JINSINAH 161~165

❄❄ *JINSINAH*❄❄

*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻

*_page_* 1⃣6⃣1⃣ *_to_*1⃣6⃣5⃣

Dakyar malam yasamu moh yayi shiru, "shiru ya ratsa, kamar anyi mutuwa, sai sheshek'an kukan moh, malam ne yayi gyaran murya yace na Allah kayi hak'uri da k'addaranka, ba lalle baneba idan kaje wajen nafisa kasameta, moh cikin sakakkiyar murya yace miyasa bazan sameta ba, malam yace eh saboda shekara d'aya da wata shidda kenan baka san inda kanka yakeba, kaga kuwa kana iya zuwa katar da tayi aure moh yace *what* kawu shekara fa miya sameni? Rashin lafiya nayi, nan malam ya kwancema moh komi, kuka yakeyi sosai yace fadilah ta cuceni amma zataga sakayya, umma kinga halin da kuka jefani, umma mi finah tamaku, wlhi yanda take maki biyayya ko d'an da kika haifa sai haka, amma kika tsaneta dan kawai ba *JINSINAH* baceba, yanzu ga wadda kikeson halin data sakamu ni dake, kuka umma keyi tace kayi hak'auri na Allah nayi nadama, duniya taman hankali, moh ya kalli malam cikin rinannen idonshi, yace kawu zanje yau nagani idan tayi aure wlhi bazan ga laifinta ba, saboda nasan taman adalci, amma zan amso gudan d'ana, malam yace gaskia ne, "nasiha malam yamasu sosai hardai umma da duniya ta mata hankali, magungunan tsari yaba su" bankwana sukama malam suka d'auki hanyar komawa sokoto, tuk'i yake amma irin hukuncin da zaima fadilah yake tunani,,,,,,

"Bari mu waiwaya baya wajen fadilah, " fadilah ce tama habiba waya tace nifa nagaji da zaman jira kizo mutafi kawai ahad'aman asirin da zaidawo da kanshi itako umma wlhi hauka zansata, habibah tace aydama gobe sati d'aya da tafiyansu, kijirani gani nan zuwa, amma kinsan sai munkwana ko? Fadilah tace nasani kedai kitaho kawai,, Allah kada kabasu fadilah sa'a akan mugun nufinsu,,,

   "Moh suna shigowa sokoto, gida yawuce ya aje umma, kallonshi tayi tace na Allah ka yafeman, duk nina saka ka wannan halin, murmushi yayi yace karki damu mahaifiyata, kedai kiman aduan samun nasara, umma tace in shaa Allah kai dama mai nasara ne, in shaa Allah nafisa matarka ce har abada, kaje nima zaka kaini daga baya, moh yace na gode yaja mota yayi gaba,,,

" Anty ce zaune tace mijinmu yakamata muje mu had'o lefe kagafa bikin saura kwana ukku, yak'e yayi yace ai aikin kine kifad'aman nawa zai isheki na baki saiki je kasuwa kawai, kafin nty tabada amsa, saidai sukaga mutum tsaye yana kwalama finah kira, duk sun razana, Amir ne yayi k'arfin hali ya kamo moh ya zaunar dashi, moh yace amir ina finah da arif suzo mu koma wlhi umma tayi nadama, babu wanda yace mashi k'ala kallon amir yayi yace abokina kardai baka rik'eman amana ba, kardai ace kabari finah tayi aure wlhi ba laifina baneba, saikuma ya fashe da kuka, amir ne ya lallasheshi yace kayi hak'uri finah batayi aure ba, amma tana gidansu, moh yace amir ya akayi kukabari takoma *JINSINTA* karta koma ruwa, murmushi amir yayi yace ayanzu iyayen finah suma musulmai ne d'aga hannu moh yayi yama Allah godia ga hawaye, kallon amir yayi yace bari naje can, tashi yayi yatafi, tagumi amir ya buga, anty data zama hoto, tunda moh yashigo, ta kalli amir tace haba ya akayi baka gayamashi gaskia ba, toh wlhi aurennan babu fashi kozai mutu saika aureta, shidai baice mata k'ala ba,,

Moh yana zuwa gidansu finah kai yasaka ya shiga, zaune take tayi tagumi, ga hawaye na binta, ga arif zaune kusa da ita yana wasa dayake yana zuwa yamata 2dayz, kamar daga sama taji muryanshi yana kiranta, tashi tayi a firgice, tafara in ina mohhh saita fashe da kuka, shima kuka ya fashe dashi, ya duk'a har k'asa yace finah kiyi hak'uri kiyafeman kizo musake sabon zama wlhi umma tayi nadama, arif kuwa kamar yasan babanshi ne kamashi yayi yana papa, d'aukanshi moh yayi ya rungume yana kuka, finah tace moh bakin Alk'alami ya bushe yanzu saura kwana ukku a d'auraman aure a zabure moh ya kalleta, yana hawaye yace finah karkiman haka wlhi zan iya mutuwa, i cant do without you, plz kiyi hak'uri ba laifina baneba, kuka sukeyi ita dashi, finah tace kayarda k'addaranmu haka take bazan iya butulciba, tsawa ya daka mata yace kincuceni kinkuma yaudareni, amma kisani duk halin dana shiga kece silah kuma yarona yazama maraya mizaki cemashi, butulu dake, yana kaiwa nan ya aje arif yayi gaba kuka take ita da arif tana kiranshi amma ko waiwayowa baiyiba, rungume arif tayi tana kuka kamar zata fidda ranta,,,,,,, "Ahaka mumny tadawo aiki tasameta hankalin mummy yatashi tambayanta tayi lafiya, kwashe komai finah tayi ta fad'ama mummy itakanta saida mummy ta razana, lallashin finah tayi amma kamar tana k'ara watsama zuciyanta garwashi gawani son moh da yadawo mata sabo,,,,,,,

"Allah kad'ai yakawo moh gida, danni kaina *yar_ficika*dana mak'ale a taya wajen d'auko maku rahoto, saida nayi dana sanin binshi, saboda gudun da yakeyi, " baiko rufe mota ba yafad'a gida cikin hanzari, parlor umma yashiga bako sallama umma naganin yanayinshi saida gabanta yafad'i tambayanshi tayi lafiya, moh yace umma nayi asaran mace mai hankali, umma yau saura kwana ukku a d'aurama finah aure wlhi umma zaki iya rasani, kuka umma keyi tace bazan rasaka ba in shaa Allah, kuma finah zata dawo gidannan, zanje gobe in shaa Allah farin cikinka saiya dawo, girgiza kai moh keyi yana hawaye, "suna nan zaune sukaji ana sallama fita sukayi shida umma, wani sukagani hannu ya mik'ama moh suka gaisa yace dan Allah kaine muhammad mijin fadilah moh yace eh lafiya, bak'on yace dama bawani abu baneba illah,,,,,,,,

Walle hannuna ya k'age kudai biyoni gobe danjin badak'ala



*_Dedicated_* *_biebee_* *_isa_*❤

IG: yar_ficika

© *_written_* *_by_*
         *_Feedoh_* *_Deedoh_*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180