JINSINAH 61~65

❄❄ *JINSINAH* ❄❄

*_Feedoh_* *_yanmata_*✍🏻

*_Page_* 6⃣1⃣ *_to_* 6⃣5⃣

Wani irin kuka moh yafashe dashi, shine yafarkan da finah, a hankali tace my moh lafiya? Juyowa yayi ya kalleta murmushin k'arfin hali yayi yace bakomai my baby, girgiza mashi kai tayi tace plz my moh karka b'oyeman komai, just tell mie mike faruwa, nan moh ya kwashe yanda sukayi da Umma yagaya mata amma baigaya Mata tana da ciki ba, murmushi tayi tace dama nasan za'ayi haka my moh karkadamu naji sauki, muna iya zuwa, zaro ido yayi tace yes muna iya tafiya,,,,

              "Dr Safiyya ce tashigo, ganin finah na k'okarin tashi yasa takara so dasauri tace, nafisa wia re u going? Bakisan halinda kike ciki baneba? Murmushin k'arfin hali finah tayi tace don't worry doctor aynasamu sauki gida zamu tafi yanzu,,,
                     ***

Arazane dr Safiyya ta kalli moh, tace moh Anya kanasan yarinyar nan kuwa bed rest fa nabata amma kake k'okarin cewa kutafi, moh yace wlhi dr ba laifina baneba mahaifiyata, finah tace shhhhhh my moh wannan issue din family house ne, girgiza kai yayi,

          "Murmushi dr Safiyya tayi saboda yanzu tagano inda matsalar take, dr tace shikenan moh kuna iya tafiya, godia moh yamata Yakama finah suka tafi,,,,,,

                 "Tundaga bakin gate yafara juyo muryan Umma, finah inbanda adua ba abinda takeyi, suna shiga gida, Umma tayi Kansu kamar kura, finah tagama razana bayan moh takoma, tana hawaye,,,,
                     ***

                "Umma tace yanzu kai moh kan wannan tubabbar saika Kama Fadilah ka buga, kumata taro dan kunga baninan, "moh yace wlhi Umma ba haka baneba, itatace fa ta dinga bugunta harsaida ta suma,,,,,

           Umma tace rufeman baki shanyayye, idan ta bugeta ayta isa itaba *_JINSINKA_* Baceba dazaka bugeta sabida wannan shegiyar tubabba, toh yau Zan kawo k'arshen iskancin, idan kai anshanyeka nikam babu shegen daya shanyeni,,

               " paper da biro ta d'auko tace gashi sakinta nakeso kayi kuma Saki ukku, basuba koni mai d'auko maku rahoto saida gabana yafadi, finah ce ta d'uka tana kuka tace Umma dan Allah kiman duk hukunci amma karki rabani da moh, wlhi shine gatana, shine bangon dana jingina, tsoki Umma tayi tace KO ubanki ne yau saikun rabu, "Fadilah mitakeyi inba murna ba🙄🙄, Fadilah tace ke tubabba yau saikin bar gidannan tunda ba gidan ubanki baneba, muhammad yace ayke naga gidan ubanki ne,,,,

             "Mari Umma ta wanke moh dashi tace nizaka zaga ba itaba, kuma Masan Allah saika saketa inba hakaba na tsinema, fashewa finah tayi da kuka, tace moh bansan sabodani mahaifiyarka ta tsinema, kayi duk abinda tace,,,

              "Duk'awa moh yayi yace Umma kiyi hakuri karki tsineman, wlhi zanyi komai saboda farin cikinki, amma Umma yazakiyi da nawa farin cikin, taya zaki rabani da uwar yayana, dan Allah karkisa nayi nesa da d'anda finah zata haifaman, idan nasaketa da ciki Ina zata, shekara nawa ina Neman haihuwa sai yanzu nasamu nayima Allah butulci, dan Allah Umma kibari finah tahaife abinda ke cikinta gidana,,,,,

                  "Wani irin razana Fadilah tayi tace wlhi Umma bawani ciki karya sukeyi, "shiru Umma tayi tace na'Allah ka tabbata tanada ciki? Moh yace wlhi Umma finah nada ciki na wata ukku,,,,,

           "Umma tace shikenan kinci albarkacin abinda ke cikinki, dan kar nakoreki ki haifeshi ki had'aman zur'ia da *_JINSIN_* Arna,, "d'aki Fadilah tanufa da gudu tana kuka, tanata zage zage,,

          "Umma tace zaku iya tafiya, tashi finah tayi amma takasa, d'ukawa tayi tana wayyo cikina, kafin moh ya juyo tuni ta fad'i sumammiya ga jini na bin k'afarta,,,,,,

Allah yasa finah ba miscarriage zatayi ba😭😭😭😭



*_Dedicated_* *_to_* *_biebee_* *_isa_* ❤

IG: yar_ficika

© *_written_* *_by_*

               *_Feedoh_* *_Deedoh_*✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180