DIJAH 216~220
🏵🏵DIJAH🏵🏵
Feedoh yanmata✍🏻
2⃣1⃣6⃣~2⃣2⃣0⃣
Tunda dijah tayi sallan asuba bata komaba, tafara shiri, "mama ce tashigo d'akin taga tanata faman shiri, mama tace haba dijah saifaman shiri kike kamar wadda zamu tashi sama, dariya dijah tayi tare da gaida mama, dijah tace mama wlhi na k'agara naje naga Aminiyata hanne ne, "wannan kayan dakikaga ina had'awa duk ita zanba, saboda kafin babana yarasu yakoyaman cewa idan zakayi kyauya kayi da abinda kafiso, kuma wlhi mama rainane kawai ban iyaba hanne, amma komai zan iya bata, "mama tace Allah sarki Allah yajak'ansu da rahma wlhi ina alfahari da irin tarbiyan dasuka baki, "kuma hakane hanne ta can can ci komai , saboda itama tamaki halarci, dijah tace hakane mama, "wajen 7am su dijah suka isa gidansu Hamzariee tana shiga Ammi ta rungumeta tace k'iri k'iri anman kwacen d'iya dariya akayi gaba d'aya, suka gaisa da juna, da'kin affy dijah tanufa ta tarda tana shiri rungume juna sukayi cikin kewar juna, "dijah tace sis bari naje d'akina zan d'auka wasu kaya, tana shiga d'akinta Hamzariee ya biyota, jitayi an murd'e mata kunne k'ara tayi, tana juyowa taganshi tsaye, dijah tace kai ya hamza minayi, "hamza yace wlhi kin ci ganye yarinya, yanzu kinzo koki nemeni, amma nakusa daidaitaki ay, zakizo hannu yarinya, "dariya tayi tace wlhi na Kira wayanka iz not reachable, tab'e baki yayi yace naji, "itadai muemushi tayi tacigaba da abinda takeyi, danta San halinshi da rigima....., "shiri sugamayi tsab suka fito dijah da hamza da affy mota guda, sai daddy baba, mama da Ammi mota guda, takwas daidai sukabar gida, sai kt, Allah ya saukesu lapia.......
*****************************
K'arfe d'aya su dijah na katsina, saida suka tsaya sukaci abinci, Hamzariee yakira naf, Nafeeu nazuwa aka gaisa suka d'auki hanyar bakiyawa, "suna cikin tafiya sunzo daidai inda Hamzariee yakad'e dijah aka gwadama su mama, mama da Ammi harda kwallah, "dijah tadinga nuna,masu hanya har suka iso, "garin na nan yarda tabarshi, ba abinda ya canja mata, tadinga,nuna masu hanya harsukazo wajen wani kwangon gida, dijah tace kamar nan ne gidan kamar kuma ba nan baneba, saboda yanda taga gidan ya rushe, "saidataga gidansu hanne kana tayarda gidanne, "suna isowa k'ofar gidan mutane suka zagayesu babu wanda yagane dijah cikinsu, "fitowa sukayi daga mota, "Hamzariee yace my babe nan kikayi rayuwa dama, "murmushi tayi tace eh, "wani yaro ta tambaya tace dan Allah Inna larai na nan yaron yace eh, Amma nasan yanzu tana wajen bara, "kirji dijah tadafe tace bara, "yaron yace eh mana bara, "saida dijah tayi hawaye sudai su Ammi yan kallo sukazama, "dijah tace ina take baran, kamar daga sama sukaji wata busassar murya tana kugafara naji ance nayi bak'i suwaye, dijah tajuya da sauri danko a mafarki zata game mai muryan....
Dijah tace inna nice, Inna larai tace kewa, "murya na rawa dijah tace Inna dijah ce, Inna larai tace dijah wace dijar badaita nan gidan ba, dijah tace ita, "kuka Inna larai tasaki, tace kumatsa Inga Yar Aljanna, inna larai harda fad'uwa wajen sauri Ammi takamata tatadata, tak'arasata wajen dijah, Shafa dijah tayi saikuma ta fashe da kuka, "dijah kuka Inna larai kuka, saida sukayi mai isarsu, "kana Inna tace keda suwaye, kushigo, "ya Allah suna shiga gidan sukaga tashin hankali, gaba d'aya gidan yakoma kwango, gawani uban bola da aka tara gefe guda sai wari ketashi, babu inda keda d'aki duk yarushe, dijah tace Inna haka kike zama, Inna tace haka nake zama Alhakinki ne yakamani, saikuma tafashe da kuka, "da kyar akasamu tayi shiru, "dijah tace Inna ina kike kwana, inna tace cikin d'akin tumakai nake kwana, shikad'aine garage lafiyayye, babu wanda baima Inna larai kukaba, "niko deedoh nace abinda ta shukane take girbewa da hanuwanta....
Dijah tace Inna ga iyayena nagani fa, dakuma iyayena wanda danabar nan koma hanuwansu, "dijah ta kwashe komai tagayama Inna, saida Inna tayi kuka, tace dijah duk nina jamaki wannan abun dama saida malam yagaya Mani, yau ga irinta nan, nagani, "ban canci kiyafeman ba, saboda nina jefaki wannan halin dakika shiga, "daddy yace ah ah Inna dama can k'addarantace haka kuma gashi tasanadiyar barinta gidan taga iyayenta na asali, dijah tace wlhi Inna nayafe maki duniya da lahira, Inna kuka taketayi "tacema iyayen dijah suyafe mata sukace sunyafe, "inna larai tace inama malam da lubabatu na da rai sukaga irin wanan abin farin ciki, dijah harda hawaye tayi tace haka Allah yahukunta, "dijah tace Inna ya'akayi gidan yafad'a haka, Inna tace hmm bari d'iyar nan hakkinkine, bayan kintafi, damina takama, kawai sai Inga d'aki yafad'a duk inda nakoma saiya fad'a da haka har gidan yafad'i d'akin tumakai kawai yayi saura, Ana haka sai wasu mutane sukazo sukaceman, yakamata nafara kasuwancin auduga, a burni saboda Ana samu, bansansuba danaji maganar kud'i bawani bincike, na tambayesu ya akeyi sukagayaman kud'i zansa masu yawa, kuma na amince, saida sukasa nasaida komai nawa nakoma banida komai, nabasu kud'i ashe yan damfarane, saidaga baya nagane yan damfara ne, nayi kuka, tundaga sannan nagane hak'k'inki ne kebina, kafin kicemi narasa komai sainayi bara zansamu abinci, "kinji abinda yasameni, babu wanda baiyi kuka ba, "baba yace sai hak'uri dama munzo mugankine kuma gashi halin damuka sameki idan badamuwa kuma idan kinada buk'ata zaki iya binmu can burni "Inna larai tafashe da kuka, tace na amince, dama akwai lokacin da malam yaceman watarana sauna koma k'ark'ashi dijah kuma ga lokacin yazo, kaicona kaicona, kuka tayi sosai dakyar su mama suka lallasheta, "hamza da naf tunda akafara magana basuce k'alaba, "Inna tace dijah kinyi aurene? Dijah tace ah ah Ammi, affy tace tadai kusa ga sirikin bakucan tagwada mata hamza, dariya Inna keyi tace sannu sirikina, gaskia kayi sa'ar mata, Allah yabaku zaman lapia, duka sukace Amin..
Dijah tace waini ko Inna ina hanne, Inna tace yar albarka tayi aure dijah tace haba "sallama sukaji dasauri dijah tamik'e dantagane muryan, da gudu taje ta rungume hanne tana hanne saikuma suka fashe da kuka, saida akamasu magana kana suka daina, "dijah tace hanne yanzu nake tambayarki, hanne tace ina gida akazo akagayaman nace Bari na garzayo, "dijah tace hanne gafa iyayena, aykuwa nan sabuwar murna tatashi, "hanne tagaida su daddy suka amsa da yimata godia tace bakomai ay dijah yar uwace wajenta, hanne tace badai kinyi aure ba, dariya dijah tayi, Inna larai tace andai kusa ga mijinta nan, "gaidashi hanne tayi, "hanne taja hannu dijah sukayi gidansu gidansu hanne akayita murna, "d'aki suka shige suka kulle Kansu, nanfa fira tatashi, hanne tace dijah ya akayi kikagane iyayenki, "nanfa dijah ta labarta mata komai, said a hanne tayi kuka, "tace saida kika tafi nagane munyi wauta, Ashe har had'ari kikayi, "hanne tace bayan munrabu nadawo unguwa Abu ya isheni narasa yazanyi, innarmu nafad'a mawa fad'a taman sosai, shiru shiru Inna larai taga baki dawo, saita aykoman nace bansan inda kika tafiba, ke har aka kwana, nanfa gari ya d'auka kin gudu, kuma kowa Inna larai yakeba alhakin guduwarki, "hanne tace wlhi dijah har ciwo nayi narashinki, daga baya na hak'ura Ashe da rabon zamu gana, "murmushi dijah tayi tace aykam, yaushe kikayi aure hanne tace shekara guda kenan, "dijah tace kuma banga yaroba bugu hanne ta d'aka mata tace saina gama amarci, dariya sukayi gaba d'aya, fira sukeyi sosai basusan tym yajaba, bugun k'ofa sukaji innarsu hanne ce tace toh kubud'e dijah ana jiranki zaku tafi.....
www.phirdauceejeebo.mywapblog.com
IG: yar_ficika
Written by
Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment