JINSINAH 56~60

❄❄ *JINSINAH* ❄❄

*_Feedoh_* *_yanmata_* ✍🏻

*_Page_* 5⃣6⃣to6⃣0⃣ *_to_**_
Bayan Wata 3
Feenah tayi Bak'ih ta yi muguwar Rama, ciki ne da ita amma ba ta sani ba ma, zaune take ta zabga Uban tagumi tana zubar da hawaye, Rayuwarta yayi kunci, ta gaji da masifar Umma da Fadila, Tijarar yai daban na gobe daban. Yanzu Shikenan haka zata k'arashe  rayuwarta? Haka zata cigaba da bautan uwar miji ba sannu bare nagode? Tana cikin tunani taji an banko k'ofa, a firgice ta dago don a zaton ta Umma ce, Amma idonta sai ya gane mata wata ba Umma ba, Fadila ce tsaye hannunta bisa k'ugunta, kee tubabba, feena ta runtse idonta ta tsani sunan nanda sauri tace donAllah ki daina kira na da tubabba, ki kirani da Nafisa, Iyeeeeeeeh Fadila ta tafa hannayenta, ayiriri, ai ba ki da wani sunan da ya wuce Tubabba, tunda har ba a chanza ma tuwo suna kema tubabba za a dinga kiranki. Feena tayi shiru ta koma ta zauna,  ba ta so hakan ba, taso feena ta biye mata suyi fada, feena ta ba banza ajiyar fadila, abun da ya qara harzuqa fadila kenan ta cigaba da zaginta ta uwa ta uba, mayun banza, tubabba sai da aka gama tanbadewa a titi kafin aka aure min miji, karuwa kawai, Feena hawaye kawai ke kwaranyowa da ga idaniyarta, kalaman Fadila ya mata zafi, Allah ya wadaran naka ya lallace, Allah kadai ya san ko gadon karuwanci kikayi wurin Uwa, feene ba zata iya jin batanci ga iyayenta ba, zuciya ta cita ta nufo Fadila, tace ki dai na sa iyayena cikin abubuwanki, naji su ba musulmai bane, amma su mutanen Arziki ne, ba mu gaji karuwanci ba ba kuma mugaji jahilci ba, fadila ta kamtseta da marih tace ni kika kira jahila? Feena ta durqushe tana kuka, aikuwa fadila ta shiga dukanta ko ta ina feena ta kasa tabuka komai ds taji wahala sai ta yanke jiki ta fadi qasa a wahalce.

Kamar an jefoshi sai gashi da sauri ya qaraso gunta ganin Fadila ya sa shi shaqure mata wuyah, fadila ta fara kakarin mutuwa, tana dukkan hanunsa, shi ko ya maqureta har jikin bango kamar zai karta, jin muryar feena yayi tana cewa My Moh help me, da sauri ya sake Fadila ya nufi feenah jin jikinta yayi zafih kamar garwashi, da sauri ya sabeta kamar wata baby. Ya wuce ya bar fadila tsaye kamar sakarya. Fashewa tayi da kuka ta fita Sashen Umma tayi don gaya mata K'arya da Gaskia, sai dai Kashh, uwar daure mata gindin ba ta nan taje suna, nan ta zauna a baranda tana jiran Dawowar Umma.

A mota ya sanyata ya nufi Softie's Clinic, hannun bibbiyu Dr Safiyya ta amsheta ta mai umarni da ya tsaya a waje, ya fita nan da nan ta shiga  dubata har kusan awa daya suna ciki. Chan ta leqo tace U can comein , ya bi bayanta, ko da ya shigo dakin yaga har ta kwantar da feenarsa ta sa mata drip da alamu ta samu bacci, Dr Safiyya ta kalli Muh'd tace haba Moh? Why? Da sauri yace me ya sameta Doc? Stress ne, Stress ne main reason din ciwon matarka, sai kuma damuwa, Muhd iya kan sanina kana da arziqi daidai gwargwado, u can provide for ur family, to meke sa ta danuwa? Nd wani irin aiki takeyi ne da yake stressing dinta haka? Ya fara inda inda, well its complicated, ba zaki gane ba, amma pls is she going to be oryt? Tace eh, sbd ta warke ds wuri ya sa Na kwantar da ita, na bata Bed Rest, shes to remain here har sai BP dinta ya sauko, Yace Toh Dr, mungode, ta miqe ta gyara zaman rigarta race Congratulations, U are going to be a Father, It wife is 3months pregnant, Allahu Akbar Muhammad yace  farinciki Mara misaltuwa ya bayyana a fuskarsa. Dr Softie ta fita da sauri ya qaraso kan gadon da take kwance, ya riqe hannunta bacci takeyi har ynzu, yace My feenah kinji abinda Dr tace? Tace kina da ciki. U are going to be a Mother. Shafa kanta ya fara yi a hankali, yana tunanin halin da feena ta tsinci kanta yakeyi, Sabida dashi ne, a hankali ya ce InshaAllah Komai xaizo karshe idan har Umma taji cewa kina da ciki, cikin JINSINTA, dole zata so ki ta so abinda ke cikin ki, kuma AKWAI LOKACIn da Umma Zatayi Alfahari da ke a cikin JINSINTA.

Fadila lafiya kike zaune a nan? Fadila ta fashe da kukan munafurci, tace Umna ni na gaji, ki sa Muhammad ya sakeni, Umma tace SubhanAllah Fadila me yayi zafi haka? Toh Umma saboda matarsa ya kusa kasheni, da ba dan Allah ya ceceni ba wlh da ya kasheni, Maqure min wuya yayi Umma duba, ta daga wuyants tana  nuna ma umma shatin hannun Muhd, Umma ta rafka Salati, tace Shi Na Allahn ya Maqure miki wuya saboda Tubabba,? Fadila tace Eh Umma, ta qara cewa shi na Allahn ya kusa kasheki sabida wata Wadda ba JINSINMU ba? Je ki kira minshi, tace Umma ya sata a mota ya fita da ita. Umna ta xaro wayarts ta miqa mata, kira min shi.

Ganin kiran Wayan Umma ya sa Gaban sa yankewa ya fadi, jiki na kyarma ya dauka da Sallama, ko sallamar bata ansa ba tace duk inda kuke Na'Allah ku dawo ina nemanku, yanxu yanxun nan, yace Umma Nafisa ce bata lafiya an ma kwantar da ita a asibiti, tace banson jin komai, ku dawo gida daga kai har itan ina nemanku na baku minti 15 Diff ta katse wayar., Muhd ya dafe kansa hannu biyu Kansa ya dau xafih matuqa Inallilahi wa ina ilaihir rajiun Muhammad ya furta. Me ke shirin faruwa ne?..

Dedicated _*to Biebee Isa❤

IG: Yar ficika

💃🏻💃🏻💃🏻Bibilicious Biebee ta Feedoh Deedoh ke cewa ku kasance tare da Firdaucy jeeboh don jin yadda Na'Allah zasu kwashe da Ummansa.

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180