DIJAH 1~5
🏵🏵🏵DIJAH🏵🏵🏵
Na
Feedoh✍🏻✍🏻
0⃣1⃣~0⃣5⃣
Note: wannan labarin kageme ba dagaske ba, banyi dan cin fuskar wani ko wata ba....
Bismillahi rahmanir rahim
Tafiya take tana sauri hartana harde k'afafuwa, gabanta sai faduwa yakeyi, gashi bata saida goro ba, kuma gashi tayi marece, yau tasan mai rabata da Inna larai sai Allah, daga baya taji ana kwala mata Kira, juyawa tayi taga mai kiranta, hanne ce qawarta, hanne ta k'araso tace haba dijah wanan sauri haka kamar zaki tashi sama.
Dijah tace hanne walhi ina tsoron Allah ina tsoron had'uwana da Inna larai, gashi bansaida goron ba ga aikin da zan tarda, bansan yazanyi ba yau hanne,
Hanne ta dafa dijah tace kiyi hakuri qawata in shaa Allah ba abinda zata maki, dijah ta girgiza kai kawai dan tasan mai rabata da Inna larai yau sai Allah.
Ahaka so suna fira harsuka karaso gida, sukayi bankwana hanne ta wuce gida, dijah ta shiga gida, tana sallama, wata uwar Harara da Inna larai ta mata saida yan cikinta suka juya, Inna larai tace shegia gantalalla sai yanzu kika gadamar dawowa, kina can yawon iskancinki, yanda uwarki tayi, yawo harta sameki, kema haka kike, shegia idan kika d'auko abin kunya saidai ya kare kanki, zonan dan ubanki matsiyaciya....
Written by
Feedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment