JINSINAH 21~25

❄❄ *JINSINAH* ❄❄

*_Feedoh_ _yanmata_*✍🏻

*page*2⃣1⃣ *to*2⃣5⃣

Muhammad ya rusuna yace ayi hak'uri Umma, kamar ya k'ara zugata, Umma tace gaskia baka tab'a b'ataman rai irin wannan ba, sokake kahad'aman *_jinsi_* da arna, baba na Allah mike damunka, "muhammad yace kiyi hak'uri Umma ki gafarceni, tashi Umma tayi tabarshi nan zaune, "shima tashi yayi ya fita,,

        "Gidanshi ya wuce yana shiga parlor ya tarda fadeelah ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya, sallama yayi, tsaki tajamashi, muhammad bai tanka mataba yawuce d'akinshi, "habaici fadilah tafarayi, "yana shiga d'aki ya kulle kanshi, tunani kala kala yayi su amma yarasa mafita, yarasa ta yanda zai b'ulloma umma ta hak'ura,,,

*_BAYAN_* *_KWANA_* *_BIYU_*
Kwana biyun nan muhammad ya fita hayyacinshi, gashi duk wata hanya da dubara dazaiyi yayi amma umma kamar k'ara tunzura ta yakeyi, "gashi gani yake idan bai auri claire ba baimata adalciba, tunda gashi saboda shi tabar iyayenta, dakuma *jinsinta* amma gashi aure zai gagara tsakaninsu, "murmushi naga muhammad yayi mayb yasamu wata hanya,,

     "Bari mulek'a wajen claire muga yazamansu yake,,

        "Claire ce tsaye kitchen tana wanke wanke, Aysha ce tafito tace haba claire banace kidaina aikin nan ba, tunda akwai masuyi, koso kike muhammad yace muna baki wahala, "murmushi claire tayi tace haba Anty Aysha miye acikin yan ayyukan dana maki, wlhi ayanda kika rik'eni baki tab'a nuna tsaana ko tsangwama ba gareni wlhi zan iya maki komai, murmushi aysha tayi tace aymun zama d'aya nidake, claire tace yawwa Anty akwai abinda nakeso muyi magana kanshi, Aysha tace olryt muje parlor,,,

        "Sun zauna Aysha tace ina jinki, kafin claire tayi magana sukaji sallamar amir da muhammad, shigowa sukayi suka zauna gaidasu claire tayi cikin murmushi muhammad ya amsa yana tsokanan Claire, yace dear kinga yanda kika k'ara kyau lallai madam ta iya reno, dariya sukayi su duka, Aysha tace wai miya maidoku, yanzu gashi munasan mutattauna, Amir yace sai mukoma, claire da sauri tace *no* karku tafi dama inasan nayi maganan gabanku, "dukansu suka kalli juna, Amir yace ok toh shikenan, muna jinki,,

Gyara zama claire tayi ta kalli Aysha, "tace Anty Aysha tabbas keda mijinki yan halak ne, kunsan darajan mutane, saboda ni shaida ce, muhammad tun randa ka kawoni gidannan har yanzu, mutanen nan ko kallon banza basu tab'ayiman ba, duk abinda nakeso shisukeman, "kuma abinda na lura dashi shine basu wasa da addininsu, gashi kullum cikin yawan kyauta suke, ga wanda baidashi, "toh ganin wannan kyawawan hali nasu dakuma naka shine, nayi sha'awar shiga addininku, gaba d'ayansu sukayi kabbara, shiko muhammad fad'uwa yayi yayi sujuda ga Allah rungume claire Aysha tayi tana kuka, tad'aga kanta sama tace Allah nagodema da kashiryu wannan baiwarka akan addinin gaskia, Amir yace tabbas claire kinyi abin da yadace saidai addininmu yana da ka'idoji, claire tace bakomai xan iya, "nanfa Aysha tafara gayamata, abubuwan da Allah keso da wanda bayaso, da abinda zakayi kashiga wuta, dakuma wanda zakayi kashiga Aljanna,   "nan take kuma akaba claire kalmatun shahad takumayi, "Allahu Akbar Claire anshigo musulunci, "muhammad yace sai maganan suna, claire tace Anty Aysha saiki zab'arman Aysha tace na zab'ar maki sunan mahaifiyata *NAFISA* rungumeta claire tayi, tana godia, Aysha ko sai kwalla takeyi,,,

     
        "Amir yace aysha saiki dinga koya mata abubuwa, kafin daga baya musakata islamiya, Aysha tace haka za'ayi, "nanfa suka dinga fira cikin jin dad'i agogo amir yaduba yace lokacin sallah yayi, tashi sukayi, muhammad yace nidai daga masallaci zan wuce argugun sai gobe zan shigo, *nafisa* tace shikenan, saika dawo,,,,,,

       "Suna fitowa masallaci muhammad yace bari na wuce, Amir yace wai mizakayo argungun, muhammad yace yayan Umma zanje nasama namashi bayani, kuma yanzu kaga nak'ara samun hujja tunda gashi ta musulunta, Amir yace gaskia ne Allah dai yasa shiya amince, muhammad yace amin, ayshi babban malamine, bazaiki amincewa ba, amir yace hakane, Allah yasa adace, muhammad yace amin, har wajen mota yarakashi, bankwana sukayi muhammad yaja mota, sai argingun,,,,,,


*_Dedicated_* *_to_* *_biebee_* *_isa_* ❤

IG: yar_ficika

*_written_* *_by_*
        *_Feedoh_* *_Deedoh_*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180