DIJAH 136~140
🏵🏵DIJAH🏵🏵 Deedoh
Feedoh yanmata✍🏻
1⃣3⃣6⃣~1⃣4⃣0⃣
Likita na isa wajen gadon dijah, yaga hannunta na motsi,"amma Hamzariee baigani ba, can k'afanta yafara motsi, limits sai murmushi yakeyi, "hamza yace doctor lapia wai naga sai murmushi kakeyi, fad'ad'a murmushin shi yayi yace kai yanzu bakaga mi nakema murmushi ba, yace "Eh, yace duba k'afar patient d'inka, "yana dubawa yaga tana motsi, "rugawa yayi ya rungume daddy yace daddyn Affy tafara motsa jikinta, "daddy yace toh bazaka godema Allah ba, "d'aga hannunshi sama yayi yana godia harda kwalla, yana gamawa ya rungume Ammi, sai kwalla yakeyi, kanshi Ammi ta shafa tace toh miye na kuka, "bayan abinda muke nema yasamu, wajen gadon dijah suka tafi, "suna zuwa daidai dijah na bud'e a hankali, tana bud'e idon tabi d'akin da kallo, kallon su Ammi tadingayi, "idonta ta d'ora kan hamza ta k'ura mashi ido kamar tasanshi, "cankuma ta kalli Afrah, "murmushi tama afrah ta d'aga hannunta da kyar alamun afrah tazo, "matsawa afrah tayi ta rik'e mata hannu, "affy tace sannu kinji, "murmushi tama afrah, "su daddy da Ammi suka dinga mata sannu, "Ammi tamatsa kusa da ita, "ta dafa kan dijah tace sannu kinji, "itadai binsu tadingayi da kallo, "doctor yace Alh abarta ta huta muje office in as an ganinku.......
Office d'in doctor suka tafi akabar afrah wajenta, "suna shiga gaisawa suka k'arayi da doctor, "murmushi doctor yayi yace su hamzarieen Ammi yau ba baka sai kunne,"ji yanda kake dariya, "Anya ba sirikar Ammi zata zamaba, "dariya daddy yayi yace kaima dai kafad'a, "sun d'anyi barkwanci kana doctor yayi gyaran murya, "doctor yace toh Alhamdulilllah, ranan da ake jira gashi tazo, "yau gashi patient d'inmu tatashi, "Amma zamu rik'eta saboda sai ankoya mata tafiya,"domin yanzu jikinta duk ba kwari, saboda ta dade kwance, "Amma bawani dad'ewa zatayiba, "hamza yace doctor kamar kwana nawa zatayi ne? "Doctor yace Hamzariee miye ka damu, ayta kusa komawa gida in shaa Allah, bazan iyacema ga kwanakin ba, idan jikinta yayi sauk'i zata koma gida kajiko, d'aga kai hamza yayi alamar ya gamsu, " godia sukama doctor suka koma d'akin dijah...
Koda suka koma d'akin sun tarda dijah zaune, "murmushi Ammi tayi, tace waya tadata zaune, "affy tace nice Ammi naga ta dad'e kwance, Ammi tace gaskia yar gidan daddy, Ashe kinfara hankali, "turo baki affy tayi, "daddy yace kyalesu kinji, "daddy yace sannu baiwar Allah, a hankali dijah tace yawwa, "dijah tace dan Allah ku suwaye kuma ya akayi nazo nan?, "dafa kanta Ammi tayi tace kiyi hak'uri harki samu sauk'i, kinjinko? D'aga kai tayi,"hamza yace sannu kinji tace yawwa, "Hamzariee yace dan Allah ya sunanki? Ammi tace haba Hamzariee nah miye na sauri?, "murmushi hamza yayi yace inasan nasani be Ammi Nah, "kamar daga sama yaji tace sunana dijah, "maimaita sunan yadingayi dijah, "murmushi daddy yayi yace toh kaji hankali ya kwanta, "yace eh mana, "haka suka dinga fira har marece yayi, sukama dijah bankwana suka tafi....
www.phirdauceejeebo.mywapblog.com
IG:yar_ficika
Written by
Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment