ZAMAN GIDA 41~45
🤔🤔 *ZAMAN* *GIDA*🤔🤔
*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻
*_page_* 4⃣1⃣ *_to_*4⃣5⃣
Marafa tace tabbas malamin nan gaskia ya fad'a muna, duk da mun mik'ama Allah buk'atunmu, bamu dogara da bokaye ba, dabamu b'ace haka ba, kuma harda hak'k'in iyayenmu wlhi kebinmu, saboda basusan muna wannan bin malaman ba, bamuyima iyayenmu adalci ba kuma bamuyima kanmu adalciba, saboda gashi duk inda mukaje abinda za'a gaya muna daban, babu Wanda muka tab'a zuwa yamuna wa'azi kamar wanann bawan Allah, "ladies nikam na tuba daga yanzu zan mik'ama Allah alamura na idan lokacin aure na yayi zanyi, kuma zai rik'e aduan da malamin nan yabamu, nikaina Marafa ina bayanki na tuba, Rookiey Kaxs ma haka, queen tace Allah ya gafarta muna, Hady kuwa harda kuka, saboda nasihan malam ya shigesu, haka suka dawo gidansu queen jiki mace babu mai wani walwala harsu kagama abinda zasuyi suka juyo katsina,,,,,,
Tunda ga wannan ranan yanmatan nan suka daina bin malamai, inbanda ibada ba abinda sukeyi, sukansu iyayensu sunga canji, saboda basu wasa da sallan dare, kullum cikin kaima Allah kukansu suke,,,,
"Suna zaune makaranta Rookiey Kaxs takirasu tace asnsamata biki sati biyu masu zuwa sunyi murna sosai, kamar su aka samawa, "lokaci yayi akayi biki lafiya aka tashi lafiya, inda aka kai amarya kano, sunyi kukan rabuwa da juna,,,,,,,,
*BAYAN* *WATA* *HUD'U*
Tsaye suke bakin skul suna jiran abin hawa Hady tace Marafa kinga haryanzu bamu samu mini jeep ba ko zamu fara tafiya ne, kafin Marafa tayi magana wata mota ta faka gabansu, basuko kalleta ba, wasu samari ne su biyu suka fito sallama suke amsawa sukayi, samarinnan suka dinga magana amma suka kyalesu, suna nan tsaye saiga mini jeep, shiga sukayi samarinnan basu hak'ura ba suka dinga binsu, harsaida sukaga inda aka ajesu,,,, "suna shiga gida saiga yaro wai ance Ana sallama da yanmatan da suka shigo yanzu, kallon kallo suka fara, mamansu Hady tace badaku akeba, tashi sukayi suka fita, suna fita sukaci karo da mazan da suka had'u dasu d'azu, sallama suka masu, tare da gaidasu, amsawa sukayi cikin fara'a d'aya daga cikin mazan yace kuyi hak'uri yanmata kunga mun biyoku, gaskia mu ba yan nan garin baneba Kaduna muke munzo duba aikin da mahaifinmu keyi kuma sai Allah ya had'amu daku, kuma maganan gaskia mu da aure mukesanku, Hady tace malamai aybamu san sunanku ba, murmushi yayi yace ni sunana Anaz kuma nike nakeso, d'ayan yace nikuma sunana Mubaraq kuma sister d'inki nakeso, kuma mu gidanmu d'aya same fada same moda, Anaz ne 1st born saini 1yr ke tsakaninmu, sannan sister dinmu maisuna zainab, itace lst born d'inmu kuma kd muke zaune unguwar rimi, mahaifinmu d'an kwangilane munyi karatun mu a ABU zaria, inda ni nakaranta business admin, shikuma anaz public admin, wannan shine d'an tak'aitattacen tarihin mu Hady tace toh ni sunana khadija ita kuma sadiya, kuma mu frndz ne amma duk nan area muke, anaz hakan yayi, yanzu mikukace mudai da aure mukesanku sadiya tace kubamu zuwa gobe Mubaraq yace Allah yakaimu,,,,,
Akwana atashi, soyayya da shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakanin su hady da su Anaz kowa burinshi ya kyautatama d'an uwanshi, yan gidansu anax sunzo Neman izini kuma ambasu inda akasaka biki wata biyu masu zuwa, amare kuwa saiyima Allah godiya sukeyi, feedoh tayi murna sosai, sai fatan itama Allah yakawo nata lokacin,,,,,,
"Shirye shiryen biki ya kankama saboda yanzu bai wuce saura sati biyu ba, feedoh da amare hady da marafa ba zama, saboda rabon iv da sukeyi,,,, "Feedoh ce ta d'auko mai gyaran jiki inda za'ama amare gyaran jiki na tsawon sati d'aya, aykam amare sun sha gyara dan idan kagansu baka ganewa, bawata bidi'a zasuyi ba, kamu kawai zasuyi, feedoh ta d'auko mai makeup saboda amare, Masha Allah amare kam sunsha kyau kamar basuba,,,,,
*********
Rana bata k'arya saidai uwar d'iya taji kunya, yau juma'a aka d'aura auren hadiza da Anaz sadiya da Mubaraq akan sadaki naira dubu Hamsin hamsin inda dubban mutane suka shaida, Ana gama d'aurin aure aka wuce da amare Kaduna, Allah sarki amare sunsha kuka, kamar zasu fidda ransu, sunaji suna gani aka wuce dasu kd, "k'arfe bakwai da rabi amare suka isa gidajensu, Masha Allah gidaje sunyu kyau, compound d'aya ne saidai kowace da part d'inta, hady tace feedoh gidanta zata kwana itama Marafa tace gidanta feedoh zata kwana, nanfa suka fara rigima, zainab k'anwarsu Anaz tace bari naraba maku gardama, nizantafi da feedoh gidanmu ta kwana, hady tace saidai haka, haka kuwa akayi feedoh saidai tabi zainab gidansu ta kwana,,,,,,
*Dedicated* *to* *Sadiya* *Marafa* *nd* *Hadiza* *Ahmad*
*Feedoh* *Deedoh*✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment