JINSINAH 41~45

❄❄ *JINSINAH* ❄❄

*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻

*_page_* 4⃣1⃣ *_to_* 4⃣5⃣

Nafisah ta kalli Anty Aysha da alamomin tambaya, girgiza mata kai Anty Aysha tayi, tace mamana kiyi hak'uri duk halin dazaki tsinci kanki, ki d'auka bautan aure kikazoyi ladanki tana wajen Allah "fashewa da kuka nafisah tayi tace Anty wannan wane irin abune haka zai tunkaroni, kijifa, nibama ayyukan data zanaman ne aiki ba, tubabbar data kirani dashi, shikenan dan mutum ya musulunta sai akace dingamai gori tabbas halayen wasu ba d'aya yake dana wasu ba, na rantse da Allah danasan mahaifiyar Muhammad batasona da ban aureshi ba, takuma fashewa da sabon kuka, ita kanta Anty Aysha tasan ba'ama finah adalci ba, ace gida kamar wannan wai da icce zata dinga girki,,,,,,

       "Jawota Anty Aysha tayi jikinta tace shiyasa nace kiyi hak'uri ki dauka zaman aure kikeyi tabbas nasan ba'a maki adalci ba, amma aikin gama ya gama, kuma kidaina cewa idan dakinsan mahaifiyarshi batasanki bazaki aure shi ba, tunda Allah ya rubuta mijinki ne, "shin zaki iya canja k'addararki ne, girgixa kai finah tayi tace toh kiyi hak'uri kicigaba da addu'a kinji ko, haka dai Anty ta dinga lallashinta hartasamu sauki a ranta,,,,,
               ***

Sunan nan zaune Anty Aysha sai k'ara ba finah baki takeyi sukaji sallama Amir ne da ango suka shigo, muhammad yace Anty Ina kawayen amarya, Nty tace aydayake kwashe kwashen kawaye gareta dazaka tambayemu, kai Ina naka abokan Amir ya nuna, Amir yace ayni yanzu babankane saboda d'iya nabaka, dariya sukayi itadai finah kala bataceba, "gyaran murya Amir yayi yace toh muhammad yau dai alkawari ya cika nafisah tazama matarka, dan Allah ka rik'eta amana dan yanzu kulawarka take buk'ata kasan yanzu batada kowa saikai, kayima yarinyar nan halacci kamar yanda tamaka, idan tayi badaidai ba ka kwatanta mata cikin ruwan sanyi, dode a Dan zaman da mukayi da ita banga wata matsala tataba, amma dayake ku zama zakuyi na har abada kuma hausawa sunce zomu zauna zomu sab'a ne, dan Allah kuyi hak'uri da juna, kema nafisah hakurin danasanshi to saikin kara wani kanshi saboda yanzu bautar aure kikazoyi saikin kauda idanunki, Allah ya albarkaci auren muhammad yace Amin, kuma in shaa Allah zanyi amfani da duk shawaranka, Amir ya kalli Anty yace bakice komai ba, girgiza kai tayi tace aykagama fad'an komai, Amir yace sai mutafi ayfanan finah tace batasan haka ba, don makalkale Anty tayi dakyar aka rabasu kowannensu kuka, bankwana amir yayi yaja matarshi suka tafi,,,,,,

          "Janyota yayi jikinshi yana lallashi wayanshi ne tayi ringing yana d'agawa yaga Umma, amsa wayan yayi tare da gaisheta, banji mi akaceba, muhammad yace toh gamunan zuwa, kallon finahi yayi yace wifey d'auko mayafinki muje Umma na nemanmu, saida gaban finah yafadi, tashi tayi jiki sanyaye ta d'auko gyalenta suka nufi part din Umma,,,,
                   ***

Sallama sukayi Umma ce ta amsa tare da yimasu izinin shigowa nan suka tarda Fadilah, d'agowa tayi a yatsine ta kallesu tanakai dubanta ga finah saida gabanta yafadi danta fita komai cikin ranta tace shiyasa ya nace mayen Ashe kyau yagani, finah ta duk'a tagaida Umma amma taki karba, juyawa tayi ta gaida fadilah itama ko kallonta batayiba abin yama muhammd ciwo, finah tasamu wuri ta rabe kamar marainiya,,,,

          "Muhammad ne yagaida Umma ta amsa ba yabo ba fallasa, Umma tace kasan dalilin kiranku? Muhammad yace ah ah, tace yawwa to, dama zan k'ara shaidama waccan tubabbar ayyukanta a gidannan, dan ba hutu tazoyi ba, "shidai baice komai ba, Umma tace na sallami duk masu aikin gidannan mai gadi kawai nabari saboda gamai aiki ka auro shima maigadin abinda yasa nabarshi dan kar azageni da har bud'e gate din ita zatayishi, dakazo wucewa kaga dan filin can anzagayeshi KO? Yace "eh" Umma tace toh kitchen din matarka ne da zata dinga girki kuma da icce, da sauri yad'ago yace icce? Umma tace eh muhammad yace Umma sai azageni Umma tace ama tsine maka, nidai nagaya maka, kuma aykaga ita fadilah ba iya girki tayiba bare su raba kaga kuma idan akace za'a dingayi kan gas za'a dinga almubazzaranci tunda akwai yawa gara da iccen yafi, saikuma gyaran gida da sashena, shi sashena sau ukku zata dinga gyarashi, saikuma idan wankina yatataru saita dingayiman, "shikenan ayyukan, Fadilah ko akwai wani abu kokema ta dingayi maki wanki da gyaran d'aki yamutsa fuska tayi tace ah ah kayana nafisan nakaisu drycleaning gyaran d'aki kuma banso saboda kar aman wani asirin, "Umma tace ayshikenan, ran muhammad yab'aci itadai finah kanta na k'asa Umma tace zaku iya tafiya, tashi sukayi suka masu bankwana suka tafi, "sunkai bakin k'ofa Umma tace ke tubabba aikinki daga gobe zaifara dan bawani zaimaki abin karin kumallo ba kifito da wuri kinjini ko? Finah tace naji Umma in shaa Allah zanfito,,,,,,,,
            ***

          "Zaune yake kan kujera yabuga uban tagumi, zuwa tayi taciremai tagumin tana murmushi tace kasan fa babu kyau, numfasawa muhammad yayi yace finah dole nayi tagumi wannan wane irin bala'i ne Umma take Neman azaman gaskia bataman adalciba, "shhhhhh finah tace mashi tace haba dear mahaifiyarka ce fa kuma dantasani aiki miye nima ay mahaifiyata ce wlhi babu komai duk zan iya karkadamu kanka, jawota jikinshi yayi ya rungume kam kamar wani zai kwace mashi ita yace nagode Allah yamaki albarka tace amin, sakinta yayi yace muje muyi sallah ko yana fad'a yana kashe mata ido dariya tayi ta ruga d'aki,,,,,,

      "Alwallah sukayi sukazo sukayi raka'a biyu bayan sunyi sallama muhammad ya d'aga hannunshi ya kwararo masu addu'oin tsari, juyowa yayi yakama kanta yamata addua Lamar yanda annabinmu ya ummurci duk wani ango yayi ran daren farkonshi, tambayoyi yamata takuma bashi amsa shikanshi yayi mamaki kamar damacan tasansu, dasaida ta musulunta yahad'u da ita dasaiyace damacan musulmace,,,,,,,

Tashi yayi yaje kitchen yad'auko masu plate da cups yakawo gasassun kajine masu zafi ga yaji madadi😋😋😋 bata yadingayi saidata k'oshi kana ya kyaleta shima yaci sunagamawa takwashe kayan takai kitchen ta ajesu kana tadawo parlor, kallonta yayi yace saura mi dariya tayi tace babu, yace akwai saura wanka, kafinta bashi amsa d'aukarta yayi kamar yad'auki BIEBEE ISA bai aje ta ko inaba sai toilet towel yakawo mata, muhammad yace Bari namaki dan kingaji cikin shagwaba tace Allah zan iya dakaina, dariya yayi yajamata toilet din, "wanka tayi sosai kana tafito tana fitowa ta tarda bashinan, saidai taga kaya an ajematasu d'aga kayan baccin tayi tana dariya dan bata iyasakasu, "shafe jikinta tayi kanatabi da humra mai dad'i kafin kace mi jikinta ya d'auki wani irin k'amshi,,,,,

        "Shigowa yayi cikin kayan bacci sunmashi kyau sosai zaune yatarda ta yace yabakisaka kayanba, finah tace kunyarsasu nakeyi dariya yayi yajawota jikinshi yace bak'auya dake, wasa yafara yimata nanfa labari yasha banban tashi yayi yakashe masu wuta, "nikuma *_Deedoh_* najawo k'afafuwana nafito tareda jawo masu k'ofa sai muce Allah yakawo k'azantar d'aki *_Amin_*,,,,,,

*_Dedicated_* *_to_* *_biebee_* *_isa_* ❤

IG: yar_ficika

© *_written_* *_by_*
       
                   *_Feedoh_* *_Deedoh_*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180