JINSINAH 171~175

❄❄ *JINSINAH*❄❄

*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻

*_page_* 1⃣7⃣1⃣ *_to_*1⃣7⃣5⃣

Fita Umma tayi da gudu tana Neman mai taimakonta babu kowa, sai maigadi, Umma tace kataimakeni kazo mukai na Allah asibiti, maigadi yace Hajia ban iya mota ba, "komawa tayi cikin gida ta duk'a gaban moh tana kuka, tace dan Allah karka tafi kabarni katashi, banda kowa saikai, na cuci kaina Allah kayafeman, fad'awa tayi kanshi tana kuka mai tsuma jiki, kamar daga sama taji ance Umma myafaru, d'agowa tayi cikin rinannen idonta ta kalli shi, cikin kuka tace amir Moh ba rai, amir yace what, "sungumanshi yayi yasaka mota, bai tsaya ko inaba sai alheri clinic, nurse suka fito da keken d'aukan marassa lafiya aka gungura moh ciki, ga jini yana bin bakinshi, Allah sarki Moh Allah yabaka lafiya, "doctors ukku ne kan Moh da kyar suka samu suka daidaitashi, kuma bugun zuciyanshi ya dawo normal, k'arin ruwa aka d'aura mashi, " *doctor* *yar ficika* ce ta fito tacema amir ka biyoni office, toh yace juyawa yayi yacema Umma kishiga d'akin ni bari naje, "amir ne gaban  *doctor* *yar_ficika*, glass d'in fuskanta ta cire tamashi dariya, gaisawa sukayi, kallonshi tayi a tsanake tace yakake da patient d'ina Moh yace bruh d'inane, gyaran murya yayi, tace gaskia bruh d'inka yana cikin mawuyacin hali, sakamakon abinda yasama ranshi bai samuba zuciyarshi ta raunana, shiyasa yake aman jini, amma munyi iya bakin k'ok'arinmu munshawo kan matsalan, amma gaskia idan baisamu abinda yakeso ba, kuma ya cigaba da saka damuwa a ranshi toh gaskia zai rasa ranshi, "salati amir yayi cikin hawaye yace in shaa Allah ma bazai rasa ranshi ba, zaisamu abinda yakeso, d'aga kanta Dr tayi, bankwaa amir yamata yabar office d'inta,,,,,,,
               *******
"Yana fita ya kira Anty a waya yace tazo alheri clinic ta sameshi, daganan yanufa d'akin Moh, Umma ya tarda gaban gadonshi tana hawaye, sallama amir yayi, yasamu wuri ya rakub'e amir yace umma kiyi hak'uri, cikin sheshek'ar kuka tace amir na cuci kaina na cuci d'ana yanzu kalli halin da yashiga, kaicho na, san zuciya yakaini yabaro, amir yace Umma kiyi hak'uri, wayanshi tayi ringin yana d'agawa ya gayama Anty room number d'in, saigata da sallama, tana shiga taga Umma na share hawaye, gaida Umma tayi ba yabo ba fallasa amsa gaisuwan Umma tayi tare da ba Anty hak'urin abinda yafaru, Anty tace miyafaru, gadon da Moh yake kwance amir ya nuna mata, ganin halin da Moh yake saidata zubda kwalla, ta tambaya mike damunshi nanfa, amir yamasu bayanin da dr tamashi, duk sun firgita, Umma kuka takeyi tace Dan Allah kukaini na je na rok'i finah tadawo, wlh dagaske Moh zai rasa ranshi, amir yace Umma bazai rasa ranshi ba in shaa Allah finah zata dawo gidan Moh,"Anty tace ina zuwa yanzu zandawo,,,,,

  
          "Koda anty tafito bata tsaya ko inaba sai gidansu finah, shiga tayi bako sallama, su mummy tagani parlor gaidasu tayi ta nufa d'akin finah suma a hanzarce suka bita d'akin dan yanayinta yabasu mamaki, "tana shiga tasamu finah na kwance Anty tace nafisa tashi muje asibiti Moh na bak'atar ki hankalin finah a tashe ga hawaye tace Anty miyafaru, Anty tace kibari saimunje, duk abinnan da ake iyeyenta na nan tsaye, tasowa tayi ta duk'a gaban iyayenta tace mummy daddy dan Allah kuman izini naje nagano moh, d'agota mummy tayi tace kije kinji Allah yamaki albarka, muma zamuzo wane asibiti ne anty tace uduth, daddy yace kuje gamunan,,,,,,,,,

           "Tunda suka shiga asibiti gabanta ke fad'uwa dan batasan mike damunshi ba, suna tunkaran d'akin gabanta yacigaba da fad'uwa, salati taciga ba dayi shiga sukayi da sallama, amir ne mai k'ok'arin amsa sallaman, Umma naganinta tataso da hawaye, ta rungumeta, Umma tace d'iyata kiyafeman duk abin da namaki sharrin shaid'an ne, finah tace Umma bantab'a ruk'eki ba na yafemaki, rungumeta Umma keyi tana godia, Umma tace *NAFISAH* ki taimakeni ki dawo wajen na Allah likita tace zaya iya rasa ranshi, wani iri finah taji da Umma takirata da sunanta ba tubabba ba, finah tace in shaa Allah Umma Moh bazai mutu ba zai rayu kamar kowa,,,,,


"Finah ce gaban gadon Moh ta k'ura mashi ido tana ganinshi tausayi yabata ganin yanda yarame, zama tayi tajawo hannunshi ta rik'e, finah tace pls my moh katashi kada ka maida yaronmu maraya, wlhi bazan iya zama dawani as miji ba saikai, pls katausaya mana nida arif katashi kada kamaidamu marayu, kifa kanta tayi bisa cikinshi tana kuka sosai, k'amshin turaren da baxai iya mantawa ba ya bugi hancinshi, a hankali yafara bud'e idonshi, harya bud'esu gaba d'aya "kallonta yayi hannunshi d'aya ya d'ago yashafa kanta cikin dishashiyar murya yakira sunanta *MY FINAH*,,,,,,,


*_Dedicated_* *_to_* *_biebee_* *_isa_*

IG: yar_ficika


© *_written_* *_by_*
           *_Feedoh_* *_Deedoh_*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180