DIJAH 31~35

🏵🏵DIJAH🏵🏵

Na
   Feedoh✍🏻✍🏻

3⃣1⃣~3⃣5⃣

Larai tabe baki tayi, suna zaune har yaya lantana tadawo, da fara'arta tace malam Ana nan kenan, kaga zabin danamaka ko? kuma nasan zaka yaba shidai malam inbanda daga Kai ba abinda yayi dan gaskia bawani kwanta mai tayiba, yana cikin tunani yaji murya yaya lantana, tace kuma inada tabbacin wanann diyar ba juya baceba dan duk zura'ar gidansu ba juya, nidai deedoh girgiza kai nayi saboda mamaki, koya akai tasan ba juya baceba, Allah yasa mudace, malam yace yaya ay haihuwa da rashinta na Allah ne, tabe baki tayi tace tunda antabo ranka ba, nidai wanann shegiyar lubabatun bantunanin haka ta barka, shidai malam mikewa yayi yace yaya ni zan wuce saina dawo, ko kallonshi batayiba ya girgiza kai yafita.

Yana fita yaya ta yuyo kan larai, tace larai abinda nakeso dake idan kinshiga gidan malam bansan ki sararama lubabatu, domin kuwa munafukar matace ta mallake malam yazama salamamme, saikinyi da gaske, dakinma haihu komai zai zama naki, saiyanda kikayi da malam, dan inada tabbacin ke kina haihuwa dan ba juya baceba girgiza kai larai keyi da alama hudubar yaya lantana ta shigeta..

Yau juma'a yau za'a daura auren malam amadu da larai bayan sallan juma'a, ya shirya tsaf yafito ya tarda lubabatu tsakar gida tayi tagumi, yace lubabatu lapia? Tadago tana yake tace malam lapia lau girgiza kai yayi yace Allah yasa dagaske, nizan wuce tace toh malam Allah yabada sa'a yakumasa abokiyar arzikice shidai malam kasa amsawa yayi, haryakai soro yadawo yace af lubabatu idan sunzo kawo amarya kibasu makkulin dan gaskia bazan shigo gida ba masallaci zan tsaya gyada mashi Kai tayi.

Habaice habaice nafaraji daga kofar gida ana buda, yaya lantana na gaba  bismillah kishigo da kafar dama domin ke ba juya baceba nan gidanki ne gidan mijinki kuma uban yayanki idan kikafara haihuwa saikinyi dozin duk wanan abun yaya lantana da makarrabanta keyi, bako sallama haka suka shigo itadai lubabatu na daga bakin dakinta da abokan arziki zaune basu tankaba,yaya lantana tace ke" lubabatu ina makkulin dakin amarya, tashi tayi ta taje ta dan rusuna taba yaya lantana, tana juyowa suka bushe da dariya, suna cewa su juya kenan...

www.phirdauceejeebo.mywapblog.com

Written by
                Feedoh✍🏻✍🏻

Comments

Popular posts from this blog

HUDAH 01~25

RASHIN GATA 1-5

RASHIN GATA 176-180