DIJAH 86~90
🏵🏵DIJAH🏵🏵
Feedoh yanmata
8⃣6⃣~9⃣0⃣
Koda suka isa asibiti, dijah bata farfad'o ba wajen gadon dijah hanne taje tana kuka, tace dijah Allah yasaka maki, Allah kuma yakawo maki k'arshen wanan wahalan, "malam haruna yace hanne kidaina kuka adua zaki mata Allah yabata lapia, nibari inje gida in nemi wanda zai kwana da ita dannasan larai, bazatazoba, hanne tace malam ayni zan kwana da ita, babu Wanda yake dolen dijah yanxu saini, girgiza kai malam haruna yayi, yace toh hanne iyayenki sun sani? Hanne tace ay habu ya Shiva yagaya mana shine innarmu tace naje na tambaya gidanka wani asibiti ne, saina tafi, yanzu dai idan kaje saika gayamasu asibitin da muke dan koda zasu kawomana abin, mlam haruna yace toh hanne Allah shi sakamaki da alkairi, murmushi hanne tayi tace ay dijah yar uwatace duk abinda na mata bakomai baneba....
Bayan malam haruna yakoma gida, gidansu hanne ya wuce yamasu bayani, jimami suka kamayi, da tur da halin larai, "yan gidansu hanne da matar malam haruna asibiti suka yini amma har suka taho dijah bata farfad'o ba, "dijah ce tafarko tsakar dare tana wani ihu tana cewa Inna kiyi hak'uri wlhi bazan k'araba, hanne sallame sallah tayi tayo kan dijah da gudu tana lapia,? Ihu dijah tasaka tana fizge fizge daidai likita na shigowa, dasauri ya k'araso yana zuwa yama dijah alluran bacci cikin ikon Allah kuwa bacci ya d'auketa, hanne inbanda kuka ba abinda take, tana neman Allah yakawoma dijah k'arshen wannan wahalan.
****************************
Satin dijah biyu asibiti kana aka sallameta kuma cikin satinan biyu Inna larai ko sau d'aya batazo ba, malam haruna keta d'awainiya da dija da yan gidansu hanne, kuma hanne ke wurinta, "yau aka sallami dijah likita yak'arayima malam tuni akan lapiarta dan duk azatan likita d'iyarshi ce, shidai malam cewa yake toh dan yasan ba abinda zai canja daga azabar da dijah ke cikinta, "hanyarsu ta komawa gida malam ya tsaya yasaima dijah magunguna kana suka wuto gida, suna isowa hanne tamata bankwana, tawuce gida , "malam haruna ne yayi sallama amma larai kota amsa shiga sukayi, "gyaran murya yayi yace larai yanzu kin kyauta kenan? Ayna d'auka ko akuyarki ke asibiti kinje kiganta bare mutum amma bakijeba, "toh ga dijah nan tadawo Allah kuma yabata lapia inyaso kikasheta yau, amma kisani in shaa Allah bazaki mutu ba saikinga ishara, itako Inna larai wak'ok'i kawai take tana habaice habaice "juyowa yayi wajen dijah yace khadija ki k'ara hak'uri da rayuwa watarana sai labari dad'i baya d'orewa haka kuma wahala bata d'orewa in shaa Allah sai larai tadawo k'ark'ashinki, "kikula da shan maganinki nizan wuce idan kinada matsala kisameni, "a hankali dijah ta bud'a baki tace nagode malam Allah yak'ara Rufa asiri , Amin yace yasakai yafita.......
www.phirdauceejeebo.com
Written by
Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment