JINSINAH 31~35
❄❄ *JINSINAH* ❄❄
*_Feedoh_* *_yanmata_* ✍🏻
*_page_*3⃣1⃣ *_to_* 3⃣5⃣
Street gidanshi ya nufa cikin murna, saida yatsaya yayi take away dan yasan bazai samu abinciba, "yana isa parlor ya tarda yar mulkin, sallama yayi, tsaki tamashi, rab'ata yayi yawuce, habaici tafara yimashi, juyowa yayi da baya, yace Fadilah ki gyara kalamanki akaina nifa mijinkine, ahaka kikeso kisa nak'i kara aure,? Kinyi kuskure bama kad'anba, idan kina shiga hankaliki kishiga, dan in shaa Allah aure nah nan kusane, garama kisan abinda kike ciki, yana kaiwa nan yajuya yashiga d'aki, baijira mizatace b,,,,
"Fadilah tace to kayi auren mugani, zanga inda zata shigo, gidanan nikadai kedashi, kuma ko mina tara idan zai kare saidai yakare amma sainaga ba'ayi aurenan ba, saikuma tafashe da kuka tanufa d'akinta tana kuka,,,
"Yana shiga d'aki waya ya d'auka yakira Amir, bugu ukku Amir ya d'auki ways da sallamarshi, amsa mashi muhammad yayi, Amir yace abokina ya akayi andace ko? Muhammad yace andace, nanfa yakwashe duk abinda yafaah. yagayamashi, Amir yace Alhamdillah, sund'an tab'a fira kana sukayi bankwana, da alk'awarin gobe zaizo yaga *_NAFISAH_* "Wayan nafisa yayi dialing takusa tsinkewa kana ta d'auka, sallama tamashi, shikanshi saida yaji wani abu ya tsikareshi, saida tace hello kana yadawo duniyar dayatafi, amsa sallaman yayi,,, "gaishe shi tayi amsawa yayi yace my feenah yakike, finah tace lapia lau, ya hanya muhammad yace hanya gatanan munshata, nafisah tace dear dama inaso ka k'arama su Anty Aysha godia, d'azu suka bani wani foam na islamiyya na cike, muhammad yace gaskia Amir da matarshi sunzama aminan kwarai, nagode sosai kuma in shaa Allah zanzo gobe gidan, nafisah tace Allah yakaimu, nanfa suka bud'e shafin firan soyayya, nidai Deedoh har bacci ya d'aukan bansan sanda sukagama soyayyar tasuba,,,,
*_BAYAN_* *_SATI_* *_BIYU_*
Muhammad ne office yana tsaka da aikinshi, wayanshi tayi ringing, yana d'agawa yaga umma ce takirashi, d'agawa yayi da sallama, amsawa tayi, Umma tace kazo yanzu inasan ganinka, muhammad yace toh Umma gani nan, tattara takardun gabanshi yayi, yatashi, kulle office d'in yayi, yamik'ama sectarian key d'in office d'in yawuce,,,
"Yana isa parlor ya tardata, wuri yasamu yazauna, yace sannu da gida Umma, Umma tace yawwa na Allah, ya aiki, muhammad yace Alhamdulillah "Umma tace waini na Allah baku daidaita baneba da wannan tubabbar? Muhammad baiso sunan da mahaifiyarshi takira nafisa dashiba, Umma tace na Allah dakai nake, muhammad yace Umma mundaidaita, Umma tace tomi ake jira, kosaitagama yin arziki dakaine, Allah yasani bansan auren nan, umarnin yaya kawai nabi, shidai baice komai ba, Umma tace abinda yasa na kiraka ka gyaraman d'ayan part dinnan, dan gidanka zankoma, komai cabana za'ayishi, nankuma nasaka yan haya, saida gaban muhammad yafad'i, Umma tace kobaka jiba, muhammad yace naci, insha Allah kuma zanyi yanda kikace, tace yawwa na Allah tashi katafi Allah yamaka Albarka,,,,,,
"Tuki yakeyi amma hankalinshi, baya tare dashi Allah kad'aine yakashi gidan amir lafiya, sallama yayi ya k'utsa kanshi cikin parlor dayake yana shiga gidan direct, parlor yatardasu, wuri yasamu yazauna, muhammad yace mijin Fadilah angon nafisa yanaganka haka, Aysha tace ayshine, numfashi yasauke, yace bari abokina, abin Umma naso yafi k'arfina, atare sukace badai tace bazaka aureta ba kuma? Muhammad yace ah ah, amma kaji abinda tace, yakwashe komai yagaya masu, gyaran murya amir yayi, yace hak'uri zakayi muhammad kayi yanda tace, Aysha tace toh kai ranks ya dade aybanga abinwani tada hankaliba, karma kawani damu, yake kawai yayi, yace ina finah, Aysha tace taje islamiyya amma gab take da dawowa,,,,
"Suna cikin fira amma shikam muhammad hankalinshi nakan hanyar shigowa dan yanasan yaga nafisa, 6:15pm tayi sallama cikin muryanta mai sanyi, amsawa sukayi, shiga tayi parlor, muhammad yakasa d'auke idonshi akanta, saboda takara mashi wani kyau, Amir ne yace malam kallon ya isa haka, dariya sukayi, nafisah tace Anty sannunku da gida, Aysha tace yawwa mamana, Amir ma ya amsa, tare da tambayanta bawani damuwa ko, nafisa tace eh, "gaida muhammad tayi amsawa yayi cikin sakin fuska, d'akinta ta wuce dan tacanja kaya, tana cikin canja kaya, aysha tazo tace idan kingama mijinki na jiranki, murmushi tayi ta sunkuyar da kanta k'asa dariya Aysha tayi tafita,,,,
"Shikad'ai ta tarda parlor wuri tasamu tazauna, kallonta yayi yace finah magana nakeso muyi dake, tace go ahead, muhammad yace yaushe kika shirya maganan auren? Nafisa tace ayni magana bata hannuna tana wajensu Anty aysha sune zakama magana, muhammad yace hakane, firan masoya suka dingayi harsaida aka kira magrib kana sukayi bankwana,,,,,
*_Dedicated_* *_to_* *_biebee_* *_isa_*❤
IG: yar_ficika
© *_written_* *_by_*
*_Feedoh_* *_Deedoh_*✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment