DIJAH 21~25
🏵🏵DIJAH🏵🏵
Na
Feedoh✍🏻✍🏻
2⃣1⃣~2⃣5⃣
Asalin labarin
Malam amadu mutumin kauyen katsina ne, bakiyawa, sana'rsa malunta ne domin almajirai gareshi kuma daidai gwargwado yana da abin hannunshi, kuma Allah yabashi wadatar zuci, domin duk wanda Allah yaba wadatar zuci ya haye, Allah kabamu wadatar zuci, malam amadu yana da mata guda daya, lubabatu kuma itama lubabatu akwai hakuri da kawaici shiyasa malam yake santa.
Shekaransu takwas da aure amma lubabatu ko batan wata bata tabayiba,abin duk ya isheta ya dameta, malam shine kullum aikin lallashi, abinda yafi dagama lubabatu hankali shine yadda dangin malam sukayo kanta da surutu ta mallake masu dan uwa gashi ita bata haihuwa gata juya na (feenat ja'afar) amma duk wannan gorin da suke mata bata taba gayama malam ba, saidai taci kukanta, tayi addua idan tanada rabon haihuwa Allah yabata, malam da lubabatu sun tasanma kusan shekara goma da aure amma haryanzu shiru kakeji ba labari.
Watarana lubabatu na zaune tsakar gida tana gyaran wake, saiga yayar malam ta shigo bako sallama, saida gaban lubabatu saboda tasan ganinta ba alkairi baneba, taduka harkasa tagaidata, amma ko kallo bata ishetaba, tace "ke" ina malam? Lubabatu tace yana daki, tace yiman magana dashi.
Lubabatu ta mike taje tayi sallama malam yace shigo, ta duka tace dama yaya lantana ce takesan magana dakai, yayi shiru yaace cemata gani nan zuwa, lubabatu ta fita, tasami lantana inda take kamar andasa icce, tadan duka tace yaya yace yana zuwa, bata kalleta ba bare tasa ran amsawa.
Malam yafito yace ah yaya sannu da zuwa shine baki zauna ba, lubabatu ya baki bata wurin zama ba, maza dauko mata abin zama, tace bazama ne yakawoni ba, susutacce wanda mace tagama dashi, toh idan tagama dakai ni bata gama daniba, shekara goma da aure mata ko batan wata bata tabayiba, kana zaune da juya, sai anyi magana kafara yima mutane wa'azi kamar kafimu sanin Allah, toh duk ba wannan yakawoni ba, abinda yakawoni shine, namaka mata kuma wlhi kaji na rantse banga mai hana auren nan ba, kuma sati nasama za'a daura auren, idan ita yar son taka bata zama toh takama gabanta, tana kaiwa nan tajuya tafita.
Malam yabita yana kira amma kobi takanshi batayiba, haka yadawo yasamu lubabatu nashare hawaye, ya duka yace kiyi hkri in shaa Allah zansan yanda zanyi afasa aure nan, lubabatu ta dago tace malam idan kanasan nacigaba da zama gidanka ka amince da wanan aure, amma muddin kaki amincewa nikuma zanbarma gidanka, nima inasan naga yayanka dunia ko ban haihuba idan ka haihu kamar na haihu ne, dan haka ka amince kawai, tana kaiwa nan tatashi domin kuka yaci karfinta,batasan tayi gaban malam....
Written by
Feedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment