DIJAH 16~20

🏵🏵DIJAH🏵🏵

Na
   Feedoh✍🏻✍🏻

1⃣6⃣~2⃣0⃣

Haka dijah tafito jikinta duk a jik'e taje ta hura wutar icce da kyar tasamu takama ta daura ruwan kwakko, tadawo tahada kayan wanke wanke ta wankesu tas, tana cikin shara ne taji wani wawan kulli a baya saidatakai kasa, nikaina feedoh bansan sanda nakai kasaba, cikin raina nace dama akwai irinsu Inna larai adunia?

Tsawar da Inna tamatane yamaidoni cikin hayyacina daga tunanin danake, tace yau ga tabbatatta haka ake shara a kauyenku? Kodayake ina shegia ma yasan kauyensu, dawo baya  kiman sharan kirki tabbatta kina kallona ido cikin Ido, dijah dai batace komaiba saboda inda sabo ta riga da tasaba, abinda kawai takasa sabawa dashi, gorin da Inna ke mata, da kuma kiranta shegia kullum aduan ta Allah ya bayyana mata gaskiar ita wacece, dawowa tayi tafara sharan daga farko tanayi Inna na mitar data saba yanda kukasan sadiya marafa😜

Tanagama shara taje ta sheka kokko tagama aikinta tsaf tazo ta tsugunnna tace Inna nagama tsaki Inna taja tace naji, jeki kitchen kosai na nan guda biyu kizo ga kwakko nan kidauka kisha salan kuma ki tsaya shegiyar nawa nikuma inkaryaki, haka dijah ta tashi jiki ba kwari ta wuce ta dauko kosai tazo tadauki kokko baikai rabin kofi ba, wanda ko yaro akaba bazai isheshiba, amma shi goggo tabata, Allah shi kyauta haka dijah tagama tazo ta duka gaban Inna tace nagama zantafi, tace naji dijah tamike Inna tace ke zonan dan uwarki, dukawa tayi, Inna takama mata kunne tace wlhi kika shaman kayan sana'a kokuma kikaba kwartayenki saina ci uwarki kinajina, daga Kai dijah tayi alamar eh" kana Inna ta hankadata, mikewa tayi ta kakkabe kayan jikinta taje ta daura kokko bisa kai tafita

Isar ta kenan inda suke saidai saidai, saiga hanne tazo wajenta, dijah na ganinta ta washe baki saboda hanne kadai ke debemata kewa, hanne batabar wajenba saida dijah tagama saidawa kana suka taho tare, dijah ta kalli hanne, tace hanne nafara zargin ni shegiace, hanne tace miyasa kikace haka? Tace toh inbadan ina shegia ba tun ina jaririya aka yardani haryau gashi shekarana 13 amma mahaifiyata bata nemeni ba, kingako ay yakamata na yarda da Kalmar lnna ni shegiace hawayen dake makale da ita suka gangaro, hanne tashare mata hawaye tace dijah jikina nabani keba shegia baceba kinada uba kamar kowa saida aka daura aure aka sameki kidaina daga hankalinki kinjiko... Nikaina feedoh jikina yafara mutuwa dijah kodai shegia ce, shin wacece dijah? Wacece Inna larai ya'akai dijah tazo wajen Inna larai, kuma dijah shegia ce kotanada uba, kudai kubiyo FeedohDeedoh domin jin amsoshin nan.....

Written by
                Feedoh✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180