida Ammin, "dariya Ammi da hamza sukayi, Ammi tace kajiman d'iya ni nasaka bakinane cikin maganarku, "tafiya tayi tana kuka hamza yace haba little Angel zonan mana ko juyowa batayi ba, tashi yayi yana dariya yace Ammi bari nayi wanka.......
**************************
Hamza ne ya fito parlour cikin k'anan kaya, sunyi matuk'ar mashi kyau, "daining area ya wuce, abinci ya zuba yaci saida yagama cin abinci kana yadawo parlour inda Ammi take zaune, zama yayi kusa da Ammi waya ya d'auka afrah ce ya kira saida ta kusa tsinkewa kana ta d'auka, tana d'auka yace little Angel sakko magana zamuyi kinji, toh afrah tace kana ya kashe way an, " Afrah na saukowa tasamisu hamza parlour wuri tasamu kusa dashi ta zauna, "hamza ne yafara magana, "yace Ammi dan Allah kiyafeman sakamakon k'in fad'a maki gaskia danayi jiya, bayanda zanyi ne hakan danayi shine dole "jiki sanyaye Ammi tace hamza miyafaru, "hamza ya kwashe Abinda yafaru tundaga kan accident d'in dayayi har neman iyayen dijah hartahowa da ita ya fad'a masu, "salati Ammi tayi itako afrah dayake saurin kuka gareta kuka kawai takeyi tana tausayawa dijah, "Ammi tace wlhi Hamzariee naji a jikina ba lapia ba kawai dai nabarshi yanda kagayaman ,"amma badan na yardaba, numfasawa Ammi tayi tace yanxu kana ganin tahowa da ita yayi? "Hamza yace anawa tunanin ke nan Ammi saboda bansamu wanda yadanta ba ita kuma gashi ta shiga commer, bare tafad'amana inda iyayenta suke, "amma nabarma Nafeeu komai idan anga iyayenta sai suzo saboda nidai bansan ranan komawana katsina ba, "Ammi tace hakane itakuma Allah yabata lapia yatashi kafad'unta hamza yace Amin, "Ammi tace yanzu tana wane asibiti hamza yace DIFF nakaita, Ammi tace yayi anjima sai muje naganta, inkuma munyi waya da daddynku saina mashi bayani, "hamza yace shikenan Ammi......
www.phirdauceejeebo.myeapblog.com
Written by
Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment