JINSINAH 166~170

❄❄ *JINSINAH*❄❄

*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻

*_page_* 1⃣6⃣6⃣ *_to_*1⃣7⃣0⃣

Sunyi accident har k'atuwan mota tabi ta kan abokiyar tafiyanta ta mutu nan take, ita kuma tana asibitu amma itama abun ba kyan gani, Moh yace Allah ya sawak'e wace asibiti aka kaisu, mutumin yace suna uduth Moh yace na code zanzo in shaa Allah, bankwana sukayi da mutumin yawuce "kallon Umma Moh yayi yace kinga yanda Allah ke abinshi ko, tun nan tafara ganin sakayya kuma na tabbata ba wata baceba ta mutu illah habiba, Umma tace hakane Allah ya kyauta gaba, yace Amin, Umma tace saimuje ko Moh yace Umma nidai bazanje ba, Umma tace ay hak'uri zakayi kaje saboda haryanzu matsayin matarka take, ka shirya kawai yanzu muje, Moh yace shikenan Umma muje d'in

*ASIBITI*
Iyayen Fadilah duk sunzo duk wanda yaga halin datake saiya tausaya Mata, mamarta da babanta sai kuka sukeyi, "sallama su Moh sukayi suka shiga d'akin finah na ganinsu ta fashe da kuka, tace Muhammad kuyafe man kaida Umma Ina zanga nafisa ta yafeman, tabbas nasan abinda namaku ne nake girba, yanzu gashi nice banda k'afa k'awa takaini ta baro, Muhammad nice namaka asiirin da ka manta da matarka da d'anka kuma na rabaka da mahaifiyarka, yanzu hakama daga Neman asiri muke mukayi accident k'atuwar mota tabi takan habiba gabana, nikuma k'afata ta cire nan take, kuyafeman, babu Wanda baiyi kuka ba banda Moh dayaji tsanar Fadilah a ranshi, "dafashi babanta yayi yace kayi hak'uri ka yafemata tabbas muma mun bada gudumuwa wajen rashin tarbiyanta, shiyasa haka duk tafaru, Moh cikin rinannen idanuwanshi yace yawuce "daddyn Fadilah yace gashi likitoci sunbada shawara a fiddata k'asar waje, gashi nikuma karayan arzik'i tazoman komai nawa yak'are yanzu haka banki ta amshe company d'ina saboda bashin datake bina, da gidana yanzu haka gidan haya muke, "Moh yace ay daddy banida abinda zanma Fadilah ishara ce tafara gani danni tuni na yanke igiyar aurenta dake kaina, "takarda ya zaro ya aje gaban gado yace gashinan na sakeki saki ukku yana kaiwa nan ya juya yatafi, Umma ko k'ala takasa cewa saboda nadamar datayi, kuka Fadilah tafashe dashi tace nacuci kaina Ina zansaka kaina, Moh karkaman haka, tuni tafara fizge fizge said a doctors suka mata alluran bacci,,,,,,,,,

     
         "Anty ce gaban amir tace plz amir karkaman haka karkace zaka janye, wlhi finah tadace dakai, "tsawa ya daka mata yace miyasa sankanki yayi yawa wai? Shin bazaki dubi farin cikinta ba, kanki kawai kikasani kinsanfa basona takeba kuma Nima basanta nakeba, amma na amince kawai, saboda farin cikinki, toh tunda mai ita yadawo basai ki hak'uraba, dalilinwa mukasanta ba dalilin moh ba, wlhi Moh baicancanci butulci wajenki ba, kumanj na janye bazan aure ta ba, saidai idan wani zakiba, yana kaiwa nan yatashi, Anty tace wlhi baiyuwa saika aureta kokuma kowa ya rasa zanga yanda za ayi takoma gidan Moh saikuma tafara kuka, "Niko *Feedoh* *yanmata* k'arfin halin Anty naban mamaki, saikace itace ta haifi finar🙄🙄🤔

"Moh ne gaban Umma yana kuka yace Umma ki taimakeni finah tadawo gidana wlhi zan iya rasa raina, kuka Umma keyi sosai, tace na Allah bazaka rasa ranka ba, in shaa Allah zatadawo, Moh yace Umma bakin alk'alami yabushe, finah aure zatayi, yak'ara fashewa da kuka, Umma tace kayi hak'uri na Allah idan da rabon tadawo zata dawo idan ba rabo, sai kayi hak'uri, kallonta yayi yace Umma wlhi daga Randa aka d'aura auren finah da wani daga ranan zanyi bankwana da duniya, Umma tace baba na Allah kadaina fad'aman irin wannan maganganun kasan banda kowa saikai, dan Allah kayi hak'uri, nina cuceka na cuci kaina, da kuma rashin ilimi yakaini ya baro, kayafeman, dukansu kuka suke sosai, Wanda nima *Yar_ficika* saida na matse kwallana😭😭, "tashi yayi zaifita yana mik'ewa yafad'i k'asa ga wani kunfa na fitowa ihu Umma ta fasa tana Neman d'auki, gakuma Moh kwance ba rai,,,,,,,,

*_Dedicated_* *_to_* *_biebee_* *_isa_*❤

IG: yar_ficika

© *_written_* *_by_*
                *_Feedoh_* *_Deedoh_*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180