JINSINAH 86~90

❄❄ *JINSINAH*❄❄

*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻

*_page_* 8⃣6⃣ *_to_*9⃣0⃣

*_BAYAN_* *_WATA_* *_SHIDA_*

Daga kitchen tafito duk tayi bak'i ga k'aton ciki dak'ar take tafiya "parlour umma ta nufa da sallama tashiga babu Wanda ya amsa mata shiga tayi kai tsaye' "umma ta tarda zaune itada da fadilah d'ukawa tayi tace umma sannu da gida' "Adak'ile umma ta amsa' "juyawa tayi tace anty sannu tsoki fadilah tayi tareda wurga mata harara "tashi tayi tanufa cikin d'akin umma, tana kaiwa bakin k'ofa umma tace, ke tubabba baki gama girkin baneba yunwa mukeji, inda sabo finah tasaba saboda umma bata tab'a kiranta da sunanta ba sai tubabba , "finah tace umma yakusa shine nazo na gyara d'akin kafin ya Ida,,,,,,

              "Tagama gyara d'akin tsaf tayi turaren wuta, d'aki had'auki k'amshi fitowa tayi tanufa wajen abincinta, "kodataje ya ida saukewa tayi,tad'auko coolers tasakama, umma nata tasama fadilah nata itama tasaka nasu d'aukan nasu tayi takai d'aki,tad'auki na fadilah takai mata "tad'auki na umma tawuce sashenta dashi,,,,,,
                ***********

              Sallama tayi tashiga, "fadilah tadinga bin cikinta da kallo wani bak'in ciki ya tasomata  "wucewa tayi ta aje na umma kan daining table, tadawo Taduk'a tace umma nagama akwai sauran abinda yarage? Girgiza kai umma tayi tace babu zaki iya tashi kitafi, Tamik'e kenan zata wuce fadilah tasaka mata k'afa ta tad'eta faduwa finah tayi tare da sakin wata k'ara  sai kuma kaji shiru daidai moh na shigowa dagudu yayo kan finah amma ina kodayazo finah tayi nisa ga jini dake bin k'afafuwanta, "ihu yasaki yashak'are fadilah yace wlhi koka kasheman mata da baby kema saina kasheki,idanuwan fadilah sukayi zuru zuru "tsawa umma tamashi tace dallah sakarta ubanwa yacema ita takadata zaka kashe masu d'iya kan wata shegiya tubabba can, "sakinta yayi yace wlhi umma itace aynaganta saikuma yafashe da kuka fad'a kanta yana sambatu,,,

               "Amir yakira yana kuka amir na d'auka yaji moh na kuka hankalinshi Yak'ara tashi tambayarshi yake lafiya amma yakasa bashi amsa, "kashe wayan amir yayi yajuya kan mitarshi sai gidan moh, baiko bari maigadi yabud'e mashi ba, yafita yayi cikin gida,,,,,,,


                "Yana shiga yajuyo muryan moh part d'in umma dan haka can ya nufa, baiko yi sallama ba yasaka kai dan hankakinshi yagama tashi saboda yasan halin da baiwar Allah nan take ciki, "yana shiga parlour abinda yagani shiyabashi tsoro ganin finah yayi kwance cikin jini kuma da alamu bata da rai,  "kallon tambaya yakema moh dakyar bakinshi ya iya furta moh miyasameta, miyafaru da ita waya yimata haka?,,,,,,,,,
                   ********

Atare yajeroma moh wanann tambayoyin, moh cikin kuka yake nuna fadilah yace gatanan komiye itace saboda ita tasaka mata k'afa ta tadeta, saikuma yafashe da kuka, "kallon tsana amir yamata yace wlhi fadilah idan finah tarasa ranta wlhi ko mi natara idan zaik'are saidai Yak'are Amma kema saikin mutu, "butulu dake kisaurari ranan mutuwarki kedai "itadai umma zare idanuwa takeyi saboda itama hankalinta yatashi ganin finah cikin jini, "Amma dan sankai irin nata saitafara zazzagama amir tijara,"saikuma akacema ita takasheta dazaka dinga yima mutane rashin kunya, toh wlhi aykasan waye ubanta kufara Shari'an kaga idan zakaci riba,,,,,

          "Dan takaici amir sakin baki yayi yana kallon umma datake neman take gaskia , "amir yace moh kamata mukaita asibiti, "moh yace wane asibiti kawai akira liman yamata sallah danta kasheta, "tausayin moh yakama amir dafashi yayi yace karkadamu abokina kaidai mukaita asibiti kajiko? "Girgiza kanshi moh yayi yakama finah sukayi waje da ita, "cikin mota suka sakata, amir ne mai driving saboda moh duk ya rud'e sai kuka yake kamar k'aramin yaro,,

               "Gudu yadingayi kamar zaitashi sama, "suna isa softie's clinic amir bai ida tsayawa ba moh yafito yana neman d'auki nurse ce tafito da gadon marassa lafiya aka kama finah aka azata ga jini sai binta yakeyi, "sukansu nurse d'in ganin jinin data ke zubdawa yasa suka tsorata, "d'akin theatre aka wuce da finah saboda ceto ranta dana babynta duk dadai kamar ta mutu, "dr safiyya ce tafito tare da takarda fuskanta ba annuri tace moh saka hannu nan saboda za'ama finah aiki, "kuka yafashe dashi yace wani kema gawa aiki, sambatu yakamayi, Amir ne yasaka hannu,,,,,,




_Awan_ _finah_ _shida_ _chur_ _cikin_ _theatre_ _room_, _ba'a_ _fiddota_ _ba_ _agogon_ _hannunshi_ _moh_ _ya_ _kalla_ _yace_ _Amir_ _kaga_ _haryanzu_ _shiru_ _kodai_ _afad'ama_ _anty_ _aysha_ ,,,

Amir yace tayimi? Sokake ta ida rud'a asibitin ko? shiru moh yayi sai hawaye, "can dr safiyya tafito sai faman zufa takeyi, "kallonsu tayi tace kutardani office, gabadaya suka bita office, suna shiga, tace Su zauna suna zama ta kallesu, ta numfasa tace am sorry to say munyi iya bakin k'ok'arinmu Amma, bata idaba moh yace dan Allah karkice ta mutu, saikuma yafashe da kuka,,,,,

*Nima* *yar* *ficika* *nace* *Allah* *yasa* *bata* *mutu* *ba* 😭😭😭😭

*_Dedicated_* *_to_* *_biebee_* *_isa*❤

IG:yar_ficika





© *_written_* *_by_*

                    *_Feedoh_* *_Deedoh_*✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180