DIJAH 131~135
🏵🏵DIJAH🏵🏵
Feedoh yanmata✍🏻
1⃣3⃣1⃣~1⃣3⃣5⃣
BAYAN WATA TAKWAS
Abubuwa sunfaru cikin wata takwas d'innan, "ciki harda rashin lapiar dijah, " acikin watannin nan, hamza har umrah yaje, " yama dijah adua neman tashi, daga ciwo "dijah tana nan kwance kamar gawa, "abun yana damun yan gidansu hamza, "hardai shi kanshi, "zuwa hamza yayi yasami daddynsu, yace daddy mizai hana, "a fidda baiwar Allah nan k'asar waje ko za'a dace a can?, "girgiza kai daddy yayi, yace hamza banak'i ta takaba, "duk inda muke wake bada sauk'i? "Hamza yace Allah, "daddy yace toh danan da can duk Allah zai bata lapia, kajiko, badai har d'akin Allah kaje kamata adua ba? Hamza yace "Eh, daddy yace toh in shaa Allah , Allah yakarb'a musaurari lokaci kajiko, "hamza yace shikenan daddy in shaa Allah, nakuma gode, "daddy yace bakomai hamzarieen Ammi kaidai kacigaba da yima amanarka adua, "dan yanzu amanarka ce da Allah yabaka, 'har kafin ta tashi asan su waye mahaifanta, " hamza yace in shaa Allah....
*****************************
Hamza ne kwance bisa cinyar Ammi, Ammi tace Hamzariee na dan Allah jiyanda ka rame, kadaina cin abinci sosai yanzu, inafa kallonka ido nasamaka, amma kaibakasan amaka zuru ba?,"Allah zamu b'ata dakai, hamza yace kiyi hak'uru Ammi nah wlhi bansan ya akai nazama haka, "ciwon yariyar nan duk ya dagulaman lissafi, "nikaina ina mamakin yanda nadamu da rashin lapianta sosai haka, " Ammi tace dole kadamu mana, hamza yace toh miyasa Ammi nah? "Ammi tace saboda ta sanadiyarka tashiga halin datake ciki yanzu, "kaidai kacigaba da adua in shaa Allah everytin will be fyn kajiko my boy, " hamza yace Ammi Nah, nagode sosai, lurv u, Ammi tace Lurv u much my boy, "daidai Afrah na sakkowa daga saman bene tab'e baki tayi, tace mutum ko kunya baiji yahaye cinya, "Ammi tace ina ruwanki, inaga dai ayba taku yahau ba, dariya hamza yayi tareda yima afrah gwalo, "daddy ne ke sakkowa yana waya, "yace in shaa Allah zangayamai, itakuma Allah bata lapia, "yakuma bata dangana, "Afrah taje da gudu ta rungume daddy, daddy yace bbynah kinyi kyau, tace nagode daddynah, "hannunta yakamo suka xauna, "daddy yace Hamzariee Alh Lawal yace nabaka hak'uri yaso zuwa duba patient d'inka baisamu ba ciwon matarshi yatashi yanzu haka suna Germany, "hamza yace bakomai Allah yabata lapia Ammi yace Amin, "Ammi tace daddyn affy asibiti fa zamu, "daddy yace ay yau tare zamu nadad'e banje naga jikin amanar Hamzariee ba, "Ammi tace aykam saimu tafi to......
Suna zuwa asibiti d'akin dijah sukawuce suna shiga, "nurse d'inta na shiryata, tanaganinsu daddy nurse tafara washe baki, tana gaodasu, "suka amsa tare da tambayarta mai jiki, "nurse tace da sauk'i, "kana tafita, tana fita Hamzariee yaje gaban gadon yaja kujera yazauna tsura mata ido yayi yana kallonta, "daga k'arshe yamata aduan samun sauk'i, tashi yayi yadawo wajensu daddy yazauna, "fira sukeyi yawancin, firan kan ciwon dijah ne, "suna cikin firan sukafarajin k'ara na'urorin dake jikin dijah suka fara k'ara, duka suka mik'e daddy ne yacema hamza yai maza yaje kiran doctor, "dasauri hamza yanufa k'ofa yana bud'ewa yaci karo da doctor ashe ya gani, dasauri doctor yayi wajen gadonta hamza ya bishi,
Komi yasa na'urorin ke k'ara oho kudai biyo feedoh, "hannuna ya Rik'e yanzu gaskia, mayb zuwa anjima kujini, "Lurv u so much my beautiful people❤
www.phirdauceejeebo.mywapblog.com
IG yar_ficika
Written by
Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment