JINSINAH 06~10
❄❄JINSINAH❄❄
Feedoh yanmata✍🏻
Page0⃣6⃣to1⃣0⃣
Muhammad bai tsaya ko inaba sai gidanshi, yana zuwa yayi horn gate man, ya wangale mashi gate, hancin motarshi ya cinna cikin gidan, parking space yasamu yayi parking, fitowa yayo ya kulle motar yayi cikin gida,
Parlor ya iske madam ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya, sallama yayi dakyar ta amsa murmushi yayi, dan inda sabo yasaba, zama yayi kusa da ita, yace sannu da gida fadeelah a dak'ile ta amsa, baidamuba dayake dama ta Saba, hamma yayi yace Ina abincina, fadeelah tace banyi ba, yace saboda mi tace haka kawai, girgiza kai yayi, yacev Allah ya kyauta, yatashi yanufa d'akinshi.
Kwance yake yayi rigingine, k'ofan ta banko, bai d'aga ido ba dan yasan wacece, fadeelah tace muhammafld inada magana dakai, tashi yayi ya zauna, yace ina jinki, fadeelah amma kisan maganar dazaki gayaman Dan nafara gajia da shirmenki, fadeelah tace kwana biyu ina kake zuwa? Muhammad yace wajen budurwata wadda Zan aura, a firgice fadeelah ta tashi tace what? Aure, wlhi baka isa ba, kace zaka k'ara aure, yo Akanmi, nizaka cima mutunci, saikuma tafashe da kuka, Muhammad yace look fadeelah nagaji da abinda kikeman giddanan, kiduba kiga banda k'ima wajenki, bakisan ki gyaraman d'aki ba, abinci kuwa bandashi, nine yawon restaurant Neman abinci kamar banda Mata, toh gaskia am tired Ina buk'atar k'ara aure nasamu mai kula Dani, ayfa fadeelah kamar jira take yagama tafara zaginshi, tsawa yamata yace get out of my room, fita tayi tana kuka, tana zage zage, tsaki yayi ya kwanta
Claire na kwance bacci yafara d'aukanta saukar bugu taji firgigit ta tashi, tana mitssike mitssiken ido, babanta tagani yana huci, da mamanta, baban yace claire naji sakonki, toh abinda nakeso kisani wlhi saidai ki zab'a komu koshi, muddin kika auri wani ba jinsinki ba, toh wlhi bani babuke zan yafeki, haka kuma mamarki itama zata yafeki, ke yanzu ki rasa wanda zaki aura sai bahaushe, kinkuwa san suwaye hausawa? Kai claire kincucemu kuma kin cuci addinmu, toh muddin kika ce musulmi bahaushe zaki aura, saidai kinemi wasu iyayen badai muba, kuma nacireki daga cikin JINSINAH, itadai claire kanta k'asa yake, batace komai ba, mummy tace ay dear nagaya mata muddin ta auri bahaushe toh bamu ba ita, amma dayake ya hure mata kunne ko ajinkinta, baban yace nidai nabata zab'i, komu ko shi, ya juya yabar d'akin, maman ta dungure ta itama tafita, girgiza kai claire tayi takoma ta kwanta.....
Koda fadeelah tatashi idonta yayi kumburi alamun tasha kuka, shikanshi muhammad tabashi tausayi saidai dole ya nuna mata shike aurenta, harkokinshi yacigaba dayi, dan yasan ba maganan break fast dama lapia batayi ba bare yanzu, yagama, yashirya zai fita, ya ajemata kud'in cefane, yakai bakin k'ofa zaifita tace yasunan wadda zaka aura, Muhammad yace Claire fadeelah tace claire, musulmace komi, muhammad ya girgiza kai yace ah ah she's not a Muslim, a zabure tatashi tace kana nufin Christian ce muhammad yace haka nake, nufi fadeelah tace gaskia kaji kunya kakuma fad'o karasa wacce zaka aura sai arniya, duk matan dake dunia wanda kuke jinsi guda amma wai christian zaka aura, muhammad yace ita nake ra'ayi fadeelah tace toh wlhi baka isa ba kaji nagayama, Muhammad yace mungani yasakai yafita, yabar fadeelah tana bala'i tana kuka,
Yana fita yakirawo claire a waya tana d'agawa yace kina Ina? D'ayan b'angaren naji tace gida, yace yazanyi naganki, shiru tayi, tace katsaya k'arshen layinmu dakazo saika kirani, muhammad yace toh, "yana isa layin yakirata, ahankali claire tafita daga gida, tana fita ta dinga sauri, hartana tuntub'e tana isa wajen muhammad ta bud'e motar tashiga, d'agowa yayi yana murmushi, saikuma yaga idonta yayi kumburi, muhammad yace Clair lapia, kuka tafashe dashi nanfa hankalinshi yatashi, yadinga lallashi, dakyar yasamu tayi shiru, muhammad yace Claire lapia, claire takwashe komai tagaya mashi, bata b'oye mashi komaiba, shiru yayi yace kiyi hak'uri claire nina jamaki kominene, murmushi tayi tace Muhammad is,not ur fault, laifinane, kuma wlhi Zan iya rabuwa da iyayena da JINSINAH saboda kai, kaidai rik'on amana nakeso, muhammad yace karki damu in shaa Allah zan rik'eki da amana, Claire tace tnx dear, murmushi yayi yace ur welcum, claire tace muhammad Bari na koma mummy batasan nafito ba, yace hakane bankwana sukayi tafita shima yatada motarshi yatafi....
Shin wacece Claire waye kuma muhammad taya akayi suka had'u claire da Muhammad shin claire zata auri muhammad tabar iyayenta, koko jinsinta zata aura, kudai biyo Yar ficika danjin amsoshin Ku........
Dedicated to biebeeisa❤
IG: yar_ficika
Written by
Feedoh Deedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment