DIJAH 211~215

🏵🏵DIJAH🏵🏵

Feedoh yanmata✍🏻

2⃣1⃣1⃣~2⃣1⃣5⃣

Suna shiga mota hamza yafara gunguni, affy kuma dariya kawai takeyi, Ammi tace haba Hamzariee nah nayaushe zamu takurama yarinya, yaufa taga iyayenta, yakamata abarta dasu suna buk'atar d'iyarsu yanzu, itakum tana buk'atar iyayenta, dan Allah kasama ranka hak'uri, duka yaushe dijah zata dawo gidanka, bama hakaba duk idan kanasan ganinta kazo, gari d'aya fa kuke, "amma yanzu mahaifiyarta harta ce mu'ara mata ita aymun bata kuma dijah bawai takoma gidansu ba, kaima kasan zata dawo gida, "jikin hamza yayi sanyi yace hakane Ammi nakuma gode sosai, "daddy dai da affy basuce masu k'ala ba, "suna isa gida hamza duk saiyaga gidan yamai bak'i daurewa kawai yakeyi d'akinshi yanufa, juyi yakeyi saman gado, "waya yajawo yakira Nafeeu, naf nad'auka yace aboki guess what? Naf yace what? Da ihu hamza yace anga iyayen dijah hamza yace dagaske, hamza yace wlhi, "nanfa ya labartama Nafeeu komai, tausayama dijah nafiu yayi, yace wlhi Hamzariee yarinyar nan taga gararin rayuwa, hamza yace wlhi, "Hamzariee yace malam kayi maza ka turo dan gaskia ina buk'atar dijah kusa dani, dariya Nafeeu yayi yace saina shirya, hamza yace toh wlhi bazan jirakuba, "dariya Nafeeu yayi, bankwana sukayi suka aje waya, "kiran dijah hamza yayi bugu biyu tayi tad'auka tace hello ya hamzariee, Hamzariee yace gaskia my babe wlhi nafara mssn naki, gaskia zanzo na d'aukeki, dariya dijah tayi tace haba my d'an saurayi kamar gobe ne zamu koma inuwa d'aya, yace hakane amma nidai still gidan yaman duhu, tace kayi hak'uri da mungama ganin dangi zandawo, haka suka dinga firan soyayya kamar karsu rabu, .....

*****************************
Dijah ce zaune parlor duk tatakure, mama tazo parlor jawota tayi, tace Khadijah duk kintakura, ko gidanku zaki ka? Kamar daga sama sukaji maganan baba, yace dole taji daban Hajia, aybata sababa, dijah tace ah ah mama nafisan nazauna kusa daku Nima, "fira suka dinga janta dashi kamar zasu maidata ciki, itako sai dad'i takeji, cikin ranta tace ashe haka iyaye suke, "sai wajen 1:00am suka tashi Hajia zainabu tace dijah d'akinta zata kwana, Alh Lawal yace yau tawaye za'aman kenan, mama tace eh mana,

Da safe kafin dijah tatashi angama komai sai wajen sha d'aya tatashi, tana tashi wanka tashiga, tana fitowa shiryawa tayi cikin purple super simple makeup tayi amma tayi kyau, sakkowa tayi k'asa ta iske iyayenta duk'awa tayi har k'asa ta gaidasu amsa wa sukayi cikin farin ciki, baba yace dijah antashi kenan tace eh baba, mama tace toh muje kici abinci, mama ta dinga ba dijah abinci da kanta harsaida taga ta k'oshi, "gaskia iyaye rahmane, Allah kabarmu da iyayenmu, Amin "baba yace dijah zanje nasami daddynku dan gobe nakeso muje bakiyawa, dijah tace Allah yakaimu, mama tace amin...

Kafin kace mi gidansu dijah yacika tab da dangi anata zuwa ganinta dijah harda kukanta, ashe ita d'iyar dangi ce gaba da baya, kuma sukama dijah kyauta sosai, tadinga godia tana kuka, sai marece kana tasamu ta natsu, "wayarta tad'auko misscal d'in Hamzariee takai guda 10, "zata kirashi kenan, taga anbud'e d'aki, tsaye yayi yanata kumbure kumbure shi adole fushi yakeyi, dariya takusa kwacema dijah, "gabanshi taje tace nasan nayi laifi charming amma kayi hak'uri yanzu naga calls d'inka, wlhi bak'i muka dingayi, "murmushi Hamzariee yayi yarungumota, yace bakomai my babe kinsan ban iya fushi dake, tace tnx hubby, hamza yace yaushe kike gama exams dijah tace Monday hamza yace yau Friday Allah yakaimu, dijah tace amin, dijah tace charming baba yace gobe zamuje bakiyawa, hamza yace eh aydamu za'ayi tafiyan, dijah tace harda affy hamza yace eh, " Hamzariee yace Ammi tace yaushe zaki dawo gida, dariya dijah tayi dantasan ba ruwan Ammi, hamza yace my babe wlhi gidannan bak'i yakeman da baki, dijah tace kayi hak'uri d'an saurayi komai yakusa zuwa k'arshe, "sai da hamza yayi isha kana yabar gidansu dijah badan yaso ba, haka suka rabu suna kewar juna..............

www.Phirdauceejeebo.mywapblog.com

IG:yar_ficika

Written by
           Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180