DIJAH 166~170
🏵🏵DIJAH🏵🏵
Feedoh yanmata✍🏻
1⃣6⃣6⃣~1⃣7⃣0⃣
Jin dad'i da walwala sun baibaye dijah alokacin data fidda ran samu, kullum saita godema Allah daya kawo mata chanjin rayuwa, yanzu burinta shine bai wuce taga iyayenta ba,
"Dijah ce toilet d'in Ammi tana wanke mata, Ammi ta shigo, tace wai dijah bana hanaki ba, akwaifa masu aiki kuma kinsani, "dijah ta duk'a tace Ammi dan Allah karki hanani samun ladanki, kenake gani matsayin uwa, dole namaki biyayya, "saboda ina kwadayin samun Ladan iyaye, jikin Ammi yayi sanyi, kamo dijah tayi tarungume tace shikenan, dijatu na yarda kuma Allah yamaki albarka, dijah tace Amin Ammi ngode, Affy ce tafad'o d'akin tana nifa dijah kin shanyani, tun yaushe nake jiranki parlor shine dan wulak'anci kikayi zamanki, kuma kinsan yanda saloon d'innan take, "Ammi tace toh suda abin magana, aiki takema mamanta, kozata fasane? Dan kina jiranta, affy tace waceni Allah yabada hak'uri, Ammi tace amin, "gwalo dijah tayima affy, affy tace haba kinfito yarinya......
*****************************
Hamzariee ne ya shigo parlor yaji shiru bakowa, zaiyi hanyar sama kenan ya had'u da affy, yace angel Ammi na fa? Tace tafita, yace dijatuna kumafa? Tace tana kitchen, "hanyar kichn d'in yanufa, yana zuwa yaga tana wanke plate, tsayawa yayi yana kallonta, "tahowa yayi a hankali, yarufe mata ido, hannun tashafa, cankuma taji k'amshin turarenshi cikin dariya tace ya hamza naganeka, dariya yayi ya bud'e mata ido tare da zagayo da ita , sun a kallon juna, "k'ura mata ido yayi, yana kallonta, gakuma wani feelings dake d'ibarshi, itakuma duk jitayi duk ta takura, saboda bata sababa, "k'arfin hali tayi tace ya hamza minene, firgigit yayi yadawo hayyacinshi tare da murmushi yace bakomai, "hannunta yaja, sukatafi parlor, suka zauna affy tafito, tace sis daddy yace yana gaidaki, tace ina amsawa, "hamza yace dijah magana nakeso nayi dake, dijah tace toh, hamza yace affy kema zoki zauna, affy zama tayi kusa da dijah, hamza yace dama bawani abu baneba illah naga ya dace daki cigaba da karatu, djah tunda labarin dakika bamu yanuna cewa kingama primary, shine nayi shawara, nida affy, affy tace gaskia ne, amma sai munji daga bakinki, hawaye dijah tafari, tace ya hamza affy banda bakin saka maku sai adua, kungama man komai, gashi burin mamana zai cika, zanyi karatu, nagode maku, hamza yace bakomai, yanzu zan samomaki mai lesson daganan saiki shiga skul, hawaye kawai dijah keyi, hamza ne yataso yadawo gabanta, tare da rik'e hannuta, yace dijah kidaina kuka, duk abinda namaki bakomai baneba, illah amanarki da Allah yabani, dole nacigaba da baki farin ciki, affy tace hakane gaskia, "itadai dijah takasa magana kukan dad'i kawai takeyi, "rungumota hamza yayi yana lallashi, wani irin Abu taji ya ratsata, kamar karta tashi daga k'irjinshi, saida tayi shiru kana yasaketa.....
Daddy ne ya shigo d'aki Ammi yace ina yayanki? Alh Lawal ne yazo ganin dijah, "Ammi tace wlhi yanzu suka fita suda yayansu, saboda affy tamatsa mashi saisuje shan ice cream, daddy yace ai shikenan, "komawa yayi yacema Alh Lawal sunfita, Alh yace wannan sab'ani da muke samu, shikenna watarana naganta, "Alh Lawal baidad'e datafiya ba su dijah suka dawo, suna zama Ammi tace Hamzariee d'azu Alh Lawal yazo ganin dijah bakunan, Hamzariee yace Allah sarki, ba rabon sugaisa, Ammi tace ayduk rikicin wannan yarinyar ne, tanuna affy, zumb'ure baki affy tayi, tayi hangar d'akinta dariya dijah tayi, tace Ammi kintab'o yaegidan daddy, Ammi tace yau ay sharrin daza'aman bayada iyaka, dukansu sukayi dariya, Ammi tanufi d'akinta, "dijah tasamu bisa kujera tazauna, Hamzariee yazo kusa da ita yazauna, yace dijatunah kinsan me? Tace ah ah, yace wlhi idan ina kallonki wani niahad'i nakeji, dariya dijah tayi tace aynima haka, duka sukayi dariya, "Niko feedoh takaici yakamani, wai duk abinnan hamza yakasa gane san dijayake😡, "hamza yace dijah gobe fa zaki Fara lesson, Myrna tafarayi, tare da k'ank'ame hannun hamza tace nagode yayana, kagaman komai na rayuwa, bintayayi da ido yana kallo, "hura mashi iska tayi, ajiyar zuciya yayi, tare da dariya.....
www.phirdauceejeebo.mywapblog.com
IG: yar_ficika
Written by
Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment