JINSINAH 26~30

❄❄ *JINSINAH* ❄❄

*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻

*page* 2⃣6⃣ *to* 3⃣0⃣

Muhammad ne gaban kawunshi yayan Umma, "kawu yace na Allah ya hanya yakabarosu umman naka da iyalanka, muhammad yace lapia kau kawu, "dama wata magana ce takawoni wajenka, gyara zama kawu yayi yace ina jinka na Allah, "muhammad yakwashe komai yafad'amashi ba abinda yarage, muhammad yace kuma kawu abin dad'in ma yanzu haka yarinyar ta musulunta, saboda taga yanda musulmai suke mu'amalarsu,,,

         "Kawuce Allahu akbar gaskia abu yayi kyau, toh inbanda mahaifiyarka na mace wayace mata bazaka iya auren wadda ba musulma ba, ay mace musulma ce ba'ayarda ko a musulunci ta auri wanda ba musulma ba, amma kai zaka iya, kuma gashima yanzu ta musulunta, kuma datake maganar ba *JINSINKA* baceba, dama ance dole sai *jinsinka* zaka aura? Ayzaka iya auren kowane *_JINSI_* Indai suna da addini, ita yanzu ba abin dad'inta baneba ace wata ta musulunta saboda d'anta, "kabarni da ita yau basai gobe ba zamuje, ni nakwana sokoton,, godia Muhammad yayi sosai, kyauta muhammad yama matar kawu kana suka d'auko hanyar sokoto,,,,,

***************************
Koda su muhammad suka iso sokoto basu tsaya ko inaaba sai hubbare, Umma na d'aki kwance tana jin labarai, taji sallamar, yayanta, tashi tayi da sauri tana amsa sallamar, "ganin yayanta da muhammad saida gabanta yafad'i, shigowa sukayi, wuri kawu yasamu ya zauna, shikuma Muhammad ya zauna k'asa, gaidashi tayi amsawa kawu yayi ba yabo ba fallasa, umma tace yaya bari akawo maka ruwa, kawu yace yanzu bana buk'atar ruwa harsaina gama abinda yakawoni,,,

          "Kawu yace haba Mariya da ina ganinki mai hankali, mai ilimi amma duk kin watsar, lallai gaskia ne, da ake cewa duk girman mace kwakwalwanta k'ara mace, "yanzu ke saiki haramta abinda Allah bai haramta ba, dan d'anki yace zai auri wadda ba musulma ba, shine zaki hanashi harkina niyar yimashi baki, Allah ya haramta auren ko kuma ku kuka haramta? Umma tace kawu nifa ba k'ara aure na hanashi ba, cewa nayi bazai auri arniya ba duk matan dake *_JINSINSHI_* amma yace ba wanda zai aura sai arniya,,,, "kawu yace naji duk matan dake *_JINSINSHI_* ba Wanda yakeso sai arniya, shin Allah yahana ya aure ta? Umma tace ah ah, kuwu yace Ku kuka hana kenan, zakuma Allah shishigi, akan abinda ya tsara, Umma tayi shiru,,,,,

        "Kuma keba abin dad'i baneba ace sanadiyar d'anki baiwar Allah nan ta musulunta, "to inbaki saniba kisani baiwar Allah nan ayau ta musulunta, saboda kyawawan halayen musulmi datake gani, dakuma gaskia irin ta d'anki, "Umma tace haba kawu tubabba ce fa, kawai tayi hakane danta aureshi, daga baya takoma ruwa, "kawu yace haba Mariya waimike damunki, ina magana kina nayi, shin dan mutum yana tubabbe shine mi? Kokuma kunfi tubabben kusa da Allah ne? Toh wallahi bari kiji, idan har tuban gaskia tayi, takuma yi abinda Allah yakeso ta kiyaye wanda baiso zata iya rigaki shiga aljanna keda kike ganin anhaifeki cikin musuluncin,,,

     "Kumani maganata ta k'arshe shine kibar yaron nan yayi aurenshi, idan kuma zaki nuna d'anki ne ban isaba shikenan gaki gashi nan,,,

         "Cikin sanyin murya Umma tace shikenan yaya na janye yaje yayi Allah ya albarkaci auren, kawu yace amin Allah kuma yashi maki albarka nagode "juyowa kawu yayi kan muhammad yace na Allah mahaifiyarka ta yarda, kuma abinda nakeso ka cigaba da yimata biyayya, sukuma matanka kayi adalci, kada kaga ita wannan dan ba *_JINSINKA_* Baceba kace zaka wulakanta ta, kayi adalci tsakaninsu, muhammad yace in shaa Allah kawu zanyi yanda kace nagode sosai Allah yak'ara girma, "Amin"

     "Idan kun daidaita kanku sai ayi maganan auren, waye zaizama waliyinta? Muhammad yace kawu abokinane Amir dama tana gidanshi, tinda iyayenta suka koreta nakaita can, kawu yace ayshikenan,,,

     "Zaka iya tafiya kabarmu muyi firan zumunci, amma gobe kazo da wuri kamaidani, Muhammad yace in shaa Allah, juyawa yayi wajen umma, "yace umma nagode Allah yajaman da ranki, dafa kanshi umma tayi tana murmushi tace amin, na Allah, "Allah yamaka albarka yanda kake farantaman yabaka 'yaya kaima masuyi maka, kawu yace Amin, "bankwana yamasu yafita yana Myrna burinshi yakusa cika, *_NAFISAH_* Takusa zama mallakinshi......


*_dedicated_* *_to_* *_biebee_* *_isa_*❤

IG: yar_ficika

*_written_* *_by_*
            *_Feedoh_* *_Deedoh_*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180