DIJAH 106~110
🏵🏵DIJAH🏵🏵
Feedoh yanmata
1⃣0⃣6⃣~1⃣1⃣0⃣
Naf yanata lallashin hamza, yace haba hamza kanada maganin k'addara ne? Ko kanka aka fara kad'a mutum ya mutu ina ga aiba da gangan kayi ba, Allah idan bakayi shiru bazan kira Ammi nagaya mata, hamza yai sauri ya d'ago fuskanshi data kumbura saboda kuka yace plz naf karkaman haka, kasan yanda Ammi take wlhi cewa zatayi saitazo katsina, kayi hak'uri girgiza kai naf yayi yace toh shikenan zan hak'ura amma saika daina kuka, kana abu kamar ba namiji ba, hamza yace shikenan nadaina, "suna cikin magana tawa nurse ta fito harta wuce tadawo tace bawan Allah yakamata ka mik'ama Allah lamuranka tunda kakawo patient kake kuka haryanzu, haba saikace ma ance ta mutu? Duka suka mik'e tsaye suna kallon nurse shidai hamza bakinshi sai rawa yakeyi, Nafeeu ne yayi k'arfin halin magana, yace baiwar Allah ai kukan da kikaga yanayi wata nurse ce ta fito tacemana yarinya da yakawo ta rasu, "mamaki ya cika nurse saboda ita tasan bata mutu ba, tace waya gaya maku ta rasu? Naf yace wata nurse ce, girgiza kai tayi tace gaskia bata rasu ba, cz yanzu haka daga wajenta muke, suna cikin haka saiga doctor ya fito, yace sistr mikike baki wuce ba? Tace wlhi harna wuce na dawo, wai wanan patient d'in da aka kawo d'azu shine akacema yayanta tarasu, doctor yayi murmushi yace bata rasu ba amma akwai wanda ta rasu ciki shiyasa, saidai gaskia itama tana cikin hali, "hamdala su hamza sukayi, naf ne ya kalli hamza yace toh hankali saiya kwanta bata mutu ba, murmushin k'arfin hali hamza yayi, doctor yace yan samari Ku biyoni office........
*****************************
Da sallama suka shiga office, murmushi doctor yayi yace yansamari have a seat zama sukayi, saida yagama yan rubuce rubuce kana ya juyo kansu, yace cikinku waya banketa jiki sanyaye hamza yace nine, "doctor yace toh gaskia sakamakon buguwar da tayi saboda ta bugu sosai ta shiga commer, salati su hamza suka d'auka ga baki d'aya hardai hamza daya firgita ganin halin da yashiga doctor ya dinga kwantar mai da hankali, yace karkadamu zata iya farkawa at any time, dafe kanshi hamza yayi dayaji yana saramashi, naf ne yayi k'arfin halin yima doctor magana, "hamza ne yace doctor plz a shirya muna ambulance gobe takaimu kano dan zantafi da ita abuja toh d best ting mubi jirgi, " doctor yace ba damuwa goben saku tafi, godia sukama doctor kana sukabar office d'in.....
Suna fitowa daga office d'in naf ya kalli hamza yace saboda mi zaka tafi da ita? Hamza yace saboda atunanina zatafi samun kulawa a asibitin abuja, kuma aikagama can nake, Nafeeu yace toh Hamzariee iyayenta fa? Hamza yace yanzu haka can zamu inda na kad'eta na nema iyayenta namasu bayani idan yaso sai wani ya bimu cikinsu, da wanan shawaran Nafeeu ya gamsu, "tafiya sukayi basu tsaya ko inaba sai inda hamza ya kad'e dijah, koda sukaje ba mutane wajen sai jini, daga tsallake suka hango wasu mutane, tsallakawa sukayi, sukama mutanen nan sallama, Nafeeu ne yace dan Allah kuna nan akayi accident d'aya yace ina wajen, Nafeeu yace kokasan gidansu yarinyar? Nan yacemai baima tab'a ganinta ba, haka dai suka dings nema amma kowa cewa yake baisanta ba, Nafeeu ne yayi ajiyar zuciya yace hamza abunnan fa yafara bani tsoro, hamza yace wlhi nima Nafeeu, haka dai sukagama zagaye amma babu alamar wani yasanta, wajen mutanen nan suka koma, Nafeeu ne yabasu number waya yace dan Allah koda kunji wasu na nemanta Ku kirani amsa sukayi sukace in shaa Allah , godia sukayi kana suka tafi "cikin mota bamai cema wani k'ala kowane da abinda yake tunani, naf ne yayi gyaran murya yace yanzu hamza yake nan? , hamza yace naf tafiya da baiwar Allah nan shine kawai yanzu idan nabarta wana barmawa gashi ba'a ga iyayenta ba gashi ni bansan sanda zan k'ara zuwa katsina ba, kawai natafi da ita shiyafi, idan ankiraka ance anga wani nata kaga komai yazo da sauk'i , naf yace hakane kuma, toh yanzu yazakayi da Ammi? Murmushi hamza yayi yace Ammi nah aykasan batada matsala idan mun isa abuja gobe na mata bayani, " waya hamza ya zaro yakira Frnd d'inshi dake kano gaisawa sukayi yace hamid kaman booking flight sonike inbi jirgi gobe inkoma Abuja amma nida patient ne, hamid yace shikenan abokina bakomai sai goben godia hamza yamashi kana ya kashe wayanshi...
K'arfe takwas na safe hamza yagama shirinshi tsaf yana jiran Nafeeu saboda jirginsu 12 ne, yana nan tsaye naf ya murd'a k'ofa ya shigo da sallama amsa sallamar hamza yayi tare da rungume naf, yace aboki sai yanzu hararanshi naf yayi yace bayan kahanani baccin safe, "murmushi hamza yayi yace sirikin naka kake harara Ashe kuwa bazan baka Afrah ba, kunne naf yakama yace kayi hak'uri ya hamza ba zan k'araba, dariya hamza yayi yace shikenan, mutafi karmu makara, naf yace hakanefa "koda suka isa asibiti angama komai natafiya suna zuwa clearing hamza yayi da asibiti kana suka d'auki hanyar kano, "suna isa kano basu tsaya ko inaba sai airport koda sukaje olrdy jirgi yafara boarding suna zuwa basu wani b'ata lokaci ba sukagama komai, hamza ne ya juyo ya kalli naf , yace Nafeeu nagode da taimakon d kaman Allah yasaka da alkairi, Nafeeu yace bakomai hamza Allah yakaiku lapia, Amin hamza yace ya juya ya hau matattakalar jirgi, yana shiga bada dad'ewa ba jirginsu yatashi, " nidai nabisu da adua Allah yasaukesu lapia, Allah kuma yaba dijah lapia....
www.phirdauceejeebo.mywapblog.com
Written by
Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment