DIJAH 26~30
🏵🏵DIJAH🏵🏵
Na
Feedoh✍🏻✍🏻
2⃣6⃣~3⃣0⃣
Binta malam yayi da idanuwa yana girgiza kanshi dan gaskia tana bashi tausai shidai inbanda dole ba abinda zaisa yak'ara aure saboda baisan wadda za'a aura mai ba, tashi yayi yafita waje, itako lubabatu inbanda kuka ba abinda takeyi, tunanin datakeyi idan an auro mata wata ta haihu tasan k'ara tsanarta dangin malam zasuyi, tashi tayi ta dauro alwalla tazo ta kabbara nafila, tagama ta d'aga hannu sama tana adu'ar Allah yabata ikon dangana da hakuri yakuma hada kansu da wadda za'a kawo mata...
Bayan fitar malam bai zame ko inaba sai gidan yaya lantana, sallama yayi ta amsa ba yabo ba fallasa, yashiga yasami gefe yazauna, gaisheta yayi nan ma a dak'ile ta amsa, malam ya gyara murya yace dama ba wani abu baneba yaya lantana na amince da maganarki ta inkara aure nan yaya lantana ta washe baki tace kokaifa amadu yanzu nasan ba'a gama dakaiba, da kana zaune da mata shekara da shekaru ko batan wata, kuma baka damuba, ay inaso naga yayanka kaga mu biyu Allah yaba iyayenmu nikuma yayana duk sunkoma ga Allah gara inga naka yaran..
Shidai malam baice mata komai ba, tashi tayi tace banga tazama ba bari mashiga namaka sallama da matar saiku daidaita kanku, tunda makwabta nane, kuma mahaifinta yabani, gyale tadauka tashiga makwabta da sallama, matar ta amsa tace lantana kece yanxu, tace wlhi kuwa larai nazo inma magana taje tasami malam yana gidana, innar larai tace toh ayhaka yayi bari namata magana, dakin da larai take ciki ta tashiga tace tashi kije ga lantana nan tazo malam nasan ganinki saura idan kinje kimashi bakin halinki, tashi tayi tana gunguni tafita tsakar gida tasami ya lantana bako gaisuwa tace gani, lantana na washe baki tace dama malam ne kesan magana dake yana gida, tabe baki tayi tace naji, kana tajuya tayi gidan yaya lantana..
Shiga tayi gidan da sallama,malam ya amsa yace shigo tashiga tasamu wuri ta zauna suka gaisa, malam yace baisa nayi maki dogon bayani ba, SBD nasan yaya duk tamaki komai, kuma ni kingama ba yaro baneba, inkinga banmakiba kigayaman, larai tace badamuwa malam nikam kaman malam yace to Alhamdulillah yasunan malamar? Tace larai, yace larai inada sharadi, tace nami? Yace inada mata guda kuma bata taba haihuwa ba, kuma inasan matata dan haka ban lamunci adinga cimata mutunciba barema har idan Allah yabaki haihuwa, bazan dauka amata wulakanciba inko akamata sai inda karfina yakare, tabe baki tayi tace, idan tashiga gonata bafa zan kyaletaba malam yace bama zata shigaba saboda nasan wacece lubabatu....
www.phirdauceejeebo.mywapblog.com
Written by
Feedoh✍🏻✍🏻
Comments
Post a Comment