DIJAH 96~100

🏵🏵DIJAH🏵🏵

Feedoh yanmata

9⃣6⃣~1⃣0⃣0⃣

Dijah na fitowa jiri ya d'ebeta ta fad'i daidai hanne na shigowa gidan, sakin kwanon hanne tayi tataho kan dijah da sauri," hanne tace dijah lapia mike damunki miyafaru dake miya fiddoki, gaba d'aya ta jeroma dijah tambayoyi, "kamar daga sama taji ance uwarki akmata, juyawar da zatayi taga inna larai, sai huci take, kamar yan dandali sub'atama ILubiee rai lolzzz, murgud'a baki hanne tayi, tace yo inna aybadake nakeba, larai tace rashin kunya zakiman? "Hanne tace idan takama aymaki aysai amaki, tunda baki rik'e girmanki ba, sakin baki inna larai tayi galala tana kallon hanne, tace hanne dama bakida kunya, hanne tajuya ido kamar sadiya Marafa tace yau kika Sani kenan, "larai tace fita tunda ba gidan ubanki baneba, "tsaye hanne tayi tana girgixa k'ugu, "dijah ce tad'ago a hankali tace hanne kiyi hak'uri kitafi gida, "inna tace kamarma tayi dan uwarta kekuma ki mik'e munahuka kiman aikina kije ki d'eboman ruwa, girgiza kai hanne tayi tafita ta hawaye, "tashi dijah tayi dakyar ta d'auka tsintsiya tana shara tana nishi a haka tasamu tagama sharan, wanke wanke tafara jikinta sai karkawa yakeyi, tanayi inna na tsine mata, haka dai tasamu tagama gyaran gidannan, inna ta d'auko wankinta tace shegiya maza d'auki bokiti ki d'ebo ruwa kiman wanki, aydama amfaninki kenan, "ba dijah ba koni feedoh saidana zibda kwalla, inamai Allah wadaran halin inna larai, "bokiti dijah ta d'auka ta nufi hanyar waje, innace takwala mata Kira, tace gantalalla salan ki dad'e  kuma wlhi jikinki yagaya maki......

Juyawa dijah tayi ta fita, tana fitataci karo da hanne, "rugowa hanne tayi ta ringume dijah, hanne kuka dijah kuka, "dak'ayar dijah ke numfashi, tace hanne kiyafeman amma yau zanbar gidan inna wanan fitar danayo, in shaa Allah nabar gidanta kenan, hanne tace nagoyi bayanki dijah, amma idan kintafi ina zaki?, "dijah tace hanne na Allah basu k'arewa in shaa Allah bazan tagayyara ba, hanne ta amince da shawarar dijah, kaji yarinta instead ov tabata shawara tahak'ura ta zauna, "hanne tace dijah ina zuwa Bari nashiga gida, tajuya kenan dijah ta rik'o hanunta, dijah tace hanne dan Allah karki gayama kowa harsaina bar garinan, murmushi hanne tayi tace karki damu yar uwata, kedai ina zuwa, juyawa hanne tayi tashiga gida, "tana fitowa takama hanun dijah, tace muje na saki hanya, murmushi dijah tayi tace toh yar uwa, haka suka dinga tafiya bamaicema wani k'ala, harsuka iso inda zasu rabu, "hanne ce ta juyo ta kalli dijah ga hawaye cike da I donta, tace dijah nan zanbarki sai ince sai Allah yak'ara had'a fuskokinmu da alkairi, dan Allah dijah duk halin dazaki tsinci kanki karki rabu da mutuncinki, "kuka dijah keyi sosai, cikin sheshek'ar kuka tace in shaa Allahu hanne zanyi koyi da maganarki, bazan wulak'antar da mutunci naba kodan mama da baba, kuka yaci k'arfinta suka rungume juna suna kuka, "hanne ce ta d'ago tace dijah garaki tafi kar wani yaganmu, ki amsa wanan kinyi guzuri ba yawa dubu biyu ce, karb'a dijah tayi tana godia, tace hanne banda bakin da zansakamaki saidai Allah shi biyaku dagindan Aljanna, Amin hanne tace , tauh dijah sai watarana , juyawa dijah tayi tana tafiya, hanne na nan tsaye tana d'aga mata hannu harta daina ganin dijah, "kwallan dasuke mak'ale da ita suka gangaro ta juya tayi gida....

Dijah tafiya take batasan ina ta dosa ba, ga jikinta yayi mugun zafi, ga yunwa tanaji, "gaba d'aya hankalinta baitare da ita, dakyar takawo kanta titi batamasan ta iso titi ba, "titi tahau gadan gadan daidai wata mota tashararo a guje horn akeyi amma batasaniba motar nan tayi tayi yanda zata kauce amma ina, d'aga dijah motar nan tayi sama, tafad'o, "wani kyakkyawan saurayine yafito cikin motan yanufa inda dijah take kwance jini yagani yana binta, jinayi yace badai ta mutu ba nashiga ukku duk ya rud'e, agaji yafara nema, tuni mutane suka cika wurin wasu sukace malam asibiti yakamata kujefa, "duk ya rud'e yace kukaman ita nasaka a mota, mutane suka kamai aka saka dijah a mota, jan motar yayi da gudu, nidai saifatan Allah yakaishi asibiti lapia nayi, "kuma Allah yasa dijah bata mutu ba....

www.phirdauceejeebo.mywapblog.com

Written by
           Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180