DIJAH 11~15
🏵🏵DIJAH🏵🏵
Na
Feedoh✍🏻✍🏻
1⃣1⃣~1⃣5⃣
Sumi sumi dijah tayi ta ja k'afa taje ta aje ruwan, tadawo ta duk'a tace goggo nagama saura mi, hararanta tayi tace saura uwarki shegia kawai, tashi ki dauko wanki na kiman gayacan daki, saura kuma aman dan halin da aka saba, dijah ta shiga dakin tana share kwallan dasuka makale Mata, tana adu'ar Allah yakawo mata sassauci, haka ta fito tafara wanki, tana wanki Inna larai na zazzaga mata masifa, ahaka hartagama wanki tas, tazo ta duka tace Inna nagama saura mi? Saura uwarki ni tashi saga gabana mayya, kurwata tafi karfinki, duk malam ne da jaye yajenshi yakawoman mugun iri gashi duk kin addabeni kinatashi kosaina karyaki, dijah taja jikinta ba kwari tashige daki..
Tana daki taji kiran sallar magrib haka tafito jiki ba kwari, saboda tanajin yunwa danma Allah yataimaketa taci abinci gidansu hanne, buta ta dauka tashiga kewaye tafito ta daura alwalla, sallah ta kabbara ta idar da sallah tazauna tana lazimi har aka kira isha tagama sallah, taji Inna na kwalamata Kira, tafito jiki sanyaye ta duka tace Inna gani, hararta tayi yace shegia munahika kina Abu kamar tagari sai iskanci cike da rayuwarki, itadai dijah kanta kasa batace komai, tashi kije kichn kingin dumame na nan ki dauko kici, dan banda abinda zanbaki, tunda kinman bakin ciki, kema saidai kici dumame, dijah ta tashi tadauka kingin tuwon jiya, haka ta dinga cin tuwon nan badan tanaso ba ga sanyi da yayi..
Saukar ruwa taji jikinta wani irin tsalle tayi ta koma gefe guda tana karkarwa, damkota Inna tayi tace dan uwarki da kika gama sallar asuban komawa kikai bacci shegia wani mari takaimata saida dijah ta kifa, tace dan Allah Inna kiyi hkri wlhi bansan sanda bacci ya kwasheniba, dama ina zaki sani gantalalla, ubanwa zai maki gyaran gidan, kuma ya dama maki kwakkwon? Ko yauma so kike inyi asara, wlhi matsawar baki saida ba yau saina hallakaki gidannan inma juye zakije kwartayen naki zasu maki kije su maki dama aykin Saba bin maza gara kiyi mai dalili dan wlhi yau ban daukar asara incidaki Kuma kisani asara baiyuwa, yarinya tunda aka kakabaman ke iftila'i ke hawana, uwarki tayi abin kunya ankawoman ke an jajibaman, nidai Allah yakawo randa zan yada kwallan mangaro in huta da kuda, wuce dan uwarki ki daura ruwa kuma ki gyaraman gidana tas....
Written by
Feedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment