HUDAH 96~100
⭐⭐HUDAH⭐⭐
Na
Feedoh & Meesha Lurv
9⃣6⃣~1⃣0⃣0⃣
Hudah na shiga gida taci karo da maaah tafito bandaki, fadawa tayi jikin maaah maaah tana murmushi, maaah ta dagota tace lallai Auta, naufal yaciri tuta, Allah na godema daka kawoma diyata farin ciki, Allah ka dawwamar mata da wannan farin cikin, "maaah ta kalli hudah tace yakukayi dashi, hudah tace maaah nabashi labarin komi akaina kum yace yaji yagani, yacema zaidawo gobe," maaah tace Allah shikawoshi lpia, abinda nakeso nagayamaki hudah shine,kirike gaskia a rayuwanki, kuma kikama mutuncin kanki, kada kisaki kiyi wasa da mutuncinki akaro na biyu kodamacan ba laifinki baneba kaddararkice haka, "hudah ta girgiza kai tace in shaa Allah maaah, nagodema Allah dayabanke a matsayin mahaifiya, murmushi maaah tayi tare da shafakan huda, haka dai suka dinga fira, maaah najin wani nishadi a rayuwanta kamar anbiyamata makka, Allah kenan mai juya lamarinshi a duk sanda yaso, Allah yasa mudace..
****************
Shiko bangaren naufal yana tafiya yana murmushi, saikace wanda akama albishir anbashi sadiya Marafa lolzzzzz, haka ya isa gida cike da nishadi, gaban wani gate naga ya tsaya ya danna horn mai gadi ya wangale gate, cinna kan motarshi yayi cikin gida, parking space naga ya nufa yayi parking, fitowa yayi yana wasa da makkulan hannunshi, har ya isa parlour sallama yayi, wasu dattijai ne suka amsa suna murmushi yasamu wuri ya zauna yace sannunku da gida papa,wata naga ta harareshi, a shagabe yace mammy minayi dan Allah, papa kana ganin mammy ko? Mammy tace ba dole na harareka ba tun safe daka fita sai yanzu kabarmu munata mssn enka, tasowa yayi yazo kusa da ita ya zauna ya daura kanshi akan cinyarta, yace Allah sarki mammy wlhi nima nayi mssn enku, mammy tace toh ina kaje? Kai ya sosa, papa yayi dariya yace mammy ni nagane inda yaje, suruka akamana ko? Daga kanshi yayi alamar eh" murmushi mammy tayi tace tau Alhamdulillah abin nema yasamu kam, yasunan surukar tamu,naufal yace HUDAH sunanta mammy, murmushi papa yayi yace toh Allah ya nuna muna, Amin naufal yace yatashi yayi dakinshi da gudu yana dariya, girgiza kai mammy tayi tace yaran zamani,papa yace aykam, Allah dai ya nuna muna, "kiranshi papayayi awaya yace yazo, fitowa yayi yazo yazauna yace papa gani, papa yace naufal yaushe zaka koma aiki me wai? Nadauka wanan satin zaka koma,cikin muryan shagwaba yace gaskia ni papa ba yanzu ba? Mammy tace toh sai yaushe my boy, yace sai upper week, mammy tace ah ah kace dai saikagama kafuwa wajen hudah, dariya yayi yace datz y I lurv u mammy, mammy tace Lurv u mre my boy, "nidai feedoh sakin baki nayi ina kallan soyayya sai suka burgeni, gaskia haka zandinga yimasu nashwa lolzzz" haka suka dinga fira har lokacin bacci yayi, naufal ne yafaramasu saida safe, suka amsa mai cikin so da kauna
Tunda tayi sallar asuba bata koma ba, sai fara'a takeyi tagama gyara gida tsaf tahada masu karin safe, zubo masu tayi itada maaah sunaci suna fira, maaah nakara godema Allah dayakawo ma diyarta naufal lokacin datake bukatar maitaimako, haka suka karasa cin abinci cikin, "wanka hudah tatashi ta shiga,bayan tafito tatsaya gaban madubi saboda kawai tanasan tama naufal kwalliya nikaina saida abin yaban mamaki, dan iya sanina da hudah data fito wanka mai da turare kawai take shafawa, gaskia da alama hudah takamu, wata red super naga ta dauko tasaka, daddy ne yamasu ita da faddy,bata taba sakawaba sai yau, daurin dan kwali tabuga nikaina saida nasaki baki ina kallonta, nace oh ni feedoh dama haka hudah ke da kyau, gaskia kwalliya na fitarda mace, dan Allah mata mudage da kwalliya, "fitowa tayi waje wajen tasami maaah zaune, tace maaah nayi kyau? Murmushi maaah tayi tace eh lallai ko ba'a gayaman ba naufal yasamu waje, turo baki hudah tayi tace maaah nifa kenamawa, dariya maaah tayi tace karyakikeyi, saurayinki dai kikamawa, amma naji dadi da Allah yakawo maki farin ciki, bazan gaji dai dagayamaki ba ki tsare mutuncin kanki kinji ko Auta na? "Gyada kai tayi tace in shaa Allah maaah.
Fitowa yayi cikin shirinshi yasha wata gizna nikaina sai dana lora🙈 ,naji dama sadiya Marafa yace yanaso, takowa yayi yakaraso dining area, nan yasamu su mammy,yagaidasu tare dayima kowa fake a kunci, mammy tace yau kuma sai ina tunda katashi da wuri nasan da inda zaka, sosa kai yayi yace gidansu matata zani mammy, rike baki tayi tace aww tamazama matarka, papa kanajinshi fa, dariya papa yayi yace aygaskia yagaya maki kincika saka ido dayawa, naufal yace tell her dai papa, aradu saisuka burgeni, haka suka karasa break fast cikin so da kaunar juna, mikewa yayi yace papa mammy natafi saina dawo, mammmy tace Allah yasa su koroka, papa yace baiji bakinka ba, tafi my boy kaji, huda takace in shaa Allah, naufal yace at papa ina ganin aure Zan nemomaka, saboda mammy tafara Shiga gonata, hade rai mammy tayi tatashi tace zakadawo kasameni, tayi cikin daki, dariya papa yadingayi yace naufal kajamani aiki yanzu jeka saikadawo, dariya ya dingayi yasaka kai yafita.
Gaban continental yayi parking, shiga yayi wayana ga yazaba IPhone6s naga yadauka rose gold gaskia wayan tayi, kudi ya biya kana yafito, wani supermarket naga ya tsaya, siyayya yayi kamar baisan zafin kudi ba,saida yagama kana ya dauki hanyar gidansu hudah, yana tafiya yanajin nishadi a rayuwanshi, kofan gidansu hudah yayi parking yasami wani yaro yace shiga kace naufal na kiran hudah, juyawa yaron yayi yashiga gidansu hudah tare da sallama, yace hudah wai naufal na Kira, hudah tace jekace ganinan zuwa, tashi tayi ta dauko gyalenta, ta duka tace maaah zanfita, maaah tace yau kushigo gida kinji, dan naufal yazama dangida, tau hudah tace kana tasa kai tafita, idonshi kur na nan kan kofar gidansu, tana fitowa ya bude murfin mota yafito, sakin baki yayi sororo yana kallonta ko kyaftawa bayayi, turo baki tayi tace kai ya naufal wannan kallon fa, yace princess kyau nagani, nagodema Allah dayasa bansaka sanyaba dana rasa mai kyau, dariya tayi tace ina wuni, yace lapia lau ya komai? Hudah tace komai fyn, naufal yace da alama baki mssn enaba, dariya tayi tace nidai mutafi cikin gida,saboda maaah tace na shigo da kai, yace toh bari na kulle mota kwaso kayan daya siya yayi itadai binshi tayi da kallo, sallama sukayi maaah ta amsa suka shigo, "dukawa yayi har kasa yagaida maaah, amsa mashi tayi cikin kulawa, nasiha ta masu kana ta bisu da fatan alkairi...
*********************
Lemu takawo mashi ta tsiyaya mashi a cup ta mika yaki karba, tace miyasa, yace saidai kiban marerecewa tayi tace plz ya naufal ka karba na maka alkawarin next time zanbaka, dariya yayi ya karba ya sha, kana yace sakaman wannan wayan chargy amsa tayi ta dinga duba wayan dan gaskia ta mata kyau, chargy tasaka tadawo tazauna tace ya naufal baka fadaman waye kaiba, murmushi yayi yace yanzu kuwa zangaya maki...
Yace kamar yadda kikasani ni sunana naufal, mahaifina Alh abdulsalam ma aikacin gwamnatine, amma yanzu yayi retired , mahaifiyata ita kadaice wajen mahaifina Hajia nafisa mu biyu ne wajen iyayenmu zulaihat ce babba saini, muna zaune a barhim yazawa road, "maihaifinmu papa muke ce mashi sai mahaifiyarmu muna ce mata mammy, zulaihat na aure abuja tanada yara guda ukku Aisha itace babba sai maryam sannan Al ameen, "nayi degree dina da masters ena a Cairo, yanzu haka ina aiki a Kaduna, kuma banda aure amma yanxu nasamu mata, dariya tayi tace lallai kam.
Haka suka dinga fira suna musayar kalmomin soyayya bandauka hudah ta iya soyayya hakaba, naufal yace princess daukoman wayar nan,tashi tayi ta dauko waya tabashi layi yasaka latse latse taga yanayi, saikuma taga wayarshi tayi kara,miko mata yayi yace princess ga wayarki number na na ciki amma ban yarda naga number wani namiji ba inba dan uwanki ba, murmushi tayi, tace ur wish is my command bae, dariya yayi ya miko mata yace ni zan wuce sai munyi waya, tashi tayi suka fito sallama yayima maaah kana yafito rakoshi tayi har bakin mota nan ma saida suka bata lokaci,kamar karsu rabu, tsaye take tana dagamai hannu harsaida taga ya bace, kana ta juya tayi gida.....
www.phirdauceejeebo.mywapblog.com
Written by
Firdausi Abdul'Azeez (Feedoh) &
Ayeesha Musa (Meesha Lurv).
Comments
Post a Comment